Sashe 40
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bebi ya tausasa murya ya ce, "Manal Mahaifi ne fa." A ɗan fusace tace, "shi din fa, ina ruwana dashi? Muna da Baba ai, yayi mana abinda har ya mutu bazai yi mana kwatankwacin sa ba. Maman mu ta rayu babu uwa, babu uba, babu dangin uwa, babu dangin uba, babu yaya, babu ƙanwa, babu uban yaran ta. Ta rayu duka babu waɗannan a gefen ta sai mijin da Allah ya bata mai jin ƙai, sai kuma maƙociya da take da ita kamar ƴar uwa. Ita ta rayu babu waɗannan jigogin a gare ta ta rayu kuma lafiya lau har ta kai ga aurar da ƴarta lafiya ba tare da wata damuwa ba. Mu kuma dan kawai babu mahaifin mu sai mu kasa rayuwa?. Ina da uwa, ina da uba, ina da Yaya, ina da kai kuma, to me zai dame ni?. Wallahil azim har addu'a nake yi yanzu akan kar Allah ya haɗa fuska ta da ta mahaifin mu in yana raye, in kuma ya mutu Allah ya jiƙan sa, amma fatan haɗuwa dashi ko dangin Mama bana yi saboda na tabbatar daga ranar Mama ta haɗa ido dashi ko dangin ta babu lallai ta kwana lafiya, ni kuma wannan shine babban abin baƙin cikina, ba kuma zan yafe musu ba, lokaci ɗaya tsanar su zata yi min dirar mikiya a zuciyata."
Ganin yadda take maganar a fusace kuma har zuciyar ta maganar take fitowa sai ya tausasa murya yace, "duk abin bai kai haka ba ai, ita rayuwar nan da muke ciki ba dan Allah yana yafe mana laifin da muke yi masa ba da dukkan mu bama doran duniya, Allah da ya halicce mun yi masa laifi ya yafe mana balle kuma ɗan adam ɗan uwan ka? kuma mahaifin ki ne duk da wannan abubuwa da kika lissafi biyayya a gare shi a wajan ki, ba dan komai ba sai dan albarkacin sunan mahaifi a wajan ki."
Manal tayi ƙaramin tsaki tace, "balle ma baza mu haɗu ba har abada balle hakan ta kasance, ni Wallahi gabaɗaya ka ɓata min rai da maganar nan" ta faɗa fuska a ɗaure tana kawar da kai gefe.
"To Manal meye na ɓacin ran? Abu ne wanda zai faru a yanzu ko nan gaba."
"Bana wannan fatan, bana so ganin sa ya sha zaman sa a inda yake mu ma muyi zaman mu a inda muke." Ya sauke numfashi yace, "hmm Manal kenan."
Ta kalle shi tace, "Wai me ya kawo wannan maganar?."
"A jikina nake ji kamar mahaifin ki ya kusa nuna kansa."
"To ka daina jin hakan, bana so wallahi. A yadda nake jin zuciyata ba dan kai ne ka ke min zancen sa ba wani bai isa yayi ba. Don Allah kaima ka bari haka."
"Shikenan na bari" ya faɗa yana riƙe hannun ta.
Miƙewa tsaye tayi tace, "zan je na kwanta dare yayi sosai." Ya kalle ta yana daga zaunen yace, "ki kwana a nan." Ta girgiza kai tace, "Mama fa tana nan, kawai sai ta farka bata ganni ba?."
"Ai ta san inda ki ke, kuma ita Mama bata ce kar ki kwana a wajena ba ko?." Manal ta turo baki tace, "eh bata ce ba, amma dai..." katse ta yayi yace, "please Partner ki kwana a nan."
Ta kalle shi tace, "To Ayan ɗin fa? Anytime zai iya farkawa."
"Sai mu dawo dashi nan." Tayi shiru tana kallon sa alamun tunani yace, "ki ɗauko baby bed ɗin nasa ya kwana a nan." Ta sauke ajiyar zuciya ta fita ya bita da kallo yana jinjina lallai za'a sha artabu da ita akan Daddy, amma yasamn zata yi sanyi da zarar ta tabbatar da mahaifin ta shine mahaifin Huzaifa, Tabbas Daddy zai ci albarkacin Huzaifa a wajan ta da wajan Maman ta.
Da Ayan ɗin ta dawo a hannu ya tashi tsaye ya karɓe shi ya kwnatar dashi a kan gadon yace, "ina nashi gadon?."
"Bana so Mama ta farka shiyasa ban ɗauko ba" ta faɗa tana zama a gefen gadon. Kwanciya tayi a gefe ya kashe hasken ɗakin ya kwanta a gefe shima ya zama Ayan ɗin yana tsakiya ya matsa kusa shi yana kallo yana wasa da kumatun sa.
Tashi taga yayi ya ɗauke Ayan ɗin ya mayar dashi bayan sa ya yi masa makari da filo, ya matso kusa da ita ta kalli Ayan ta ce, "ya zaka mayar dashi baya in ya faɗa fa?."
"Bazai faɗa ba, baki ga na kare shi ba?."
"To sai kayi bacci ka danne shi? Nidai ka dawo dashi kusa dani yayi min nisa."
Jawo ta jikin sa yayi yace, "shi bakya so yayi miki nisa ni kuma kina so nayi miki nisa ko?." Kafin tayi magana ya kuma cewa, "saboda shi ke kika haife shi ko?, kin fi ji dashi a kaina?." Ta kalli idanun sa ta turo baki gaba tace, "to shi fa jariri ne, kai fa?.".
"Nima jariri ne a wajan ki, in kika so zaki mayar dani kamar shi."
"Kamar shi? Shifa baya cin abinci ka manta ne?."
"Nima sai na daina ci, na koma shan abinda yake sha."
Ta wara idanu waje tace, "eyee!." Ya ɗaga mata gira yace, "uhum" ya faɗa yana haɗa fuskar sa da ta ta. Tayi dariya tace, "kace zaka zuƙe ni ne kawai."
"Shi Ayan ɗin ya zuƙe ki?."
"To kai dashi ɗaya ne?."
"Ɗaya ne mana, ni na fishi ma dan ni ɗan kaɗan zan dinga sha."
Tayi dariya tace, "ban yarda ba."
"Ni kuma na yarda daga yau za'a fara, bara ki ga." Da sauri ta riƙe hannun sa tace, "A'a don Allah, yi haƙuri dai."
"Yau bakya so?." Ta kalle shi ya ɗaga mata gira yace, "ki bani amsa, yau bakya son na...." Ta rufe masa baki da hannun ta tana girgiza kai.
Yayi dariya ya cizi hancin ta yace, "matsoraciya."
"Uhum naji ɗin."
"I missed you" ya faɗa yana sake riƙe ta sosai a jikin sa. Ta riƙe shi itama tace, "duk da ba wani sosai nayi kewar ka amma dai nayi."
Yayi dariya yace, "mai ƙarya..?." Bata ce komai ba ta kwanta a jikin sa tana dariya ya riƙe ta yana sauke ajiyar zuciya. Rumana ke zuwa zuciyar sa da maganar Daddy, bai san ya zai yi da batun Rumana ba, Allah ya sani baya buƙatar a tarwatsa masa farin cikin gidan sa, dan furtawa Manal zai auri Rumana daidai yake da lalata farin cikin gidan sa.
Sai asuba Manal ta koma ɗaki duk kunya ta ishe ta suka gaisa da Mama bata ce mata komai ba sai karɓat Ayan da tayi tace, "Sarkin haƙuri wani lokacin sarkin rigima, ki canja masa pampers ɗin jikin sa." Manal ta amsa da to ta ɗauko pampers ɗin amma ta kasa saka masa, Mama tayi dariya tace, "ai kuwa ke zaki saka masa, bazan karɓe shi ba anjima ma ke zaki yi masa wanka."
Manal tayi dariya tace, "Allah yasa kar na shaƙa masa sabulu a hanci." Mama tayi dariya tana nuna mata har ta saka masa sannan ta kwanta itama Maman ta kwanta. Sai kuma Ayan ɗin ya farka yana kuka, Manal ta tashi ta fita dashi falo yana kafaɗarta yana jijjiga shi amma yaƙi shiru, ta zauna ta bashi nono amma yaƙi yayi shiru duk ta ruɗe.
Adnan ne ya fito har ya shirya da kofi a hannun sa yana shan yourgut. Ganin ta a ruɗe gashi yana kuka ya ƙaraso ya karɓe shi yace, "lafiya yake kuka?."
"Nima ban sani ba, yaƙi yayi shiru kuma."
"Ko bashi da lafiya?" ya faɗa yana duba jikin sa har lokacin kuka yake sosai.
Manal ta ruɗe kamar zata yi kukan ita tace, "ban sani ba."
"Ba yunwa yake ji ba kuma?."
"Yaƙi karɓa, Sai kuka yake yi."
Mama ce ta fito da hijjabi a jikin ta jin muryar Adnan ya saka ta sako hijjabi, tace, "rigima ce irin tasa, kawo shi" ta faɗa tana karɓat sa a hannun Bebi ya gaishe da Maman ta amsa kafin yace, "Mama anya ba wani abun ne yake damun sa ba?." Mama tayi dariya tace, "Lafiya lau yake wallahi, gashi yayi shiru." Mama ta kalli Manal tace, "shiyasa nace miki zan dinga bar miki shi, rainon nashi ne baki iya ba shiyasa yake wannan kukan" ta faɗa tana shiga ciki.
Manal ta sauke numfashi ta dafe kai tace, "duk ya ruɗa ni." Bebi yace, "Lallai duk ranar da Mama ta tafi za'asha aiki, mata kuma iyaye zasu yi aiki." Ta kalle shi yayi murmushi ya ɗauki glass cup ɗin sa yace, "zan fita."
"Baka yi break b?a." Ya nuna mata cup ɗin hannun sa ya ce, "wannan ya isa."
"Kwana biyu baka son cin abinci, ka tsaya na kawo maka, akwai doya da kwai ta jiya sai na yi warming."
Hararar ta yayi yace, "ke ni fa ke kaɗai za'a yi warming a kawo min na ci, amma in ba ke ba bana cin abu jiya na maimaita shi yau." Manal tace, "to ni abinci ce?." Numfashi ya sauke yana kallon idamun ta ya zuba hannayen sa a aljihu yana yi mata kallon ƙasa-ƙasa tare da lashe lips ɗin sa.
Dariya tayi ta rufe ido da hannun ta dan ta fahimci mai hakan yake nufi, idanun ta a rufe tace, "Ashe nima sai an ɗumama ni kenan?." Yayi ƴar dariya ya kalli ɗakin da Mama ta shiga ya sake kallon Manal yace, "ke ai ko kwana dubu ki ka yi ko babu warming i will enjoy it" ya faɗa yana kashe mata ido.
Dariya tayi tana girgiza kai tace, "ashe iyayin naka bai yi nisa ba, na ɗauka har ni ai." Yayi dariya tare da girgiza kai yace, "wato kin haihu yanzu kin yi free ko?, saboda kina ganin har yanzu baki da tsarki ko?, Shikenan zan kama ki" ya faɗa yana ƙarasowa ya yi mata kiss a goshi ya juya ya fita.
Yana fita gida yaje wajan Abba amma sai ya tarar duk gidan bacci suke dan lokacin ko tara na safe bata yi ba. Yana niyar fita daga falon Mama Rumana tace, "Ina kwana Yaya Adnan." Kallon ta yayi ta zuba masa ido saboda yayi kyau cikin black ɗim suit mai kyau da laushi yace, "Lafiya Ruman, ya jikin ki?."