Sashe 20
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Burin ki zai cika ai, tunda bakya son cikin zai fita da kansa kin ga kema sai ki huta." Da sauri ta kalle shi tana goge ido tace, "Allah ina son cikin, wahalar dani da yake yi ne bana so." Ya ɗauke kai daga kallon ta bai ce komai ba tace, "ka yi haƙuri, in sha Allah bazan kuma sha ba. amma ka dinga min addu'a wallahi bana sane nake yi, tunda na samu cikin nan na canja, nima bana so nake sha saboda lafiyata" ta faɗa murya na rawa tana goge idanun ta.
Sai ta bashi tausayi duk fushin da yake yi da ita ya kau daga zuciyar sa, tabbas ciki ne ya saka ta aikata hakan ya sani kuma babu abinda ta isa tayi a kai. Shi shaida ne a baya sugar ɗin ta ƙasa yake yi har sai an so ta sha wani abun mai zaƙi.
Ya kalle ta a tausashe ya ce, "yawan hawan da sugar ki yake illa ne a wajan ki da abinda yake cikin ki, shi ciwon sugar ga mace mai ciki yana da matuƙar hatsari domin zai iya cutar da ita da abinda yake cikin ta. Wannan dalilin ya saka kika ga ina yi miki faɗa in kina shan abu mai zaƙi, bawai ina yin faɗan dan ki ji haushi bane ina yi saboda lafiyar ki. A shekarun ciwon sai yafi miki illa akan Mama, saboda ciwon yafi na tsatsanta ga wanda shekarun sa bai wuce naki ba Manal. Yawan high blood sugar da ake samu a kan ki ayanzu zai iya sakawa ki yi miscarriage, zai iya saka ki shan wahala a lokacin haihuwa fiye da tunanin ki, sannan zai iya sakawa sugar jikin abinda zaki haifa yayi yawa shima ƙarshe a haife shi da ciwon ko ya mutu."
Ganin ta nutsu tan jin sa ya saka yace, "Diabetes can also stop babies from glowing nomally Manal, zasu iya zama either too small or too large. Hakan sai ya jawo ki faɗa wani abu da ake kira da Stillbirth a turance, ma'ana yaron ya mutu a cikin ki after 20 weeks ko kuma during labour. Azo ace sai an yi cs za a cire babyn shima kuma in dai sugar ki ya yi high ba zai yu a yanka jikin ki ba, in an samu yadda ake so ma za a jima kafin ki warke."
Yadda ta bashi hankalin ta tana sauraren sa ya sake gyara zama yace, "let me give you example, kina da ciwon sugar sai sugar ki ya zama always is high, ga kuma baby a jikin ki wanda duk abinda kika ci shine zai dinga cycleting a jinin sa. Kin sha abu mai sugar sugar jinin ki yayi yawa sosai, ya kike gani in sugar ki yayi yawa a jinin ki bayan kuma shi jinin ki ne yake zagawa ko ina a jikin sa? Kina ganin zai rayu kasancewar sa fetus abinda bai zama mutum ba?."
Ta girgiza kai alamun a'a yace, "abinda nake guje miki kenan, na san ba yin kan ki bane amma you have to be very careful, it's a very dangerous a blood sugar ki ya dinga zama high. Shi fa ciwon nan yana hana mata ɗaukar ciki, suna shan wahala kafin ma su samu su ɗauki cikin wasu sai an basu magani suna sha wanda zai taimaka musu wajan samuwar cikin, in sun samu sai dokoki su biyo baya saboda lafiyar su da ta yaron. Ke kin samu Allah ya baki cikin ba tare da kina shan wani magani ba kuma zaki salwantar?."
"Na faɗa miki duk abinda kike so ki faɗa min ko tea din ne da madara ki faɗa min, akwai madara irin taki na siya na ajjiye miki amma bakya son sha. Akwai sugar irin naki na siya na ajjiye shima bakya sha, ba dole raina ya dinga ɓaci ba Manal? In wani abun ya same ki ya zanyi? Ke na fara samu kafin abinda yake cikin ki, rayuwar ki tafi min tasa mahimmanci, in na rasa shi zan iya samun wani, ke kuwa in na rasa ki na rasa kenan har abada."
Jikin ta yayi sanyi da jin kalaman sa na ƙarshe ta taso ta dawo kusa dashi ta shiga jikin sa ya rungume ta yace, "shine abinda nake guje miki Manal, ko babu ciki shan sugar zai iya jawo miki illa babba. Yan saka ciwon ido, rama, bugawar zuciya, ciwon koda da sauran su duka ciwon nan yana sakawa musamman ke fa kike da ƙarancin shekaru."
"Ka dinga yi mun addu'a Allah yasa na daina."
"In sha Allah zaki daina. Yanzu ma na san kin ci cake ɗin da naga kin yi ko?." Ta ɗago tace, "Wallahi ban ci ba ko kaɗan, na dai yi unsweetened ban saka sugar ba yana nan na ajjiye, shi kuma wannan meatpie ɗin babu sugar a ciki ko kaɗan."
"To meyasa baki faɗa min na saka an baki wheat flour a wajan Mummy ba? Ina ke ina normal flour itama ai ba abincin ku bace."
"To bazan sake ba." Yayi murmushi yace, "ko yaushe haka ki ke cewa baza ki sake ba, to naji."
"Ka yi haƙuri ka daina fushi dani."
"Na daina, shikenan?." Tayi murmushi shima yayi sai ta haɗe fuska cikin shagwaɓa tace, "ka tafi ka barni." Yadda tayi maganar sai da yaji ta a ko ina na jikin sa, Manal ta iya shagwaɓa ta riga da ta zamar mata jiki kowa ma yi masa take yi duk da tasa ta musamman ce.
Murya a ƙasa ya ce, "babu kuma abinda nayi ba, kawai saboda ki san kin yi laifi ya saka ni fita." Ta kalle shi tace, "kuma har harara ta kayi." Ya sake hararar ta yace, "yanzu ma na kuma."
"Allah ka daina sona, na faɗawa Mama ka daina sona sai faɗa take min wai ba tace na daina saka ta a maganar mu ba."
Yayi dariya mai sauti yace, "Manalin Mama, kice har kin bata labari?." Ta turo baki tace, "na faɗa mata, maimakon ta rarrashe ni ta dinga yi min faɗa." Ya dungure mata kai yace, "faɗan shine daidai dake ai."
"To duk ba laifin ka bane."
"To da nayi me?."
"Da kayi min ciki mana" ta faɗa tana kwantar kanta a ƙirjin sa.
Yayi dariya sosai mai sauti itama dariyar take yi yace, "Allah ko? To daɗin abin ba mutum ɗaya ne yake samar da cikin na dole akwai haɗin kan na biyu." Tana daga jikin sa tace, "ba wani haɗin kai, ta dole aka min." Dariya ta sake bashi sosai yana dariya yace, "haka kika ce? Shikenan zan kama kina hannuna yarinya."
Ta ɗago daga jikin sa ya sake kallon tayace, "ya maganar school ɗin ki ne? Ana ta karatu babu ke hakan daidai ne?."
"Allah ni na tsani makarantar gabaɗaya, dana shiga sai na fara jin amai yana tawo min."
"Ba kina attending online ba?."
"Kwana biyu na daina, amma zan dinga yi yanzu."
"Ai yafi in ba haka ba burin ki bazai cika ba. A asibitin mu ina ji ana ta yabon ki, ana cewa indai girki ka ke so mai kyaunda sauƙi kaje page ɗin cookwithManal."
"Da gaske ka ke?."
"Da gaske nake mana." Manal cikin farin ciki tace, "ka san ana ta bani advert, dan kwana biyu bani da lafiya ne amma da kaga sabon update. Yanzu ma abinda nayi ai nayi vedio."
yayi murmushi yace, "kice mai kuɗi ce a zaune a gabana." Tayi dariya shima yayi kafin yace, "Allah ya taimaka, Allah ya sa ki zama babba ki wuce inda ki ke tunani." Ta sake riƙe shi tana murna tace, "Na gode mijina, goyan bayan ka ne ya kawo ni wannan matakin."
"In kin gama wacce makaranta zaki tafi ki yi karatu?." Manal ta sauke numfashi tace, "aikin ku baya burge ni da nace zan zama nurse ko midwife, aikin lawyer baya burge ni da na zama, kai ni komai ba burge ni yake yi ba. Na fi ganewa na buɗe babban cafe ko bakery na dinga siyar da abinda na ƙware a kai."
Yayi murmushi yace, "ke dai kika sani." Kiran sallah akayi ya saka shi tashi ya fita itama tayi alwala tayi sallah ta cigaba da suyar ta.
Da ya dawo ya same ta a kitchen ta kalle shi tace, "Yauwa na gama, don Allah ka zuba min a cikin wannan packs ɗin kayi min packaging." Kallon sama da ƙasa ya yi mata yace, "ni ɗan aikin ki ne?."
"Allah nace ai." Ya shigo ciki kusa da ita ta nuna masa a inda zai zuba.
Kallon sa yaga tana yi ya ce, "Faɗi abinda yake ranki." Tayi dariya tace, "ni fa na ɗauka komai in ina so a gidan nan zaka dinga min, kamar girki da shara da komai in ina so zaka yi. Abinda ya saka na fara sarewa da kai lokacin ka ƙin cin abinci saboda nayi warming, na ɗauka zaka haƙura kaci saboda ni ɗin ni ce, na ɗauka zaka ci saboda kar raina ya ɓaci. Amma sai ka ƙi ci ka tashi ka barni da kayana ka kuma ce na dafa maka sabo."
Murmushi yayi ya kalle ta ya ce, "Da yake ga Mummy, dole naci saboda kar ran Mummy ya ɓaci."
"To duk ba cikin so bane?" Ta faɗa tana kallon sa. Banza yayi mata baice komai ba sai murmushi da yake yi tace, "yanzu fa ko buɗe min mota baka yi in zan shiga ko zan fito irin na masoyan nan, rabon ka da buɗe min mota tun farkon auren mu lokacin kana lallaɓa ni. Shiyasa akace in kina amarya kiyi abinda kike so da zarar aure ya fara nisa komai canjawa zai yi, lokacin nan har haƙuri ka ke bani fa, yanzu kam taɓɗijam."