← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 84

Sashe 76

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban ta ya faɗi matuƙa jin maganar Adnan, ta wara ido waje ta waiwayo a hankali tana kallon sa. Yana tsaye daga nesa yana aiko mata da kallon da ya saka ta ruɗewa. Sam bata ji motsin sa ba balle ta san ya shigo sai maganar sa kawai ta ji a kanta.
A dabarbace tace, "sannu da zuwa." Ayan ya tashi a guje ya faɗa jikin sa shi kuma ya dauƙe shi yana murmushi yace, "ɗan gidan Mama, yaushe kazo?."
"Tare da Ammi muka zo, Abbie ka siyo min popcorn?."
"Ai ban san kana nan ba Ayan ɗina, da na san kana nan da zan siyo maka."

Zama yayi a nesa da ita Ayan na jikin sa yana yi masa surutu shi kuma yana biye masa suna hira. Tashi Manal tayi jiki a sanyaye gabaɗaya tsoro ya kama ta, tsoron sa take ji a duk lokacin da ta san tayi ba daidai ba ya haɗe mata rai. Duk da nature ɗin sa ce ɗaure fuska amma in tayi laifi yanayin daban yake. Abinci ta kawo masa bai kalli abincin ba ya riƙe hannun Ayan suka tashi suka shiga ɗakin sa. Shi kaɗai ya fito bayan ya canja kaya ya zauna ya fara cin abincin, har ya gama bai kalle ta ba kuma bai yi magana ba.

Sai da ya gama ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo ta zauna tayi shiru ta kasa magana. Kallon ta yayi ya ce, "sai nace ki faɗa min sannan zaki faɗa?." Manal ta sauke ajiyar zuciya tace, "takura min yake yi da magana a school bana kula shi, ban san a inda ya samu number ta ba ya fara kira na jiya. na faɗa masa ina da aure amma yace wai banyi kama da mai aure ba. Nayi blocking wancan number shine ɗazu ya canja number ya sake kirana har yanzu bai yarda ina da aure ba."

Yayi ƙaramin tsaki yace, "kenan bani da amfanin da zaki faɗa min tun lokacin da ya fara yi miki magana?." Manal tace, "kayi haƙuri, naso na faɗa maka tsoro nake ji."
"Tsoro! saboda dukan ki zan yi?. Wani banza yana yi miki magana a makaranta yana cewa yana son ki baza ki faɗa min ba?, Har ya samu lambar ki ya kira ki shima baki iya faɗa min ba?."

Ganin faɗa yake mata sosai sai sai tace "kayi haƙur...." Ka katse ta yace, "bazan yi haƙuri ba, in kika sake cewa nayi haƙuri sai na fasa miki baki. Ni zaki yiwa wannan wulaƙanci Manal?, Namijin da ba maharramin ki ba ya dinga yi miki waya har kina amsawa? Meya amfani na da ba'a ki faɗa min ba?."

Ta sunkuyar da kai tayi shiru bata ce komai ba. Cikin fusata yace, "dan tsabar shirme da tsabar shashanci wani yace yana son ki a makaranta baza ki faɗa min ba?, saboda kin raina ni ko?.” Nan ma tayi shiru bata ce komai ba yake yin dogon tsaki alamun ran sa ya ɓaci sosai yace, "meye sunan sa?."
A ray bane tace, "Malam Umar Haɗeja, yana koyar damu Food hygn." Kai ya girgiza ya tashi ya bar nata falon.

Ajiyar zuciya tayi bata so yaji maganar ba gashi yanzu abinda tazo masa dashi ya watse bazai saurare ta ba. Koda ta shiga ɗakin nasa ma yayi kwnaciyar sa shida Ayan, ta kalli gadon Ayan da yake gefe ta sake kallon sa tayi ajiyar zuciya. Ta kalle shi dan ta san idon sa biyu a sanyaye tace, "kayi haƙuri." Tsaki yayi bai ce nata komai ba ta zauna kawai tana kallon sa.

Da wuri yayi bacci ba tare da ya sake yi mata magana ba, ita kuma tana zaune tana kallon sa kafin ta tashi ta ɗauke Ayan ta saka shi a bed ɗin sa ta kwanta a gefen sa bacci ya ɗauke ta.

Da safe ta riga shi tashi lokacin da ya tashi har ta shirya Ayan ta gama haɗa breakfast. Yana tashi wanka yayi ya ɗauki key ɗin mota ya fita daga gidan, bai jima ba ya dawo yayi breakfast ya canja kaya ya sake fita bai ce mata komai ba.

Itama fita tayi ta shiga cafe ɗin ta ita da Ayan a nan suka zauna har la’asar sannan ta fito suka je gidan Mummy dan ta gaishe ta. A falon Mummy ta samu Bebi yana cin kilishi da take gaban Mummy a ajjiye. Ayan yana shiga ya tafi wajan Mummy a guje ta riƙe shi dariya tace, "A'a Ayan saukar yaushe?." Ya zauna a kusa da ita ta bashi kilishin yana ci sannan ta kalli Manal suka gaisa Mama tace, "shine kika je kika ɗaukowa Mama shi?."
"A'a wallahi, jiya ne da naje ya ganni sai ya maƙale min."
"Amma Ayan ba alƙawari" Mama ta faɗa tana jan kumatun sa. Mama tace, "Manal kici mana." Ɗauka tayi tana ci Adnan ya tashi ya fita Mama ta kalle ta tace, "Ya makaranta?."

Manal tace, "Lafiya lau Mummy, jiya Mama tace na gaishe ki." Mummy tace, "ina amsawa" ta faɗa tana murmushi. Mummy ta sake cewa, "Kausar tazo tana ta ciwon baki tace baki je ba." Tayi dariya tace, "Wallahi Mummy yau nayi niyar zuwa, to ban samu dama ba har yanzu."
"Ai na sani na faɗa mata, nace laifin Yayan ta ne." Manal tayi dariya tana cin kilishin.

Ganin magriba tayi sai ta miƙe tace, "Mummy bara na wuce." Mummy tace, "baya son tuƙin dare ko?."
Ta ɗaga kai tace, "Baya so."
"Allah ya kiyaye. Ayan ka tafi ko?." Ya maƙale kafaɗa alamun bazai tafi ba, Mummy tace, “a nan zaka zauna?.” Ya ɗaga kai alamun eh Manal tace, "Mummy na bar miki shi" ta faɗa tana murmushi ta fita ta hau mota ta tafi gidan ta.

Ko da ta koma aallah tayi sannan tayi masa abinci tana ta sauri kar ya dawo, tana gamawa ta shiga wanka a lokacin ya shigo ya sake fita sai da yayi sallar i'sha sannan ya dawo. Da ya shigo ya same ta a zaune akan dining bai ƙarasa ba ya zauna akan kujera yace, "Kawo min abincin nan." Ta amsa ta ɗauko ta kawo masa ta zuba masa ya fara ci itama tana ci a plate ɗin da yake ci.

Yana gamawa ya tashi ya shiga ciki ya tare da yace mata komai ba. Ta san fushi yake da ita shiyasa yaƙi yi mata magana, ta kwashe ragowar abincin na cikin kwanon ta kaiwa mai gadin gidan sannan ta kai kayan kitchen ta ajjiye ta shiga ɗakin ta. Kayan ta cire ta saka na bacci ta saka body mint ɗin da yake so a jikin ta sannan ta wuce zuwa ɗakin sa.

A zaune ta same shi yana danna waya ta ƙarasa ta zauna a kusa dashi ya kalle ta ya ce, "Ayan ɗin fa?." Manal tace, "yace a wajan Mummy zai kwana." Shiru yayi bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi. A raunane tace, "kayi haƙuri, na san nayi maka laifi amma ka yafe min don Allah." Kallon ta yayi ya ɗauke kai bai yi magana ba, ta sake cewa, "Don Allah, Don Annabi ka yi haƙuri. Bazan sake ba in sha Allah."

"Saboda kawai kin raina ni, kin raina aurena da yake kan ki wani yana cewa yana son ki a waje baza ki iya faɗa min ba. Harda samu number ki yana kiran ki shima baki sanar dani ba. Dan tsabar kin gama raina ni sai kika ce wai tsoro kike ji, dukan ki zan yi in kin faɗa min ko me?." Ta riƙe hannun sa duka biyun tace, "kayi haƙuri don Allah, nayi laifi na sani amma kayi haƙuri bazan sake ba."
"Bayan shi sai waye?."

Manal tace, "babu kowa."
"Ban yarda ba, domin ina zuwa school ɗin ɗazu ina faɗar sunan ki shugabar makarantar taku tambaya yake daman da gaske kina da aure. Manal ki faɗa min waye bayan shi?." Ta fara kuka tace, "Wallahi!, Wallahi!! bayan shi babu kowa, in akwai za’a faɗa maka."

"Naji. Meyasa suke miki kallon baki da aure? Ɓoyewa kike yi bakya so a san ke matar aure ce?." Ta rausayar da kai tace, "ta ya zan rufe darajar da Allah yayi min?, Wallahi bana ɓoyewa kowa faɗa nake ni matae aure ce a ko ina. Kuma har da Ayan ina zuwa, an san ni na haife shi.” Ya girgiza kai yace, "ban lamunci cigaba da saka abaya in zaki je makaranta ba, dole ki dinga saka dogon hijjab kamar yadda kike yi a baya."

Manal tace, "to, daman kuma bana shigar banza kafi kowa sani."
"Na dai faɗa miki, gwara ma ki yi kiyi ki gama makarantar a huta." Tayi shiru jin abinda ya ce kamar ba shi ne ya takura mata akan karatun ba. Jin yayi shiru sai ta kalli fuskar sa tace, "ka yi haƙuri." Ya kalle ta ya ce, "ya wuce, amma kar ki sake ɓoye min irin wannan ko a makaranta ko a hanya, yanzu da naji labari naje school ɗin naku nayi musu gargaɗi, in ya sake yi miki magana ki faɗa min."

Manal tace, "to zan faɗa maka in sha Allah." Baice komai ba ya cigaba da danna wayar sa.

Tayi shiru bata ce komai ba sai wasa da hannun ta da take yi. Ya ɗago ya kalle ta ganin alamun da magana a bakin ta ya ce, "me kike son cewa?." Manal ta kalle shi tace, "to ka ƙi ka saki fuskar ka, akwai abinda nake so na faɗa maka wannan fuskar ce bana so.” Ya kalle ta yace, "me kike so kice?."

"Don Allah kayi dariya, na fa baka haƙuri kuma kace ka haƙura."
"Abin ne yake min ciwo, matata ace wani yana bibiyar ta a waje kuma bata faɗa min ba. Bazan ɓoye miki ba kin bani haushi kuma kin ɓata min rai." Manal ta kulle ido jin ya dawo da maganar da ya ce ta wuce tace, "ka yi haƙuri, bazan sake ba in sha Allah."
Chapter 76 · 0% Book details