Sashe 83
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farida tana dariya tace, “Allah ya sa ya dawo ya ji ku.”
Mimi tace, “to ko ya ji mu yanzu ai ba da bane, sai dai hararar kawai.” Suka yi dariya gabaɗayan su kafin Yaya tace, “to ga wani turare ma ki shafe jikin ki tass dashi, ni so nake a daren nan a siya miki private get.” Mimi tace, “kin manta waye mijin nata ne?.” Manal tana dariya tace, “Yaya ta manta gaskiya, so take aljanun sa su tashi.” Suka yi dariya gabaɗaya Farida tace, “na ɗauka kin canja shi ai ashe hali yana nan.”
“Yana nan, baya son turare mai ƙarfi har gobe musamman ma wannan oil ɗin, kuma ko ya na saka sai ya gane shiyasa na daina.”
“Ahh bara na mayar jaka to, ni da nake so a baki jirgin sama in kika shafa ai ko keke baza ki samu ba.” Suka sake yin dariya suka cigaba hira da nishaɗi har suka tafi. Manal bayan ta sun tafi ta shanye abinda Yaya ta bata sannan ta shiga ciki ta shirya a lokacin taji ya shigo.
Har ɗakin ya bita yana yace, “kizo kici abinci tunda sun cinye wancan.” Manal ta biyo shi ta zauna a nesa dashi ya buɗe meatpie ne da fish pie, sai kuma basmati rice da salad. Ta ɗauki fish pie ta fara ci yana ci shi kuma yana kallon ta.
Guda uku tashi ta tashi ta shiga ɗaki ta shiga banɗaki tana wanke bakin ta ta fito ta ganshi ya leƙo suka haɗa yace, “Ayda ta tashi.” Yana faɗa ya juya ya fita daga ɗakin zuwa ɗakin sa. Fitowa tayi daga ɗakin ta ta shiga ɗakin nasa, tana shiga ya kulle ƙofar ta kalle shi ta kalli Ayda da yake bacci a nan ta fahimci wayo yayi mata.
Hannu ta harɗe a ƙirji ta kawar da kanta gefe bata ce komai ba. Ya riƙe hannun ta da yake ƙirjin duka biyu yace, “har yanzu baki huce ba?.” Bata ce komai ba yace, “babu wata baƙuwa da zata sake kwana a gidan nan in sha Allah, tunda bakya son hakan na daina.”
Manal tace, “ni wacece da zan hana baƙuwar ka zuwa gidan nan?.”
“Ke matar gidan.”
“Bani da wannan mahimmacin ai.” Ya karyar da kai ya ce, “maganar nan ta huce don Allah, indai Dr Zainab ce ko tazo zata sauka a hotel ba sai tazo nan ba.”
Manal tayi dariya tace, “in tana hotel ɗin ma sai ka biya ku yi hira?.”
“Ni na isa?, Babu inda zan je ko da tazo, duk abinda ya kamata a kai mata zan aika a kai mata.” Ta taɓe baki tace, “Waya da ita kuma fa?.”
“Abokiyar aikina ce kuma tana sama dani, ina samun ƙaruwa sosai in nuna tattaunawa da ita. Amma zan rage tunda bakya so.”
Kallon ido sa tayi tace, “zaka rage ba zaka daina ba?.” Ya girgiza mai yace, “in nace miki na daina ƙarya nake miki, gwara na faɗa miki gaskiya zan rage ba zan daina ba.” Ta girgiza kai bata ce komai ba yace, “yanzu batun ta ya huce, baza ta sake zuwa ba in sha Allah.”
“Meyasa take ce maka handsome? Sannan Meyasa ka ke bari tana taɓa ka?.”
“Wannan sunan tana faɗa min tun nuna makaranta har yanzu bata daina ba, kamar yadda a gida suke ce min Bebi basu daina ba har yanzu itama haka. Sannan a turawa take rayuwa, ita bata ɗauki riƙe min hannu wani abun ba, amma in zaki min adalci zaki ga ina kaucewa saboda na san haram ne.”
Manal tayi shiru ta sunkuyar da kai ƙasa ganin hakan sai ya samu damar riƙo ƙugun ta yace, “wannan fushin naki ne bana so, kin hora ni da yawa na kasa jure wannan shiru shirun naki. Na amince nayi laifi kuma bazan sake ba in sha Allah, amma ki saki ranki, ki bani dama na wanke laifina a daren nan.”
Ta kalli idanun sa da idanun ta da suka ciko da hawaye tace, “Kana sona har yanzu?.” Ya riƙe fuskar ta da duka hannayen yace, “soyayyar ki ƙaruwa tayi a zuciyata fiye da baya, ina son ki ina ƙaunar zama dake har a aljanna.” Ta kwanta a ƙirjin sa ya sauke ajiyar zuciya ya riƙe bayan ta yana lumshe idanun sa tace, “ina kishin ka sosai, kar ka yi min kishiya kaji.”
“In sha Allah dake kaɗai zan yi rayuwa har mutuwa.”
“Don’t sugarcosting me.”
“Ni na isa na yi miki daɗin baki?.”
“Ka dinga girmamawa Yayana.” Jin abinda tace sai ya ɗago ta daga jikin sa ya kalle ta sai tayi dariya shima yayi dariya yace, “dole ki yi dariya ai.” Ta koma jikin sa ta kwanta tace, “ina sonka my life partner.” Ya matse ta sosai a jikin sa yace, “nima ina son ki my life partner, Allah ya bar mu tare har aljanna.” Ta amsa da amin tana murmushin farin ciki shima kan sa farin cikin yake ji yana ratsa zuciyar sa.
Bayan wani lokaci.
Hajiya Manal ta zama shararriyar ƴar kasuwa fitacciya a ɓangaren iya sarrafa abinci. Abin ya kawo duk wani biki da za a yi a nigeria da ya amsa suna biki a ƙarƙashin gidan abincin Manal ake yin abincin biki. Lokaci kaɗan ta ɗaukaka matuƙa iyawar ta ya zaga ko ina dan ko yaushe cikin koyo ta ke, koyan girki ya kai ta har ƙasar dubai da america ta koyo abubuwan da itace ta fara sarrafawa ta siyar dasu a nigeria.
Tun yana ɓoye fuskar ta har fuskar ta ta zama sananniya a ko ina kowa ya santa. Ta sake yin haske jikin ta yayi kyau duk da baya yi ƙiba sosai ba amma ka da ka ganta ka ga hajiyan kuɗi kuma matar mai kuɗi.
Ɓangaren Adnan asibitin su ya bunƙasa sosai ya zaga inda basu yi tunani ba, sun samu kyauta daga ƙasashe sosai sun sake zamanatar da asibitin ta inda ya zama lamba ɗaya a arewacin najeriya. Ganin Adnan ma a asibitin wahala yake yi saboda baya zama yau yana wanna gari gobe yana wata ƙasa ganin sa sai da dogon booking ko da sanayya.
Rayuwa tayi musu daɗi ƙalubalen da aka fuskanta ya zama labari komai ya wuce farin ciki ya mamaye ko ina a dangin su.
Ranar juma’a Manal bata fita ba tana gida ganin lokacin masallaci ne sai ta haɗa wuta tana turaren wuta kafin ya dawo. Hayaƙin ya baibaye ko ina kawai sai gashi kamar an cillo shi.
Runtse idanu yayi ta kalle shi ta wara idanu tace, “yi haƙuri ban san zaka dawo yanzu ba.” Bai tanka mata ba ya wuce ciki ta kashe wutar ta kunna a.c sannan ta shiga wajan sa. A tsaye ta same shi sai yatsina ya ke yi tace, “ka yi haƙuri ban san zaka dawo yanzu ba, ina fatan bau ciwon kan ko?.”
Kallon ta yayi bayan ta ƙaraso ya ce, “haka ki ke yi kwana biyu, kin san bana son abu amma sai ki dinga yi.” Ta rausayar da kai tace, “ai na bayar da haƙuri ko?.” Wayar ta da take hannun ta ce take ƙara ta duba taga baƙuwar number ta ɗago ta kalle shi ya ce, “ɗauki.” Ba musu ta ɗauka ta zauna ana zancen abincin biki da ake so ayi tana faɗa musu yadda tsarin yake. Ganin yana kallon ta sai ta ce zata yi musu magana a whatsapp ta kashe wayar.
Murmushi ya yi ya ce, “Chef Manal.” Tayi murmushi tace, “Dr Bebi.” Ƴar dariya ya yi ya ce, “Wannan Bebi dai yaƙi barin bakin ƴan gidan mu da su Yayan ki, yarana biyu amma a dinga ce min Bebi.” Tayi dariya tace, “wannan suna ai bazai ɓata ba.” Ya sauke numfashi ya ce, “Su Ayan basu dawo bane?.”
“Tunda ka ganni a nutse har na samu damar yin turaren ƙhamshi ai basa nan, in suna nan ni na isa?.” Yayi murmushi ya ce, “in basa nan gidan baya daɗi.”
Ta zuba masa ido tace, “kenan ni hoto ce ko?.” Ya girgiza kai yana taɓe baki ya ce, “ni dai ban ce ba, kawai nace in ƴaƴana basa nan gidan baya daɗi.” Jin ya maimaita sai taji haushi har a fuskar ta ta nuna hakan. Bata yi magana ba ya ga tayi shiru yayi dariya kafin ya yi magana tace, “akwai wacce na yiwa alfarmar ganin ka ranar monday a asibiti.” Ya ɗage gira yana kallon ta ganin ta canja ya ce, “to har alfarma ki ka fara yi ban sani ba?.” Ta kalle shi tace, “ko ban isa nayi ɗin bane? In nima sai an bani long booking ɗin sai a faɗa min kar na wahalar da baiwar Allah.”
Dariya yayi ganin ta fusata ya ɗaga hannun sa ya ce, “wane mutum inji mutuwa?. Tuba nake ranki ya daɗe Allah ya kaimu monday ɗin.”
“Amin” ta amsa a taƙaice bata kalle shi ba.
Wayar ta ake kira ganin school ɗin su Ayan ne sai ta tashi ta fita ya bita da kallo yana dariya dan ya san ya tsokano ta. Babu jimawa sai ga Ayan ya shigo a guje ita kuma tana riƙe da hannun Ayda. Falon ya fito suka zauna tare gabaɗaya a nan suka ci abinci har lokacin bata saki ranta ba.
Bacci suka yi ta kai su ɗakin su ta zauna a ɗakin ta tana yiwa matar da suka yi waya bayani a whatsapp. Shigowa yayi ya jingina da bango yana kallon ta yana murmushi ya ce, “Kafin na samu Ayan da Ayda Ammi na fara samu, Ammi itace fitilar gidan Adnan, Ammi itace hasken da yake haska ko wanne lungu na dinga Adnan. Manal ɗina itace jin daɗina da walwala ta a cikin gidan nan.” Kallon sa tayi ya tako ya zo inda take ya ce, “ki daina fushi akan nace in su Ayan basa nan gidan babu daɗi, wasa nake miki kema kin sani.”