← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 84

Sashe 25

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gani tayi kamar baya cikin hankalin sa ta ƙarasa inda yake tana kiran sunan sa amma idon a kulle da sauri ta fita taci karo da Bebi a harabar gidan yana shirin shiga mota ta kira shi, ganin ta hankali tashe shima hankalin sa ya tashi ya bita. Yanayin da yaga Abban ya saka shi hankalin sa ya tashi, gashi shi kaɗai ne babu sauran mazan dole sai driver ya kira suka riƙe Abban suka fita zuwa asibiti.

Cikin ƙaramin lokaci aka isa asibitin da gaggawa aka fara taimakon Abba aka masa allurar bacci bayan an masa allurai an saka masa ruwa. Duk Bebi ne yake yi da kansa sai taimakon wani likita da suke a team work ɗim ranar, basu jima a ciki ba suka fito daga ɗakin ya kalli inda aka tanada dan zama yaga Mama  da Mamy sai Maryam a kusa da ita, sai gefe kuma Lubna da Kausar ne da yayyen sa maza duka a zaune.

Ƙarasawa wajan su yayi kowa jira yake yaji abinda zai ce ya kalle su ya ce, "ku kwantar da hankalin ku ba wani abun damuwa bane, jinin sane ya hau soaai shiyasa hakan ta faru, amma mun yi solving problem ɗin yanzu da ya farka in sha Allah zafi warware."

Yaya isma'il yace, "ka tabbatar da abinda ka ke faɗa Bebi?."
"In sha Allah." Mama dai kuka take yi hakan ya saka Bebi ya ce, "Mummy me ya firgita Abba lokacin ɗaya haka?."
"Waya aka yi masa akace company na lagos yana ci da wuta, tunda yayi salati ya ajjiye wayar shikenan."

Yaya Bilal yace, "an kira ni an sanar dani, amma wutar ta tsaya a yanzu kuma ba'a yi asarar rai ba. Dukiya ce dai an yi asara amma sai naje gobe da safe na gani da idona." Bebi ya sauke numfashi yace, "ku kwantar da hankalin ku in sha Allah zai samu lafiya" yana faɗar hakan ya juya ya bar wajan ya sake komawa inda Abba yake.

Suna zaune a wajan har tara na dare ta wuce duk sun shiga sun ga Abba sun fito dan hankalin su yaƙi kwanciya gani suke kamar an ɓoye musu wani abun akan Abban. Farida ma sai da tazo da mijin ta saboda hankalin ta bazai kwanta ba in bata zo ta ganshi ba. Bebi ne ya dawo wajan da suke ya ce, "Mamy ya kamata ku tafi gida dare yayi, ni zan zauna dashi a nan duk abinda yake faruwa zan sanar da ku."

Mamy tace, "A'a ai babu wanda zai iya tafiya yanzu, dan in mun tafi hankalin mu bazai kwanta ba." Yaya Bilal yace, "haka zamu tafi Mamy, haƙuri za'a yi tunda gamu a nan ai babu wata damuwa." Maryam tace, "Nima dai zan zauna bazan iya tafiya na bar Abba a nan ba."

Bebi yace, "ku yi haƙuri duka amma babu wanda zai zauna a cikin ku, Allah ya nuna mana gobe da safe sai ku dawo."

Shiru sukayi duka kafin Mummy tace, "ko kuma Mamy ta zauna mu sai mu tafi." Bebi ya sauke numfashi kawai ya juya ya shiga office ɗin sa. A nan yaga wayar sa na haske dan ya kashe ƙarar ta, ya ƙarasa ya duba yaga kiran Manal babu adadi hankalin sa ya tashi da tunanin wani abu ya same ta ya kira ta da sauri amma bata ɗauka ba, ya sake mira bata ɗauma ba har sau uku. "Ya Rabbi! Me ya same ta?" Ya faɗa yana fitowa wajan yana kuma kira amma bata ɗauka ba dai.

A kira na biyar ta ɗauka ya ce, "ina kika shiga? Lafiya kike dai ko?."
"Lafiya lau, na shiga banɗaki ne. Kana ina har goma na dare ta wuce baka dawo ba? Cewa kayi fa ƙarfe bakwai zaka dawo." Bebi ya ce, "ki yi haƙuri ina asibitin har yanzu, amma yanzu zan turo miki Kausar ko Lubna ku zauna tare ko nace ku kwana ma....." katse kiran yayi saboda kiran sa da yaji ana yi masa sai ya fito.

Bai jima a can ba ya dawo ya samu suna nan inda ya bar su ya kalli Kausar ya ce, "Kausar ko ke ko Lubna wata tabi Yaya taje su kwana da Manal, bazan koma ba yau gaskiya, in ma zan koma sai dare sosai." Mamy ta kalle shi tace, "A'a Bebi, ba a barin mai tsohon ciki ita kaɗai a gida ba daidai bane, cikin ya shiga watan haihuwa fa, bai kamata kana yin nisa da ita ba."
"Mamy shiyasa nace Lubna ko Kausar wata taje, duk abinda yake faruwa sai su sanar dani."

Mummy tace, "tunda kace komai lafiya kaje gida in yaso sai ka dawo kaima da asuba." Huzaifa ne yazo wajan suka gaisa da su Mama yake cewa kwana zai yi   A asibitin Mamy tace, "Shikenan ma, Kaga ga Huzaifa ma abinda yake faruwa ya faɗa maka. Amma me Kausar ko Lubna zasu iya yiwa Manal in haihuwar ta samu?, in suka yi maka wayar ma kafin kaje daga nan ta galabaita."

Ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Mamy" ya faɗa yana barim wajan. Sun riga shi tafiya sai da ya gama duba wani file sannan ya hau mota shima ya wuce gida lokacin sha ɗaya na dare tayi.

A zaune ya samu Manal fuskar nan tayi ja da alama yaci kuka dan ya san daman za'a yi haka, ita daman baka mata laifi bama tana kuka balle an yi mata, balle kuma bai faɗa mata dalilin zaman sa ba. Ɗarasowa yayi ya zauna ya kalle ta kafin tace komai  ya ce, "Abba ne babu lafiya yana asibiti a kwance shiyasa na jima.." Jin abinda yace sai tayi sak kuma ta gyara zama tace, "Me ya same shi?."
"Jinin sa ne ya hau."
"Allah ya bashi lafiya, ko nazo muje a duba shi?."
"A'a ki bari sai gobe."
"Allah ya kaimu" ta faɗa tare da yin shiru.

Kallon ta yayi ya ce, "kin ci abinci?." Ta ɗaga masa kai alamun eh tace, "Akwai naka ma in zaka ci, daman ni tuwon alkama na yiwa Mama shi naci, ga naka abincin nan a ajjiye."
"Girki biyu kika yi? Meyasa ni ma baki ajjiye min tuwon ba?."
"Ai na san baka ci."

Ta kalle shi jin bai bada amsa tace, "na kawo abincin?." Ya tashi yana cewa, "huta, zan ɗauko da kaina duk da bana jin yunwa ma" ya faɗa yana buɗe abincin yana zubawa a plate. Zai ci ne kawai dan kar ta sha wahala tayi bai ci ba, a yanayin da take ciki bata fashin yin girki shiyasa zai ta daure yaci ba dan yana jin yunwa ba sai dan in bai ci ba baza ta ji daɗi ba.

Dawowa yayi ya zauna ya fara ci amma bai ce komai ba itama bata ce ba, daman bai zuba da yawa ba ya cinye ya ajjiye plate ɗin. Ta kalli abincin da yake kan dining tace, "bara na saka shi a fridge gobe sai a bayar tunda dare yayi yanzu."

Hana ta tashin yayi ya tashi ya ɗauki abincin ya fita dashi, bai jima ba ya dawo da flaks ɗin ya kai kitchen ya wuce ɗakin sa. Tana nan zaune bai fito ba sai ta tashi ta kashe hasken falon ta wuce ɗaki ta zauna dan tasan yau yana cikin damuwa baya son yawan magana in yana cikin damuwa.  Tana zaunen ya leƙo ɗakin ya ce, "baza ki zo mu kwanta ba?." Tashi tayi tsaye ta ƙarasa bakin ƙofar ya riƙe hannun ta suka fita daga ɗakin zuwa na sa ɗakin.

BDƘB3P14

Washe gari tana bacci ma ya fita ya je asibitin yana zuwa ya samu Mamy tana nan kuma Abban ma ya farka idanun sa biyu sai dai har lokacin bai magana ba. Wajan Abban ya fara ƙarasawa bayan sun gaisa da Mamy ya ce, "Abba Sannu, ya jikin naka?."

Kai ya ɗaga alamun da sauƙi Bebi ya ce, "Abba magana zaka yi halan shine zai saka mu san kaji sauƙi." Mamy da take gefe tace, "faɗa masa, yaƙi magana tunda ya farka."
Abba maganar sa bata fita sosai ya ce, "da sauƙi." Bebi yaji daɗi a zuciyar sa ya ce, "Allah ya ƙara lafiya, Mamy ki je gida ki huta tunda nazo."

Da to ta amsa Bebi ya kira wanda zai kai ta ya bashi motar sa yace ya kai ta ya dawo. Tana fita Abba ya kalli Bebi ya ce, "Adnan zo nan." Bebi ya ƙarasa kusa dashi Abba ya ce, "ka cigaba da kula da ƴan uwan ka ko bani da rai kaji?, duk da daman kai ne mai kula dasu bani ba, ka cigaba da jajircewa akan lamarin ƴan uwan ka."

Nan take tsoron ya mamaye zuciyar Bebi amma bai nuna ba ya ce, "in sha Allah Abba, zaka samu lafiya amma sai ka rage damuwa a zuciyar ka, itace ta jawo maka wannan ciwon da ka ke fama dashi a yanzu."

Abba ya ce, "damuwa baza ta tafi ba a wajena Adnan, Sai dai ma damuwa ta ƙaru ba dai ta tafi ba, ni kaɗai na san abinda nake ji."
"Haƙuri ake yi Abba, Asara takin arzuƙi ce abinda aka rasa Allah zai mayar. Kuma tunda aka yi sa'a gobarar bata ci rai ba sai mu gode Allah." Abba ya kalle shi dan shi ba akan gobara yake magana ba, daman yasan tunda ya kulla alaƙa da zina ai dole ya dinga asara a rayuwar sa.

Abba ya sake kallon sa ya ce, "ka cigaba da haƙuri akan abubuwan da zaka ji suna ɓullowa a kaina, ka kula da iyayen ka da kowa na gidan kamar yadda ka saba, kar ka gajiya ka yiwa kowa abinda ya kamata daidai da rayuwar sa Adnan."

Bebi jikin sa yayi sanyi dan gani yake Abba kamar wasiyya yake bashi hakn ya saka ya zauna kusa da Abba ya ce, "Zaka tashi in sha Allah Abba, ai ciwon ba mai wahalar warkewa bane. Jinin ka ne ya hau sosai kuma yanzu ya sauka so nake ka samu hutu sosai a nan sannan ka koma gida, Mun tabbatar da ko bacci baka samu shiyasa abubuwan suka yi maka yawa amma zama a nan zai saka ka warware in sha Allah."
Chapter 25 · 0% Book details