Sashe 82
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manal tayi shiru bata amsa ba ya kalle ta ya ce, “kin yi shiru.” Ta ja numfashi tace, “Zuwan ta bai dame ni ba, ko kwana ɗari zata yi a gidan nan bazai ɗaga min hankali ba saboda ba a kaina zata zauna ba. Duk da gidan ka ne ba nawa ba, kana da ikon yin duk abinda zaka yi a cikin sa, amma kasan ni ma a gidan nake zaune yana da kyau in zaka yi baƙuwa ka sanar dani zuwan ta ka kuma faɗa min a nan zata zauna kafin tazo. Ban san da zuwan ta ba sai ganin ta kawai nayi, sannan baka ce min zata kwana ba sai bayan tazo. Ta fito falo da kayan bacci kamar matar gidan ta zauna, kaima ka zauna kuna hira da ita har ta dinga taɓa ka saboda daɗin labari. Daga ƙarshe sai abin ya zama har faɗa ka dinga yi min a kanta, ka share ni ko abinci da ita ka ci ka manta ma dani. wacece ita da zaka yi min faɗa har haka a kanta?, wacece ita da ka tattara nutsuwar ka gabaɗaya a kanta har ka manta dani?.”
Ya kulle ido ya buɗe yana kallon ta, kafin yayi magana ta tashi tsaye tace, “tunda tazo ko abincin na daina ci kayi, baka damuwa da naci abinci tunda tare ku ke ci kai da ita. Da kace min ka tafi kai ta baka dawo min ba sai dare ka dawo kana cewa na faɗawa Yaya Huzaifa dukan ka zai yi. Ba dukan ka zai yi ba, na faɗa masa ne dan na ji sauƙin abinda nake ji a zuciya ta saboda shi ɗin jinina ne, ban damu ba dan baka kallon sa a haka, ni a matsayin jinina nake kallon sa. Bayan duk abin nan da kayi min sai ka daina shiga harkata, fuska a ɗaure ka ke dawowa kullum a haka ka ke komawa. Sai dai naji kana waya da ita kana yi mata bagajiya bayan ni baka san ya na kwana ba. Shekara biyar da auren mu amma har yanzu na kasa fahimtar ka, ko laifi kayi min a ko yaushe ni ce mai laifi ba kai ba, amma in nice nayi laifin ba kai ne kayi ba ni ɗin ce. Tunda haka ka zaɓa shikenan” ta faɗa tana wuce shi ta fita daga ɗakin.
Dafe kai yayi bayan ta fita, tabbas bai kyauta ba duk abinda ta faɗa haka ne, ya kamata ace ya faɗa mata kafin zuwa Zainab. wannan shine kawai laifin sa da ya gani amma shi bai ga laifin zuwan Zainab ba.
Kukan Ayda ya jiyo sosai hakan ya saka shi ya taso ya fito falon ya same ta sai kuka take yi ya karɓe ta yace, “me ya same ta?.” Manal tace, “faɗuwa muka yi ni da ita, shine kanta ya ɗan bugu.” Jijjiga ta yake a kafaɗar sa ita kuma ta zauna a kujera tana kallon hannun ta da ta faɗi a kai tana goge hawaye.
Bacci tayi a kafaɗarsa ya wuce da ita ɗakin sa ya kwantar da ita a gadon wanda yake kusa da wanda Ayan yake bacci. Ya dawo falon ya zauna kusa da ita ya kalle ta yace, “ki zo muje ki kwnata tayi bacci.” Ta girgiza kai bata ce komai ba ya miƙe yace, “muje ko?.”
Ta kalle shi tace, “zan shigo.”
“Ki tashi mu tafi tare.” Kawar da kai gefe tayi bata ce komai ba kafin ta tashi ta wuce ɗakin bata kalle shi ba. Tunda yaga ta kwanta a can ƙarshen gadon ya san abinda yake nufi, shima bai tunkare ya ba ya share yayi baccin sa kamar yadda tayi bacci.
Sai da aka sake kwana biyu Manal bata dawo daidai ba tun yana ganin abin kamar wasa har abun ya dame shi ya fara neman hanyar shiri amma taƙi bada dama, sai dai yayi magana ta amsa ta ajjiye masa abinci wani lokacin ma kafin ya tashi ta fita ta tafi cafe ɗin ta. Duk ya damu saboda ba haka suka saba zaman ba, ya jure shirun na ta amma ya kasa shiyasa yake shige mata amma ko sauraren sa bata yi.
Da yammacin ranar asabar ta dawo daga cafe ta shigo falon tana kallon agogo dan lokacin magriba ya kusa, ta sauke ajiyar zuciya saboda gajiya a bayyane tace, “na gaji yau..”
“Hello my love, welcome back” ya faɗa yana kallon ta da murmushi a fuskar sa yana ƙarasowa inda take.
Kallon sa take har ya ƙaraso ya karɓi Ayda da take hannun ta yana yi mata wasa. tace, “Yauwa, ashe ka dawo?.”
“Na dawo ina ta jiran ki.”
“Yau akwai customers sosai a can, na kuma gana da wasu guests ne suna so zamu yi serving ɗin su a events ɗin da zasu yi, shiyasa na daɗe.”
“Good. yanzu ki shiga ki yi wanka ki huta ga abinci na gama haɗa miki.” Kallon sa tayi yayi mata murmushi ta ɗauke kai tace, “Okay” abinda tace kenan a taƙaicr ta wuce ciki.
Bata fito ba sai da tayi wanka dan taji alamun tafiyar period ɗin ta sannan tayar da sallar da ta wuce ta. Tana idarwa ya shigo yana kallon ta yace, “oh ashe period ɗin naki ya tafi. Anyway, mu je kici abinci.”
Kallon sa take yi kafin ta tashi tsaye ta biyo bayan sa ta zauna a akan kujera ya zuba mata basmati rice da gasheshshiyar maza da kuma salad, ta kalle shi dan ta san a wajan leemars_delicious yayi order, yanayin ƙhamshin abincin ya tabbatar mata da abincin ta ne dan ƙhamshin abincin ta na daban ne. Ta hana shi cin abincin matar nan amma kamar tayi masa asiri a abincin, in yace ya dai bazai iya ba sai dai taga kawai ya siyo. Ta iya girki sosai, ta iya abinci mai daɗi musamman mandi rice ɗin ta in kana ci sai ka ɗauka a saudia ka ke, har ta ta taso tafi ta saudia daɗi saboda ita da ɗanɗano ta saudia kuwa haka take salam. Iya abincin ta ne ya saka Manal take kishi da ita, akan me duk iya girkin ta ya kasa haƙura da cin abincim matar nan?.
“Abincin leemars_delicious ne don Allah ki ci, kinga basmati rice ce ga salad.”
“Amma nace bana son abincin matar ban ko?, Kenan abincin ta yafi nawa daɗi?.”
“Haba Manal me ya kawo wannan maganar?, saboda na hutar dake ne ya saka ni na siya ba wani abu ba.”
Manal tace, “ni dai bazan ci ba.”
“Saboda a waja ta na siya baza ki ci ba?.”
“Kafi kowa sanin bana so ai ko?.”
“Ba da wani abun na siya ba fa, saboda ke ne.”
“Shiyasa nace bana ci.”
Zai yi magana kenan aka yi sallama aka shigo suka kalli masu shigowar tare da amsa sallamar, Yaya Farida ce da Mimi da kuma Kausar. Ɗan ɓata rai yayi dan bai ji daɗin zuwan su ba, ita kuma Manal ta taso daga kan dining ɗin tana murmushi tace, “Barkan ku da zuwa, daga ina haka?.”
Mimi tace, “biki muka je muka biyo nan mu yi sallah.” Manal ta zauna kusa da Kausar kafin tace, “Yaya ina yini.” Yaya Farida ta amsa tana kallon Bebi da yake a tsaye ya harɗe hannayen sa a kƙrji yana kallon su tace, “Ko mu koma ne?.”
Manal ta kalle shi suka haɗa ta ɗauke kai ya kallo Farida yace, “kawai sai nace ku koma?. Daga ina haka da daddare?.” Farida tace, “daga biki muke, ina Ayda da Ayan ɗin?.”
“Ayda tayi bacci, Ayan kuma…” ta faɗa tana kallon Bebi dan bata ana inda ya kai shi ba ita kuma bata tambaya ba. Bebi yace, “yana wajan Mummy.” Mimi tace, “Mama dai na ji da Ayan.” Kausar tace, “to ke sunan miji wasa ne?.” Suka yi dariya har Manal kafin tace, “ga abinci.”
Mimi ta tashi tace, “bara nayi sallah naci abincin.” Kausar ta tashi ta shiga ciki tana cewa, “ni ma dai sallah zan yi.” Falon ya rage daga Farida sai Manal dashi da yake tsaye sai kallon Manal yake yi. Yaya Farida ta kalle shi ganin Manal yake kallo, ta kalli Manal da ta ke ɗauke da yarom Kausar tana yi masa wasa.
Tayi dariya hakan ya saka Manal ta kalle ta tace, “ina su Baby?.” Farida tace, “suna gida,yunwa nake ji.” Manal tace, “bara na kawo miki.”
“A’a yi zaman ki” ta faɗa tana tashi ta ƙarasa wajan dining ɗi.
Bebi ya kalli Manal yace, “zan je na dawo.” Ta ɗaga kai kawai ya kalli Farida yace, “Nasan kafin na dawo maybe kun tafi.” Farida tace, “gaskiya dai ba jimawa zamu yi ba.” Ya buɗe ƙofar ya fita.
Hira suka dawo suka tayi suna cin abinci ana dariya cikin nishaɗi. Farida ta ɗauko wani abu a leda ta bawa Manal tace, “an kawo mana shi daga sokkoto bashi da matsala ki karɓa kema ki sha.” Manal kunya ta kama ta amma ta saba indai Farida ce ta saba bata irin wannan kayan.
Manal tace, “To Yaya na gode, Allah yasa babu zaƙi” ta faɗa tana buɗe murfin robar tana kallon maganin. Kausar tace, “babu zaƙi ko kaɗan, kuma yana da kyau sosai.” Farida tace, “Shiyasa na bata ai, dan a taimakawa ƙanin nawa da alama fushi ake yi dashi, yadda ya barwa Mama Ayan a yau a taimaka a taimaka masa.” Manal ta fasa sha tana dariya.
Mimi tayi dariya tace, “ai gwara tayi masa haka, shima baya raga mata.” Manal ta kalle ta tace, “Allah yayi miki albarka, in yana yi min faɗa kamar bai taɓa sanina ba ko kuma abokan gaba ne ni dashi.” Kausar tayi dariya tace, “Yaya Bebi manya, har yanzu halin sa yana nan babu inda yaje.”
Manal tace, “hali ai baya canjawa, ni gani nayi ma har gwara da akan yanzu.” Mimi tayi dariya tace, “kice dai kawai an samu cigaba a lamarin na sa. Kai Yaya Bebi bala’i ne, in ya fara zazzaga masifa baya ji baya gani. Sai dai kuma yana ji dake fa.” Manal tayi dariya Kausar tace, “eh ai gaskiya ne, yana ji dake ko yayi faɗan ma zai bada haƙuri. Wani kallo yake yi miki yanzu kamar ya ɗauke ki, ni na san Yaya Bebi ɗan soyayya ne.”