Sashe 54
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Mustapha yace, "Alhamdulillah!.
Yanzu Rumana ba matar Adnan bace kamar yadda kowa yaji abinda yace, babu kuma aure a tsakanin su indai yana tare da Manal matsayin matar sa. Ke Rumana yanzu kina matsayin ƙanwar sa ne kuma Yayar matar sa, Allah ya baki matsayin har guda biyu a lokacin da baki tunanin samun sa ba, sai ki yi haƙuri ki ɗauki ƙaddara, Allah bai rubuta zaki zauna da shi matsayin mijin ki ba shiyasa tun farko baki aure shi ba ki ka auri wani daban. Sannan Allah ya taimake mu komai ya bayyana kafin a kai ga aikata haramci, ina nufin kafin ki kai ga tarewa da Adnan Allah ya bayyanar da ke ƴar uwar matar sa ce. Sai ki yi haƙuri Allah ya fito miki da miji na gari."
Falon yayi shiru sai kukan Ayan kaɗan-kaɗan Mama ta kalli Manal tace, "yaron nan yunwa yake ji, Mimi miƙa mata shi" ta faɗa tana bawa Mimi shi ita kuma ya bawa Manal. Idanun Manal a kulle suke Mubeena tace, "tashi mu fita waje sai ki bashi nan ana kallon ki." Tashi suka yi su biyu Mubeena tana riƙe da Ayan ta kuma riƙe hannun Manal suka fita daga falon.
Alhaji Mustapha ya ce "Shikenan ai komai ya ƙare ya kuma zo ƙarshe. Aure tsakanin Rumana da Adnan babu shi a yanzu babu shi, wancan da ya faru ya zama labari kamar ma bai faru ba, Manal itace matar sa har yanzu ba Rumana ba. Kowa ya san Rumana ƴar uwar sace a yanzu dan haka komai ya wuce ai ko?." Daddy ya girgiza kai yace, "komai ya wuce."
"To ma sha Allah. Sai wata nasiha da nake so nayi muku ku yara" ya faɗa yana kallon Huzaifa da da Adnan da Sultan da kuma yayyen Adnan yace, "Kar wani abu ya kai ku wani gari ko wata ƙasa ku yi aure ku bar matar a can ko da ciki ko babuciki, ku dawo garin ku ku manta ma kun yi wani aure, irin wannan abubuwan da suke faruwa ba sai kaga ba tare da sanin ka ba sai kaje wata ran kana soyayya da ƴar cikin ka baka sani ba. Hakan bashi da amfani kuma bashi da fa'ida ana kuma cutar da zuciya, yanzu kalli Rumana kowa yasan an raunata mata zuciya daman gata tana da ciwon zuciyar, ita kanta Manal ɗin an raunata ta Allah kaɗai yasan abinda take ji a zuciyar ta. Irin hakan bashi da wani amfani, in zamu yi aure a tsananta bincike ba iya halin yarinyar ba har halin iyayen ta sai kun sani, kai in da yuwa kakannin ta ma ya kamata ace kun san halayen su kafin auren yazo, ta haka za'a samar da zuri'ar da babu kwaɗo a cikin ta."
Yace, "yanzu da ace Huzaifa shine ya auri Manal ko shine ya auri Rumana don Allah wacce irin kunyar duniya za'a ji? Yaya da ya kasance uba ɗaya ya auri ƙanwar sa ta jini ba tare da ya sani ba?. Kuma iyayen su ne suka jawo suka raba kan yaran su wani yana nan wani yana can ba tare da an sani ba, babu riba ka auri mace ka barta da yara baka sake waiwaiyar ta ba babu ribar haka, wata ran zaka haɗu da ƴar ka ba tare da ka san ita bace, wataƙila kayi nata wata ɗabi'a mara kyau ko ita tayi maka, in ta bayyana ƴar ka ce itama ta san kai baban ta ne kazo kana jin kunya kuma duk kaine ka kawo hakan. In mata sama da ɗaya zaku yi ku yi amma ku tara su waje ɗaya, wannan ya san wannan, wannan ma yasan wannan. Yanzu a iyalan Alhaji Aliyu haka zasu tashi babu shaƙuwa a tsakani, Manal da Yayar ta kawai ta shaƙu saboda ita kaɗai ta sani matsayin ƴar uwar ta, sauran yaran suma da ƴan uwan su suka shaƙu dasu saboda su suka sani, haka Rumana yanzu itama gani zata yi kamar zata yi rayuwa a cikin wanda bata sani ba. Don Allah a dinga gyarawa, a dinga sanin abinda ya kamata ayi kar ana ana dana sani mara amfani."
Daddy y san maganar kaf dashi ake kuma haka ɗin ne sai girgiza kai yake yi kawai zuciyar sa tayi rauni sosai. Dagq nan dai taro ya tashi maza duk suka fita sai matan ya rage a falon.
Adnan ya kalli Huzaifa a harabar gidan su suna tattaunawa yace, "baka ganin irin kallon da Mummy take min? Wallahi gabaɗaya na tsoro ta." Huzaifa yace, "dole zata yi maka wannan kallon, amma zata warware in sha Allah, ina Manal ɗin?." Bebi ya kalli wajan yace, "nima ban ganta ba, da alama tabi Mubeena." Huzaifa yace, "sai kayi haƙuri" ya faɗa yana kallon sa ya girgiza masa kai kawai.
"Wayyo Allah! Yaya Adnan Rumana ta Suma! Ta suma kazo" Kausar ta faɗa da ɗaga murya tana yi masa magana, ya kalli Huzaifa da hanzari suka shiga inda suke.
Yadda suka barta a jingine akan kunar ashe ta riga ta suma a haka, Bebi ya ƙarasa inda take Mama tace, "Kar ka sake hannun ka ya taɓa fatar jikin ta, tunda baka ƙaunar ta kar na sake ganin ka a kusa da ita, kai kar na sake ganin ka daga yau ka fita ka bani waje!, kar na sake ganin ka a gidan nan!" Ta faɗa cikin ɗaga murya wacce ta firgita Adnan.
Kallon Mama yake yi hankalin sa a tashe sosai tace, "baza ka fita ba kenan?." Da sauri ya juya ya fito ya jinjina da mota cikin damuwa. Yana tsaye Huzaifa ya fito da Rumana a hannun sa kamar ƴar tsana aka aaka ta a mota aka wuce asibiti.
Shima motar ya hau ya tafi asibitin jikin sa a sanyaye sosai zuciyar sa na yi masa ƙuna sosai. Tunda ya tunkari inda suke yake jin kukan Mama ana ta bata haƙuri amma bata daina kuka ba, ya tsaya yana jin ɗaci a zuciyar sa jin kukan mahaifiyar sa kuma shine silar faruwar hakan. A lokacin Huzaifa yazo wajan ya riƙe Huzaifa yace, "me yake faruwa?." Huzaifa yace, "Dr Fulani yana kanta, amma condition ɗin ta is very bad Adnan, numfashi ta yana gab da barin jikin ta."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kukan Mummy nake jiyowa haka?." Huzaifa ya juya ya kalle su yace, "ba iya Mummy ba, dukkan su kuka suke yi." Adnan yace, "Huzaifa ya zanyi, abinda zan iya shi nayi amma Mummy baza ta fahimce ni ba, ina zan saka raina ne?."
Huzaifa yace, "a yanzu baza ta fahimce ka ba, amma zuwa nan gaba zata sakko fushi tayi kawai sai kayi haƙuri." Huzaifa ya wuce shi yana nan tsaye yana kallon yadda Maman sa take kuka ta dalilin sa.
Yana hango fitowar Dr Fulani ya fito duk suka yi kansa suna tambayar sa yanayin jikin ta, bayanin halin da take ciki yayi musu da nutsuwa yadda baza su firgita ba yazo zai wuce Bebi ya riƙe hannun sa yace, "ya jikin ta?." Dr Fulani ya kalle shi yace, "Gaskiya yanayin babu daɗi, komai zai iya faruwa. Numfashin ta yayi ƙasa da sixty percent. So lamarin sai addu'a kawai." Bebi ya sauke ajiyar zuciya ya dafe kansa, Dr Fulani ya wuce shi kuma ya ƙarasa ya shiga office ya zauna ya dafe kansa da duka hannayen sa kamar zai yi kuka.
Bai san adadin lokacin da ya ɗauka a haka ba kafin ya tashi ya fito zuwa inda suke yana kallon Mama har lokacin kuka take yi. Ɗago kai tayi ta kalle shi kawai tana miƙewa ta wanke fuskar sa da mari mai zafi dan a fusace take dashi. Bata san ma hannun ta ya sauka a kan fuskar sa ba, kawai ji tayi ta mare shi cikim rashin sani saboda ɓacin ran da yake taso mata daga zuciyar ta.
"Ka bani kunya, a yau na tabbatar da baza ka iya bani farin ciki ba tunda ka kasa yi min abinda nake so. Me kazo yi nan?, Kazo ta gan ka ta kuma shiga wani yanayin?, Kazo ta ganka ka sake jajjada nata baka son ta Adnan!" Ta faɗa cikin murya mai amo.
Tunda mare shi fuskar sa na gefe yana ɗaya yana kallon tiles ɗin ƙasa yana sauke numfashi zuciyar sa na yi masa zafi. Umma ce ta da tsaye ta riƙe ta tace, "Haba Hauwa meye haka? A asibiti muke kuma shi laifin me yayi miki har zaki mare shi?."
"Shine ya jawo komai, shine ya kawo komai Yaya. Da yayi abinda nace da yanzu haka bata faru ba, da ya aure ta tun farko da hakan bata kasance, yanzu tana kwance ba'a san a yanayin da take ciki ba, zata rayu ko baza ta rayu ba babu wanda ya sani, yadda likitocin suke fitowa zai tabbatar maka da halin da take ciki yayi muni. Wallahi in Rumana ta mutu bazan yafe masa ba."
Suman tsaye Adnan yayi jin abinda Mama tace, bashi da bakin yin magana a wajan yayi saurin barin wajan kar ya jawo tayi wata maganar da zata saka shi a kwantar dashi shima a asibitin. Office ya koma ya rasa abinda yake masa daɗi, hankalin sa ya kai ƙarshe wajan tashi damuwa tayi masa yawa har ya fara sana sanin zaɓar Manal da yayi a matsayin matar sa ya bar Rumana, ji yake ina ma bai sake ta ya cigaba da zama da Rumana ɗin kodan hankalin Mama ya kwanta. Bai san yana hawaye ba sai jin ɗumin su yayi a kuncin sa, yayi sauri ya goge yana kallon waje ɗaya cikin tsananin damuwa.