Sashe 30
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni nafi son tafiya gida Allah."
"Sai ki yi haƙuri, ai na faɗa miki daman bana son zaman gidan nan bayan ina da ina baƙi zasu zauna" ya faɗa yana fita ya barta. Ba jimawa suka tafi gida Maman Surayya ta wuce gida da niyar haɗa kayan ta na kwana, su kuma suka wuce gida saboda Abba yaga yaron.
BDƘB3P16
Gidan Maman suka fara zuwa a kai mata yaron dan ta ganshi, Surayya ne da Mubeena a bayan motar yaron yana hannun Mubeena tace, "Manal ba sai kin fito ba bara ba kaina Maman saina dawo dashi." Surayya tace, "gaskiya dai ki zaman ki Milky, mu je Yaya Mubeena" suka buɗe motar suka fita.
Bebi ya kalle ta bayan sun fita ya ce, "sannu." Ta kalle shi ta daga kai ta mayar da ido ta kulle. Hannun ta har lokacin da flasta ya riƙe hannun nata ta sake kallon sa tace, "hannun ka sanyi."
"Me yake damun ki yanzu?."
"Ni komai ma damuna yake." Ya girgiza kai yace, "Sai a hankali."
Da Mubeena ta shiga da yaron Baba yana nan shi ta fara bawa ya karɓa yana yi masa addu'a yana cewa, "in da rai akwai rabo, hausawa suna cewa in da rai da rabo watarana jariri ango ne, yau ga ɗan da Manal ta haifa ne a hannuna, Allah mun gode maka." Mama murmushi take ya bata ɗan tana kallo tace, "ai wannan yaron babu ta inda ya bar Manal." Baba yace, "nima abinda na gani kenan, kama suke da ita kam sosai ma."
Ganin Surayya bata wajan sai Mubeena tace, "Mama wai Maman Surayya ce zata zauna da Manal?." Mama tace, "itace Mubeena." Mubeena tace, "kuma babu takura? Ni Sai naga kamar zata takura."
Mama tace, "babu yadda ban yi ba amma tace Manal ƴarta ce zata je har gida ta zauna da ita, ni cewa nayi ta dawo gida ma tace a'a mazan yanzu basa so zuwa wankan gidan na saai dai dole, tunda tana da yalwataccen wajen da za'a zauna gwara aje can ɗin. To kar na dage akan maganar taga kamar wani abun shiyasa na amince. Kuma daman Manal ta faɗa min baya so tazo gida, kuma Baban su Surayyan kinga yayi tafiya kuma ya kan yi sati uku zuwa huɗu baya nan."
Baba yac e, "gwara da kika amince, Balaraba ai ba ƙashin yar wa bace ba. Kuma tunda tace zata je ai ba wani abun bane tunda Adnan ɗin baya so yazo zaman gida." Mubeena tace, "Mama bani shi na kai musu suna mota." Mama ta miƙa mata shi tace, "kice ina mata sannu, shi kuma Adnan ɗin kice ina yi masa barka."
Mubeena ta amsa ta fita ta ƙarasa inda suke ta buɗe gaban motar ta bawa Manal yaron ta kalli Adnan tace, "Mama tace nace maka tana yi maka barka da samun ƙaruwa, Ke kuma tace tana yi miki sannu Allah ya ƙara lafiya, tace nace miki ta san ke raguwa ce babu abinda kika iya sai rakin tsiya."
Manal tace, "Mama baza tace min haka ba, wannan faɗar ki ce kawai." Mubeena tayi dariya tace, "Sai nazo Maman baby boy" ta faɗa tana kulle mata motar ta juya ta shiga gida. Manal kuwa ta rufe ɗan da mayafi tana cewa, "Rana tana damun shi." Murmushi yake ya ja motar suka tafi zuwa gidan su.
A harabar gidan su ya faka motar Kausar na ganin şu ta taho a guje ta buɗe gaban motar ta karɓi yaron a hannun Manal tayi cikin gidan da sauri. Ya kalle ta ya ce, "ki yi zaman ki zan kaiwa Abba shi." Manal tace, "kuma nazo sai na zauna a mota?."
"Eh haka nace." Kai ta ɗaga kawai ya wuce zuwa cikin gidan.
Basu jima sosai ba suka dawo ya shiga motar Kausar ta bata yaron tana cewa, "Sis meye sunan da zamu dinga faɗa masa?." Manal tace, "sai kin zo zan faɗa miki." Tace, "ai kam zan zo an jima kaɗan." Manal tace, "ƙarya." Kausar tayi dariya tana cewa, "wallahi zan zo in sha Allah." Manal ta amsa da Allah ya kawo ki ta rufe motar suka tafi.
Da suka je gida shi ya karɓi yaron ya shiga dashi gida ya kwantae dashi a kan kujera ya dawo ya riƙe ta suka shiga ciki. tana shiga falon ta kalli inda ya ajjiye yaron tace, "kai partner a kan kujera ka ajjiye min shi?, in ya faɗo fa?. Dan baka san zafin haihuwa ba sai ka bar min yaro a nan?" Ta faɗa tana ƙarasawa ta zauna tare da ɗaukar sa.
Shi dariya take bashi in yaga tana ji yaron, ya lura so zata yiwa yaron ba na wasa ba dan gashi ya fara ganin alamu hakan. ya ce, "Allah ya baki haƙuri wacce ta san zafin haihuwa, amma ina so na tuna miki ɗan Adnan ne."
"Eh na sani, amma rabin sa ne naka ba duka ba, dan ba kai ka shiga labour room ba. Kai other room ka iya shiga" ta ƙarasa faɗa ƙasa-ƙasa.
Yayi dariya ya ce, "ai na ji ki, wato ni other room na iya shiga ko?, to ai kinga an raba, ke kin shiga labour ni na shiga other room."
"Amma ai a labour room wahala ake sha ga azaba wacce ta wuce misali, can kuwa fa?."
Idon ta yake kallo ya ce, "can kuwa me ake ji? Shi nufin ki ba'a shan wahalar?." Ta ɗauke kai tana murmushi ya ce, "ki faɗa mana, an faɗa miki samar da cikin sauƙi ne dashi?." Kallon sa tayi tana taɓe baki tana ɗage gira alamun bata yarda ba sai tayi murmushi tace, "wanka nake so nayi."
Shima yai dariya ya ce, "okay jira na dawo" ya faɗa yana shiga ciki ba jimawa ya dawo yace, "kawo shi na kai ɗaki tunda kinga yayi bacci, ga baby bed ɗin shi can ma na haɗa miki" ta miƙa masa shi ya karɓe shi tace, "ko iya riƙe shi baka yi ba, nidai ka bi a hankali kar ka ƴar min da ɗana."
"To mai ɗa" ya faɗa yana dariya ya shiga dashi ya kwantar dashi tare da yi masa kiss a goshi, shi kansa ƙaunar yaron yake ba kaɗan ba amma ya lura in bai yi da gaske ba Manal zata danne tasa ƙaunar. A hanya suka haɗu tana takowa a hankali yace, "Yauwa ki dinga daurewa hakan shine zai saka ɗinkin ya warke da wuri."
"Kawai a ɗinke mutum kamar wata ƙwarya, ni ba sai a barni haka ba."
"A barki haka? Kin ƙaru fa."
"Eh zan ragu ne." Yayi murmushi yana biye da ita har banɗakin. Tana shiga banɗakin saka hannun ta acikin ruwan tace, "ai babu zafi sosai."
"Eh babu ke babu ruwa mai zafi sosai ɗin na ai har sai kin warke." Manal bata ce komai ba ya ce, "kafin zuwan Maman Surayya da kaina nake so nayi miki wankan saboda na kula da stitches ɗin sosai." Manal ta kalle shi tace, "Sai tazo taga ka fito daga banɗakin?."
"To akwai aibu ne?" Ya faɗa yana fara cire mata rigar jikin ta tace, "don Allah ka bari nayi da kaina" ta faɗa tana zama a gefen bathtub ɗin daƙyar. Ya girgiza kai yace, "da kaina zan miki kawai ki tsaya." Babu yadda zata yo haka ya mata wanka tas yana yi yana gasa nata jikin ta dan shi tazsan ta wahala wajan labour shiyasa yake tauyasa mata.
Sai da ta gama ta ɗaura towel ya riƙe ta suka fito ta zauna a gefen gado ya ɗauko mai ya shafa mata ya ɗauko kaya ya ajjiye a gefen ta, fita yayi ba jimawa sai gashi da trolly ɗin da aka je asibiti da ita ya buɗe ya ɗauko pad ɗin ta ya kawo mataya ajjiye, ya koma ya ɗauko undies ya ajjiye. Kallon ta yake yi ya ce, "na shirya ki?." Tayi murmushi tana kallon sa tace, "zan shirya kaina."
"Okay Madam" ya faɗa tana mata kiss a goshi tare da jan hancin ta yana murmushi itama tana yi.
Kallon sa take yi tana murmushi tace, "Bacci ka ke ji ko?."
"Sosai ma kuwa, wanka zanyi yanzu nayi sallah sai nayi bacci."
"Ya kamata, ka gaji da yawa."
"Duk gajiyata ban kai ki ba, kin yi ƙoƙari sosai na tabbatar da ke ɗin jarumar mata ce." Tayi murmushi tana kallon sa yana daga tsaye yana kallon ta tace, "kaje kayi sallar." Ya ɗaga mata kai ya fita ita kuma ta fara shiryawa zuciyar ta cike da farin ciki.
Tsab ta shirya cikin riga da siket kamar ba ita ce ta haihu ba, ta ƙarasa wajan Baby bed ɗin ta jawo shi da yake yana da taya ya a ƙasa biyo ta tazo dashi har wajan gadon ta zauna tana kallon yaron da yake bacci. A gefen ta taga wayar ta dan tasan shine ya ajjiye ita ina taga tunanin waya lokacin da suka bar gidan, ɗaukar wayar tayi tana yi masa hotuna masu kyau tana kallo tana murmushi.
Ya ɗan jima kafin ya shigo yana cewa, "Maman bata ƙaraso ba?." Ta kalle shi tace, "bata zo ba, kasan sai ta gama da komai na gida sannan zata taho. Sun barni ni kaɗai kamar mara gata, bayan in an haihu cika gida ake ana yiwa mai jego sannu. Ai ko Yaya da Surayya ne yaci ace sun biyo ni."
Yayi murmushi yace, "to ai baki yi kama da wacce ta haihu ba Manal, ni kaina mamaki nake yi. Amma nasan addu'ar da na dinga yi miki ce tayi tasiri, kullum fatana Allah ya raba ki da cikin nan lafiya gashi Allah ya amsa."
Tayi murmushi itama ya zauna kusa da ita yana kallon ta ya ɗauko yaron ya riƙe shi ya kalle ta ya ce, "kin san ya sunan shi?."
"Ba kace min sunan Abba ba?." Ya girgiza kai ya ce, "sunan sa Ibrahim Mu'azzam. Wanne suna zaki dinga faɗa masa?."