Sashe 56
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Huzaifa kawai ta gani a akan kujera da ta dawo ya kalle ta sosai bayan ta zauna yace, "Manal lafiya dai?, na san ba lafiya bace zata saka ki fito daga gida har ki kwana a nan ba, me ya faru?." Manal ta sauke numfashi ta kalli gefe yana kallon fuskar ta a nan yaga shatun hannun Adnan a gefen fuskar ta, abin ka da fara gefen fuskar har kumbura yayi ja kana gani ka san marin ta aka yi. Sosa kunne tayi tace, "kunne na ne yake ɗan yi min ciwo." Shiru yayi bai ce komai ba dan shatin marin da ya gani a kuncin ta zai iya saka ta ciwon kunne.
Hawaye ta fara yi tana gogewa, ya kalle ta a nutse yace, "Manal ba kuka nace ki yi ba, ce miki nayi lafiya kika fito a daren jiya ba tare da Adnan ba?." Manal murya na rawa tace, "ni na bar auren sa Yaya." Da mamaki Huzaifa yace, "kamar ya kin bar auren sa?." Manal tace, "bazan koma ba, na gama auren sa." Yayi murmushi jin abinda tace dan ya fahimci faɗa suka yi yace, "A'a ki daina faɗar hakan."
"Yaya meyasa ya ɓoye min batun Rumana tun kafin ya aure ni?, Meyasa bai faɗa min lokaci yake jira zai kawo ta gidan ba?. Ai ya kamata tun kafin ya aure ni na san da maganar amma bai taɓa yi min maganar ba ko da wasa."
Huzaifa ya girgiza kai yace, "kar kice min a kan wannan maganar kika bar gidan ki Manal?." Ta kawar da kai gefe tana turo baki tana goge idon ta bata ce komai ba. Huzaifa yace, "wannan ai ƙaramar matsala ce tunda yanzu babu wannan maganar bai kamata ace ta ɓata miki rai har kizo gida ba, yanzu ai babu aure a tsakanin su ko?." Manal tace, "amma da hakan bai faru ba fa?, da sai dai naga an kawo ta ance itama matar da ce ba tare da ya faɗa min ba?. Meyasa zai ɓoye min tun farko?."
Huzaifa yace, "eh bai kyauta ba. Tun farko yana da kyau ki san da maganar. amma bai kamata ace wannan maganar ta kai ga kin baro gida ba, a tsakanin ku ya kamata ku tattauna komai zai wuce. Kin san halin mijin ki kema ya san naki, in ku ka nutsu ku ka yi magana shikenan."
Manal tace, "ni bazan koma ba, da nace zan tafi cewa yayi in naga sama kar na dawo, kuma ai cewa yayi in ba dan Ayan da na haifa ba babu abinda zai saka shi ya zaɓi zama dani akan ta. Dan haka ni a na zan zauna." Yayi dariya yana girgiza kai ya san halin Bebi matuƙa tsaf zai aikata abinda tace. Manal tace, "don Allah ka barni na zauna a nan, kuma don Allah kar ka faɗa masa koda zai tambaye ka kace baka san inda nake ba. Inda ya damu dani zai neme ni amma ko waya bai yi min ba har yanzu" ta faɗa hawaye yana sake sakko mata.
Huzaifa yace, "kina da ikon zama a nan Manal kar ki damu, kuma bazan faɗa masa ba. Amma kin san jiya yana cikin ruɗani ne shiyasa hakan ya faru, da kin sani baki yi masa maganar a jiya ba, sai ki bari sai an kwana biyu sai ki masa maganar sai ya baki haƙuri a wuce wajan, kin fini sanin halin mijin ki."
Manal ta kalle shi tace, "Shine zai bani haƙuri?."Huzaifa ya murmusa yace, "zai baki mana ai laifi kike ganin yayi miki." Manal tace, "hmmm! Shi ya sani dai, ni dai kayi min alƙawari baza ka faɗa masa ba."
Yayi murmushi yayi yace, "bazan faɗa masa ba sai ya neme ki." Manal ta taɓe baki tace, "ko ya neme ni bazan koma ba" ta faɗa tana buɗe ledar da aka kawo mata, yaga kayan Ayan ne ta ciki da tayi order aka kawo mata wato baza ta koma ba ɗin ba. Ya girgiza kai yace, "ki je kici abinci."
"Zan ci, zan ma je makaranta
"Allah ya kiyaye" ya faɗa yana tashi ya shiga ciki.
Bebi gabaɗaya ya shiga damuwa tafiyar Manal ta dame shi sosai a haka ya kwana bai kira ta ba sai da safw ya kira number amma user busy. A haka ya shirya ya fita daga gidan ya wuce asibiti wajan Rumana.
Da yaje Mama bata nan sai Ammi kawai hakan ya bashi damar shiga cikin ɗakin yaga halin da take ciki, har lokaci bugun zuciyar ta da numfashin ta bai yi daidai ba amma an samu cigaba. Bebi ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Rumana da take kwance ya kulle ido ya buɗe zuciyar sa na bugawa sosai cikin rashin jin daɗi.
Jiki a sanyaye ya fito suka haɗu da Ammi da take zaune a waje ya kalle ta yace, "Ammi ina kwana?." Da fara'a tace, "Bebi ashe ka shigo, Lafiya lau ya gida?."
"Lafiya lau Ammi, ya mai jiki?."
"Jiki da sauƙi."
"Allah ya ƙara lariya." Ta amsa da amin tace, "Ina Ayan, yana lafiya?." Girgiza kai kawai yayi alamun lafiya lau.
Mama ce tazo wajan ta ƙaraso ta zauna ya kalle ta bayan ya tsuguna yace, "Mummy ina kwana." Banzan kallon da tayi masa ne ya saka shi sunkuyar da kai gaban sa ya faɗi sosai tayi tsaki tace, "Dallah malam wuce ka bawa mutane waja, kar na sake ganin ka wajan Rumana ka barta ta mutu tunda baka ƙaunar ta." Ya buɗe baki zai yi magana cikin tsawa tace, "nace ka wuce ka bani waje, kar ka ce min komai ka tashi ka bani waje kawai." Jiki a sanyaye ya miƙe tsaye ya fita zuwa office ya zauna ya dafe kansa gabaɗaya zuciyar sa a raunane take.
Hamza ne ya shigo office ɗin nasa kafin ya gama shigowa Huzaifa yazo wajan suka ƙaraso ciki suka mipa masa hannu duk suka gaisa Huzaifa yace, "naga yanayin jikin nata ba kamar jiya ba." Ya ɗaga kai kawai baice komai ba.
Hamza yace, "Allah ya ƙara lafiya, ni bara na koma bakın aiki" ya faɗa tana fita. Huzaifa ya kalle shi yace, "ka daure wannan raunin ya daina bayyana a fuskar ka, rauni baya dacewa sa kai Bebi." Ajiyar zuciya yayi kawai baice komai ba. Ganin baya son magana sai ya tashi ya fita ya bashi waje kawai.
Kwanan Rumana uku asibiti ta samu lafiya ba laifi dan ta farfaɗo har magana tana yi. Bebi gabaɗaya ya rasa yadda zai yi, Manal wayar ta bata shiga duk a tunanin sa tana gidan Mama shiyasa hankalin sa yake a kwance bai wani tashi hankalin sa yqna neman ta ba, yana so yaje gidan nasu amma so yake ya daidai ta da Mama sannan ya neme ta hankalin sai zai fi nutsuwa.
A kwana na ƙarfe sha biyu na rana su Mama suka fito daga asibitin da Rumana da aka sallame ta. Bebi ganin su sai yazo wajan ya buɗe motar sa yace, "Don Allah Mummy ku shiga." Ammi ce ta ja hannun Rumana suka shiga tana riƙe da hannun ta ganin hakan Mummy ma ta shiga suka tafi.
BDƘB3P34
Gidan Hajiya tace su je suna shiga gidan Hajiya suka tarar da Yaya Mustapha da kuma mai bin da Yaya Sulaiman a wajan Hajiyan. Suna shiga Rumana ta zauna a kan kujera tana jan numfashi gabaɗaya ta canja lokaci guda.
Hajiya tace, "sannu Rumana, ya jikin naki?." Ɗakyar tace, "da sauƙi Hajiya, na sannu lafiya."
"Allah ya ƙata lafiya, sannu kin ji komai na duniya haƙuri ake yi." Ta ɗaga kai kawai bata ce komai ba.
Hajiya ta kalli Bebi da yake zaune kai a ƙasa ta kalli Mummy tace, "Hauwa duk bawa baya tsallake ƙaddarar da, Allah bai rubuta Rumana zata zama matar Adnan ba tun farko, shiyasa ki ka ga an samu saɓabi tun suna soyayya bai aure ta ba saboda ba matar da bace, ina so ki tuna wani baya auren matar wani, matar mutum ta kasance kabarin sa kamar yadda hauaawa suke faɗa, kamar yadda wani baya shiga kabarin wani haka babu wanda zai auri matar da ba tasa ba. A zanen ƙadarar Adnan babu Rumana a ciki, Fatima itace matar da Allah ya rubuta zai aure ba ita ba, fushi da kike dashi kamar kina fushi da hukuncin Allah ne, domin kuwa ba shi ne ya ƙaddara hakan ba Allah ne, Allah ne ya rubuta hakan shi kan sa bai isa yayi abinda Allah bai nufa ba."
Mama tace, "ba fushi nake dashi ba Hajiya, kawai ina jin haushin yadda ya iya barin Rumana duk da yanayin ciwon da ta samu saboda shi, Hajiya ciwon zuciya ne da ita fa, amma bai tausaya mata ya zaɓe ta matsayin mata ba." Hajiya tace, "yanzu in ya zaɓi Rumana ya bar Fatima an yi mata adalci kenan ita? Matar da ce fa wacce suka zauna tsahon watanni ina tunanin watan gobe zasu shekara da aure, ga ɗan da suka haifa shi da ita. Kuma yarinyar nan bata san maganar Rumana ba tun farko, kenan ita dan ba ƴar ki bace in ya sake ta ya zaɓi ƴar ki yayi mata adalci kenan? Daga shekara ɗaya da yin auren sa da ita ace ya rabu da ita saboda cikar burin ki?, hakan daidai ne Hauwa?."
Mama ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru bata ce komai ba,Hajiya ta kuma cewa, "Allah bai rubuta zai auri Rumana ba, kuma gwara da Allah ya bayyana matar sa da Rumana uban su ɗaya, da yanzu sai bayan ta tare a zo ana da an sani ana jin kunya. Yaron nan yayi miki biyayya duk da baya son auren ta ya amince zai yi saboda ke, bayan ita lokacin da nuna bata so ba'a tilasta mata ba an barta tayi abinda take so. Shi kuma ya amince zai aure ta sai kuma Allah ya bayyanar da wannan maganar amma kin kasa karɓar ƙaddara kina ganin kamar shine ya cutar da Rumana."