Sashe 44
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Afuwa muka zo nema a wajan ki ko nace nazo nema a wajan ki, na yi laifin da bazan taɓa goge irin sa ba a rayuwata, na aikata kuskuren da girman sa ya wuce tunani wanda ake bawa labari. Ni mai laifi ne a wajan ki gaba da baya na sani, duk wani hukunci daga wajan ki na cancance shi saboda ban riƙe amana ba, ban kuma yi tunanin abinda zai biyo baya ba na aikata son raina ne na kuma tsallake nayi tafiya ta. Bani da abinda zance miki wanda zai wanke laifina, na san babu, kowa ma yasan babu shi a duniya. Na kasa nustuwa, a kullum tunani nake kamar mutuwa zata riske ni a ko yaushe tunda na haɗa idona dake, fargaba da tunanin mutuwa da haƙƙin ki ya gama mamaye min zuciya. Zahra don girman Allah ki yafe min, ki yi haƙuri don Allah ba dan halina ba kice kin yafe min, in baki yafe min ba ban san inda zan saka raina ba a wannan yanayin da nake ciki, bani da buri a yanzu illa naga kin ce kin yafe min duk da na san abu ne mai matuƙar wahala a wajan ki, amma ki duba Allah ba ni ba kice kin yafe min."
Muryar Daddy rawa take yi kowa a wajan ya tausaya masa har Manal da Mubeena, wani iri suke ji a zuciyar su jin yadda yake roƙon Mama muryar sa tana rawa, suka kalli Mama da tunda ta kulle ido bata buɗe ba. Hakan ya saka Baba yace, "Fatima don Allah ki yafe masa ko dan darajar ɗan sa Huzaifa." Ido ta buɗe ta kalli Baba yace, "eh, Huzaifa shine babban ɗan sa, shine yaron da yake faɗa miki a wancan lokacin yace miki yana da yaro guda ɗaya saboda. Na san Huzaifa ba abin yarwa bane a wajan ki, to ko dan shi ki yafe masa."
Kallon Huzaifa tayi taga yana zaune kusa da Adnan sun sunkuyar da kai, sai ta ɗauke kai ta kulle idanun ta tana girgiza kai. Zuciyar ta tunani take wanne tsautsayi ne ya kai ta ga amincewa da Manal ta auri Adnan oho, yanzu da duk wannan tashin hankalin bai faru ba, da tana nan lafiya lau babu abinda ya taso nata wanda bata son tunawa. Shiru falon yayi, babu wanda yake magana a cikin su sai kukan Ayan ɗin Manal wanda yake hannu Surayya, sai Surayya ta tashi ta fita tsakar gida tana jijjiga shi dan yayi shiru.
Daddy ya sake cewa, "Allah ya san zuciyata nayi dana sanin abinda na aikata, babu lallai ki amince a yanzu amma Allah shine shaida nayi nadamar abinda nayi miki dake da yarana. Kuma na koma har Zaria neman ki amma akace min ai bakya nan. Hankalina ya tashi na rasa inda zan neme ki, kullum cikin fatan Allah ya haɗa ni dake nake yi ko dan ki yafe min abinda anyi miki. Gashi yanzu na gan ki, don Allah don annabin rahama ki yafe min, ki yi haƙuri."
Baba ya kalle ta jin ta sake yin shiru kamar ba da ita ake maganar ba yace, "baki ce komai ba." Ta sauke numfashi ta cire glasses ɗin idon ta ta goge idanunta sake mayar dashi tare da kulle idon bata ce komai ba. Ɗakyar ta iya cewa, "to me zance? Wani lokacin bawa baya sanin ya aikata kuskure sai lokaci da nadama ta riske shi, daga wannan lokacin sai a fara dana sani ana kiran aikin shaiɗan ne. Bayan tun farko kai ne ka bawa shaiɗan damar da ya shiga zuciyar ka har ya samu gurbin zuga ka kai kuma ka ɗauki zugar sa, lokacin bama fahimtar hakan, amma da lokacin nadama tazo mana duk sai mu fita daga hankalin mu. Na rasa mahifiyata na zauna lafiya, na rasa mahaifina na zauna lafiya, na rasa ƴan uwana na zauna lafiya, ban san kowa a dangin mahaifiyata ba shima na zauna lafiya. Dawowar wani abu a rayuwa a yanzu bana tunanin zai bani farin ciki ko meye shi."
A hankali take maganar hakan ya saka Manal fara kuka, Mama ta kalli Manal da Mubeena da suke zaune Manal tana kuka. Manal ta kifa kanta a cinyar Mubeena tana kuka ita kuma ta riƙe bayan ta tana hawaye, Mama murmushi itama hawaye sun cika idon ta tace, "ƴaƴana ne, na rayu babu uwa da uba da kowa nawa, su kaɗai nake kallo naji farin ciki a zuciyata saboda ni ce na haife su, a kaf duniya basu da wani kamar ni bayan ni sai kai Baban su. Bana tunanin dawowar mahaifin su zai basu farin cikin da yafi wanda suke ciki a yanzu."
Baba ya kalle ta a tausashe ya ce, "Haka ne, amma mahaifi sunan sa mahaifi, Sai dai a kira wani madadin mahaifi ba mahaifi ba, dan duk inda mahaifi yake martabar sa daban take." Mama ta kalli Baba tace, "kuma har shi yana cikin masu martaba daban ɗinn?."
Baba yace, "shi ba mahaifi bane?." Sai tayi murmushi ta kawar da kanta gefe ta kalli saman ɗakin kamar mai karantar wani abu, ta sake sauke kai ƙasa ta rufe ido ta buɗe alamun ta rasa ma abinda zata ce.
"Shekarar Manal ashirin da huɗu zuwa da biyar, ta rayu a hannun wanda ba shine ya haife ta ba, ya saka ta a makaranta ya bata ci da sha da suttura, ya yi mata tarbiyya da har aka gani aka zo neman auren ta ya kuma aurar da ita. To wanne mahaifi zata buƙata a cikin rayuwar ta a yanzu?. Tana da uban da yayi mata abinda mahaifin bai yi mata ba, babu amfanim bayyanar wani da sunan mahaifi a wajan ta."
Baba yace, "maganar Manal da Mubeena duk babu ruwan ki a ciki, mahaifin su ne zasu iya ji sun yafe masa har zuciyar su. Yanzu a kan ki muke maganar ba a kan su ba." Mama tayi ƙaramar dariya ta kalli Huzaifa da ita yake kallo a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tace, "ni ban san abinda zan ce ba."
Sallama aka ji a tsakar gida ta mutane aka amsa kowa yayi shiru ana jira sun shigo cikin falon. Sake maimaita sallamar akayi a lokacin da aka shigo falon kowa ya bi su da kallo cikin rashin sani, Bebi ne kawai ya san maganar a amma babu wanda ya san su ko ya san da zuwan su.
Wanda ya shigo cikin falon yace, "Barkan ku, muna neman izinin zama." Baba ya kalle su ya kalli Mama da take kallon maza guda biyu farko da matan da suke bayan sa.
Baba yace, "bismillah ku zauna." Da yake falon na da girma sosai duk ya dauƙe su aka zauna. Alhaji Ahmaf yace, "Ku yi haƙuri mun katse ku, Gashi na san baku san mu ba." Mama kallon su take yi kamar yadda suke kallon ta suna murmushi. Baba yace, "gaskiya bamu shaida fuskar ba" ya faɗa dan yana so ya faɗa da kansa ne amma shi ya san shi.
Ya girgiza kai yace, "Sunana Ahmad Muhammad Jalingo, Yaya a wajan Zahra Muhammad Jalingo." Sauke kai Mama tayi ta kulle ido sai ta miƙe zunbur kamar an yi mata allura sai ganin ta suka yi a tsaye. Halima da take cikin matan ta taso ta zo wajan Mama tace, "Tabbas ke ɗom jinina ce Zahra, kin gane ni? Nice Halima Yayar ki, nice Halima da muke kwana waje ɗaya mu tashi waje ɗaya, nice waccs muke cin abinci tare, nice wacce komai namu yake zana iri ɗaya hatta kayan sakawa. Don Allah kar kice baki gane ni ba Zahra, kar kice baki gane ni ba, bani da laifin komai, nayi kukan barin ki gida tun a wancan lokacin, nayi kuku Zahra" ta faɗa tana kuka tana kallon Mama da jikin ta yake rawa sosai hawaye na zuba mata masu yawa.
Hannun Mama ta riƙe tace, "ki kalle ni, zaki gasgata da gaske ni ce, na jima ina neman ki, duk inda naga wani mai irin fuskar ki ko ta gwaggo sai na masa magana ko ya san ki?. Zahra don Allah ki kalle ni kar laifin da ban aikata miki ba ya yafe ni." Mama bata iya buɗe ido ba hawaye ne yake zuba wani yana bin wani, jikin ta ya fara rawa kanta yana mugun sarawa, da hannu ɗaya ta dafe kanta kafin a farga Mama ta suma a wajan.
A haukace Manal ta taso tayi wajan ta tana kiran sunan ta tana jijjiga ta amma ina Mama bata numfashi, kuka Manal take tana jijjiga tana cewa, "Don Allah Mama ki tashi, ki tashi Mama kar ki tafi ki bar mu, bamu da kowa sai ke, ke kaɗai ce gatan mu a duniya. Ku taimaka min Mamana bata numfashi." Mubeena ta taso tana kuka itama tace, "bamu buƙatar taimakon kowa, mu muka saba kula da ita kuma zamu cigaba da kula da lafiyar ta, Baba zamu kai Mama asibiti" ta faɗa tana zuwa kusa Maman tana girgiza ta.
Addah Halima da take tsaye a gaban Maman tace, "ni likita ce zan iya duba yanayin jikin ta, don Allah ku bani wannan damar" ta faɗa tana riƙe hannun Mama tana jin bugun zuciyar ta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Zuciyar ta na bugawa na wuce ƙa'ida, nunfarhin ta yana tsayawa ayi hanzarin tafiya asibiti" ta faɗa tana kuka sosai tana kallon Yayan su.
Da kansa ya tashi ya ɗago Mama daga kwance da take yana cewa, "Zahra kar ki yi mana haka don Allah, kar ki mana haka." Nan take hankalin kowa ya tashi ana ƙoƙarin fita da Mama daga falon Mubeena tace, "wallahi in wani abun ya samu Maman mu babu wanda zamu yafewa, mun haƙura da kowa a bar mu da ita daman da ita muka rayu."
Fita akayi da Mama hankalina tashe da kansu suka saka Mama a asibiti ba tare da sun san asibitin su waye ba aka wuce da Mamaa asibitin su Bebi.