← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 84

Sashe 41

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumana tace, "lafiya lau. Ya Babyna Ayan?."
"Yana Lafiya lau."
"Nace ka turo min pictures ɗin sa bqkq turo min ba. yace, "bani dasu, amma zan tura miki." Tayi murmushi tace, "zan faɗawa Mummy ka shigo in ta tashi." Ya amsa ya fita ta bishi da kallo tana dafe zuciyar ta saboda bugawar da take yi.

Asibiti ya wuce ya shiga office ya fara abinda yake gaban sa. Suna da treater ta dashen zuciya ƙarfe sha ɗaya na rana hakan ya saka shi gama yin komai da wuri, wayar sa ma a office ya barta suka shirya dashi da team ɗin ranar aka shiga don aiwatarwa. Suna fitowa lokacin sallar azahar yayi ya hau sama zai shiga office kenan ya haɗa da Huzaifa, Adnan yace, "Ashe ka zo?."

Huzaifa yace, "na zo kun shiga treather." Bebi yace, "yanzu muka fito sallah nayi na dawo nan, yunwa nake ji sosai." Huzaifa ya kalle shi yace, "Muje office to akwai abinci da nazo dashi sai kaci, dan ni na kasa ma ci wallahi." Tare suka shiga office ɗin nasa Huzaifa ya ajjiye masa abincin doya ce da kwai  da plantain sai sauce a gefe.

Huzaifa ya kalle shi yace, "yanzu Bebi da gaske abinda yake faruwa gaskiya ne? Daddy shine mahaifin su Manal?." Bebi da yake ƙoƙarin fara cin abincin ya kalle shi ya ce, "gaskiya ne mana Huzaifa, wannan ai ba ɓoyayyen abu bane ba ne, abu ne a bayyane."

Sallama Hamza yayi ya shigo ganin su su biyu sai ya tsaya daga bakin ƙofa yace, "okay na dawo." Huzaifa yace, "ka shigo mana." Ya shigo yana cewa, "ai naga kamar kuna tattaunawar sirri ne." Ya zauna Huzaifa ya kalli Hamza yace, "wani abu ne yake damuna ko nace yake damun mu Hamza."

Hamza yace, "to ina jin ka."
"Manal ɗin Bebi Daddy mu shine mahaifin ta, shine jinin ta wanda yayi silar ta zuwa duniya." Hamza da mamaki yace, "ban gane abinda ka ke faɗa ba."

Huzaifa yace, "ya kamata ka gane, abinda nake nufi kenan, jiya an tabbatar da mahaifina shine mahaifin ta." Bebi ya kalli Huzaifa dan Hamza ya kasa magana yace, "ya ka baro Daddy? Ko Baka je ba?."
"Naje, yana nan kwance ina jin ma bashi da lafiya. Gabaɗaya  yanayin sa ya canja ba shi kaɗai ba kowa na gidan."

Hamza yace, "Nifa kun barni a duhu." Bebi ya kalle shi yace, "zaka fito haske in an baka labari, amma yanzu ka cigaba da zama a duhun ka, abinda Huzaifa ya faɗa maka kuma gaskiya ne."

Huzaifa ya kalle shi ya fara bashi labarin duk abinda ya faru kamar yadda aka faɗa masa, duk da a taƙaice ya bashi labari bai kuma faɗa masa zancen dukiyar Mama ba. yana gama faɗa yace, "wannan shine abinda ya hana mu zuwa jiya, ta yadda ma za'a fahimtar da Maman su Manal ɗin shine aiki."

Hamza ya girgiza kai cikin wani irin yanayi yace, "Allah gwanin hikima. Wato shiyasa Allah bai saka maka son Manal a zuciyar ka ba tun farko, Sai ya saka maka tausayin ta kamar ƴar uwar ka ashe ƙanwar kace ta jini. Da ace yanzu kaine ka ke auren ta har da yaro da labarin ya sake canja salo."

Huzaifa yace, "har ka saka gaba ya faɗi, bari kawai." Bebi baice komai ba yana goge hanun sa da tissue tare da shan ruwa, Huzaifa ya kalle sjk yace, "Ka sanar da Manal ɗin ne?." Ya girgiza kai alamun a'a yace, "ɓata baki ne in na faɗa mata, Manal duk abinda Maman ta take so shi take so, in Mama ta karɓi Daddy ta kuma ce komai ya wuce Manal zata kalle shi matsayin mahaifi. In kuma akasin haka ya faru Manal baza ta tanƙwaru ba a yanzu."

Wayar Huzaifa ce take ƙara ya kalla sai yace, "kaga Manal ɗin ce take min waya." Bebi yana kallon sa ya ɗauka ya saka a speaker Manal tace, "Yaya Huzaifa ina wuni? Don Allah in kuna tare da Partner ka faɗa masa Mama babu lafiya na fita na tafi asibitin, ina ta kiran wayar shi bai yi picking ba" ta faɗa a haɗe ba tare da ta bari ya amsa gaisuwar ba.

Huzaifa ya kalli Bebi da yake kallon sa sai yace, "Shikenan zan faɗa masa in sha Allah, a wanne.....!" Kafin ya ƙarasa tambayar ta sunan asibitin ta yanke wayar.  Huzaifa yace, "Allah yasa ba maganar jiya bace zata tayar mata da ciwon ta."

Bebi ya miƙe yace, "Allah dai ya kiyaye kawai, bara na kira ta naje asibitin tunda an faɗa min." Huzaifa yace, "nima zani bara na sakko." Tare suka fita su ukun dan shi Hamza yana da marasa lafiyar da zai gani da shima zai je.

BDƘB3P23

Manal lokacin da suka shiga asibitin Mubeena ce ta faɗa mata inda suke ta shiga ɗakin da Maman take, ɗakin mai mutane biyu ne a ciki, wata mata tana kan gadon ta kwance sai kuma gadon Mama. Ganin Maman tayi a zaune tana cin salad tayi turus Maman su Surayya da take bayan Manal tace, “ashe jikin da sauƙi.”

Mama ta kalle su tace, “Balaraba daman ba wani ciwo bane ba, Mubeena ce ta nace sai mun zo asibitin dan a nan muka kwana.” Mubeena tace, “Wallahi Mama da daddare jikin ta zafi yayi, har rawa jikin ta ya dinga yi shine kuwa na kira Baba muka zo nan.” Manal da take jin su tace, “daman wai tun dare bata da lafiya ban sani ba?.” Mama ta kalle ta tana hararar ta tace, “ke tafi can, banda ma zamani ina ke Ina fitowa Manal? Haihuwar da ko wata ɗaya ba’ayi ba har yanzu amma yawon ki kike daga nan sai nan.”

Manal ta turo baki gaba tace, “To Mama ai wajan ki nazo.” Ta ƙaraso kusa da Maman ta riƙe hannun ta tana kallon ta tace, “in akace min baki da Lafiya Mama hankalina tashi yake sosai, wallahi kawai ganina nayi nazo ban san ta ya akayi ba.” Mama tayi murmushi bata kula ta ba tace, “Mubeena bani Ayan ɗin na gan shi, yaro mai sunan ƴan gayu, ko nace Khalil dan ni bazan ce wani Ayam ba.” Mubeena ta bata shi tana kallon sa tace, “tabarakallah, yaron yayi nauyi sosai yayi kiɓa kamar yayi wata biyu, kema gaki nan sharr dake lalɗai Mama tana baki kulawa.”

Manal tayi dariya tace, “ai duk lokacin Mama ta dawo gida ban san ya zanyi ba, Mama ko pampers fa ban iya saka masa ba.” Mama tayi dariya tace, “zaki koya ai.” Da sallama Bebi da Huzaifa suka shigo ɗakin Mama ta kalli ƙofar ɗakin da suke tsaye tace, “Adnan ku ne tafe?.”

Sai Bebi yaji daɗi ganin Mama bata canja masa ba duk da bata san waye Huzaifa a wajan ta ba, ya ƙaraso suka gaisa da Maman suka sake gaisawa da Maman Surayya kafin yace, “Mama ya ƙarfin jikin?.”
“Da sauƙi.” Huzaifa yace, “Amma Mama da babban asibiti aka je ba’a zauna a nan ba. Ni ban ma san asibitin nan ba sai yau.”

Mama tace, “Mubeena ce ta takura ni da bazan zo asibiti bama, sun ce yanzu ma zamu wuce gida babu wata matsala daman zazzaɓi ne kawai.” Bebi ya ce, “Amma duk da haka Mama ba nan ya kamata azo ba, kuma da gaskiyar ta ai ko ya ciwo yake ba a wasa dashi, musamman irin ciwon da kike dashi mai hatsari.”

Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Basu jima sosai ba suka yi sallama suka fita. Manal ta biyo bayan sa ta samu zai shiga mota tace, “Partner.” Jin muryar ta sai ya dakata da shiga motar ta ƙaraso gaban motar tace, “zan bi su Mama gida in an sallame su.”
“To” ya furta a taƙaice. Kallon Huzaifa tayi taga yana kallon ta sai tayi murmushi tace, “Yaya Huzaifa ina Ayra?.”

“Ayra tana nan Manal, Sai maganar ki take yi.” Ta sake yin murmushi tace, “Ai ƙawata ce, a gaishe su har su Aisha da Mama har Daddy ɗin ma. Na kira Aysha na yi musu bangajiya ban same su ba, amma don Allah kace ina yi musu bangajiya” ta faɗa tana komawa ciki da sauri. Huzaifa ya shiga motar yana sauke ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi. Bebi ya ce, “ka kula da fuskar Mubeena kuwa? Suna kama da Aisha.”

Huzaifa yace, “na gani wallahi, abinda zan ce maka kenan maganar Manal ta ɗauke min hankali, kuma kaga a baya ban gani ba amma yanzu yanayin su gabaɗaya iri ɗaya ne.” Bebi yace, “shiyasa nake tunanin a inda na san mai irin fuskar Mubeena, Ashe Aisha ce. jini ba wasa bane” ya faɗa yana jan motar suka fita.

Basu jima a asibitin ba suka koma gida gabaɗayan su har Maman su Surayya, sai bayan ta raka Mama gida ne sannan ta shiga nata gidan.

Suna zaune tare da Mama Ayan yana hannun Mama tana ta yi masa wasa kafin ta kalli Manal tace, “Manal.” Manal ta kalli Maman kafin Maman ta kalli Mubeena tace, “abubuwa suna ta faruwa a cikin rayuwar ku wanda baku yi zaton su ba ko?.” Suka yi shiru babu wacce ya amsa Mama ta sake cewa,

“Ko bayan raina kar ku karɓi wanda yazo yace muku shine mahaifin ku, ku cigaba da rayuwa kuna ɗaukar Baba matsayin mahaifin ku ba wani daban ba. Kar wani yazo yace shine ya haife ku ku amince dashi, kar wani yazo yace shi dangina ne shima ku amince dashi. Yadda aka nuna ba’a sona kuma ba’a son ku a ƙyale ku ku cigaba da rayuwar ku Allah yana son ku.”

Mubeena tace, “Daman Mama ni babu wanda zan iya kallo matsayin mahaifina bayan abubuwa da aka yi miki, zuciyata baza ta iya yafe musu ba wallahi.” Mama tace, “Ku cigaba da riƙe kan ku kuna zumunci da juna, ga uwa nan kuna da ita a kusa Balaraba, duk abinda zan muku wallahi zata kwatanta saboda tana son ku gabaɗaya ku.”

Manal tace, “me ya faru ne?.” Mubeena tace, “au baki sani ba? Mijin ki bai faɗa miki da wanda suka zo gidan nan jiya ba?.” Manal ta girgiza kai alamun a’a tace, “bai faɗa min komai ba.”
Chapter 41 · 0% Book details