Sashe 19
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru yaji tayi bata ce komai ba yace, "Milky."
"Uhum."
"Talk please, me ki ke so Adnan ya baki?."
"Nidai uhum uhum."
"You can say it, please ki faɗa" ya faɗa yana ɗauko ta jikin sa ya fara bin wuyan ta da hancin sa. Tayi shiru idanun ta a kulle ya kalli fuskar ta yace, "shikenan tunda babu abinda ki ke so mu yi baccin mu."
Manal ta buɗe idanun ta suka haɗa ido zai yi magana ta hana shi maganar ta hanyar kulle masa baki, ya wara ido yana kallon ta tayi saurin kulle idon ta dan kar ma ya saka ta kasa abinda tayi niyar yi.
BDƘB3P11
Washe gari ta riga shi tashi da safe saboda yunwar da ta fara damun ta, ta tashi ta fito daga ɗakin ta fita zuwa Babban falon gidan ta tarar dashi tass ba kamar lokacin da suka shigo ba. Ta wuce zuwa ɗakin ta tayi wanka sharp-sharp saboda yunwa, bayan ta fito ta buɗekayan ta ta saka doguwar riga ɗinkin fitted gown, ta aaka hijjabi tayi sallar walha kamar yadda ta saba bayan ta idar ta ɗaura ɗankwali ta fito zuwa kitchen.
A tsaye ta tarar da mai aikin ta tana aikin goge kitchen ɗin duk yayi ƙura, gaisawa suka yi da Manal kafin tace, "Anty kwana biyu bakya na, kin dawo lafiya."
"Lafiya lau Lubabatu, ya akayi kika san na dawo?."
"Ant Khadija ce ta faɗa min kin dawo." Manal tayi murmushi mai aikin tace, "na gama zan koma, akwai abinda kike so?." Manal tace, "babu komai, in akwai zan kira ki." Ta amsa da to ta fita Manal tana kallon kitchen ɗn tana tunanin abinda zata ci don yunwa take ji sosai.
Kittle ta kunna ta dafa ruwan zafi hannun ta har rawa yake yi ta haɗa tea da yaji uwar madara harda milo ta saka sugar, da sauri-sauri take yi saboda kar ya fito ya ganta. Duk zafin sa haka ta zuba a bakin ta ai kam bata iya haɗɗiyewa ba ta dawo dashi saboda zafin sa, ta sake sha a lokacin ta haɗɗiye harda lumshe ido saboda daɗi.
Karɓar kofin taji anyi daga baya ta juyo suka haɗa ido gaban ta ya faɗi saboda kana gani yadda fuskar sa take ka san ta ɓata masa rai. wajan sink ya ƙarasa ya zubar da tea ɗin ya kuna fanfo ruwa ya tafi dashi ya ajjiye kofin baice mata komai ba ya wuce ya fita.
Manal kamar zata yi kuka tace, "to ni ya zanyi? In ba sha ba bana jin daɗi wallahi" ta faɗa hawaye na sakko mata ta rasa ma abinda zata yi. Tana sharar hawaye tana ƙoƙarin haɗa breakfast amma yunwar da take ji baza ta bata damar hakan ba. Fridge ta buɗe taga babu komai sai yourgut guda ɗaya har ya zana ƙankƙara saboda sanyi, ta ɗauko ta duba jikin sa ganin unsweeted ne sai ta saka shi a ruwan sanyi dan ya narke ta sha.
Rasa abinda zata yi tayi kawai ta fara kuka wiwi kamar wacce aka daka. Yana jiyo ta yana falo kawai bazai tashi bane dan ta ɓata masa rai ya kuma lura bata jin magana ko kaɗan. Tashi yayi ya fita ba jimawa ya dawo da leda a hannun sa ya ƙarasa wajan dining ya ɗauko plates a inda suke, abinda yake ciki ya juye a ciki ya nufi kitchen ɗin dan kukan nata ya ishe shi.
"Dukan ki nayi kike min kuka?." Jin muryar sa a kausashe ya saka ta kalle shi ta ga fuskar a ɗaure matuƙa jikin ta har rawa yake saboda yunwar take ji.
"Kawai dan shagwaɓa zaki fara yi min kuka dukan ki nayi ko wani abun aka yi miki?" Ya faɗa cikin faɗa yana kallon ta. Maimakon kukan ya tsaya sai hawaye ya sake sakowa yayi tsaki tace, "in baki daina kuka ba in nazo nan sai na miki abinda zaki kukan da hujja, Malama ki fito ki ci abinci in zaki iya."
Ai da sauri ta ƙarasa inda yake ta raɓa ta gefen ta wuce, tana zuwa tsakiyar falon taga abincin ta zauna tana cin dankali da kwai kamar Allah ya aiko ta. Tana ci tana kuka saboda yunwa take ji ga faɗan da yake mata bata so.
Kusan rabi ta ci ta sha ruwa tana sauke numfashi cikin jin daɗi har lumshe ido take yi, shi dai yana tsaye yana kallon ta ikon Allah, ta bashi tausayi sosai gabaɗaya cikin ya canja ta ta koma mai rigima ga yawan kuka sannan ga jin yunwa kamar wacce bata cin abinci. amma ta ɓata masa rai sosai tausayin ta bazai hana ya nuna mata kuskuren ta ba. Yana tsaye ta taso a guje zuwa sink ɗin wajan dining tana amai duk abinda taci a lokacin sai da ya dawo.
Ruwa ya miƙa mata ta bayan ta, ta karɓa ta sha ruwan yace, "sannu." Ta ɗaga kai yace, "meyasa baki ce min bakya son ci ba?."
"Dan ban sha tea bane shiyasa nayi amai."
"Okay, zauna na kawo miki" ya faɗa yana zaunar da ita akan kujerar dining ta zauna ya shiga kitchen. Ba jimawa ya kawo mata tea ya ajjiye a gaban ta ya sake dauƙo wanda ta rage ya zauna a gefen ta yace, "Gashi nan ki sha sai kici."
Kallon fuskar sa tayi suka haɗa ido taga fuskar a ɗaure babu damar da zata yi masa magana,ta sunkuyar da kai ta fara shan tea ɗin gabaɗaya baya yi mata daɗi in ba mai sugar ta sha bata jin daɗi. Sai da ta sha rabi sannan ta sake cin dankalin tana yi tana kallon sa. Yana ganin ta sai ya cigaba da danna wayar sa kamar bai san wata wajan ba. Tana daga inda take yaji tace, "baza ka ci ba?." Kai ya girgiza mata kawai baice komai ba ta cigaba da ci kafin ta ture alamun ta ƙoshi.
"Kayi haƙuri, ba da son raina nake shan tea mai sugar ba wallahi." Tsaki yayi yace, "ke kuma kika sani" ya faɗa yana tashi ya bar mata wajan ta sauke ajiyar zuciya ta rasa abinda yake damun ta gabaɗaya.
Tana zaune ya fito ya shirya da alamun fita zai yi ya kalle ta yace, "zan je aiki na dawo, zuwa yamma zamu je mu gaida Hajiya da Mummy." Ido ta ya ciko da hawaye tace, "amma kace min baza ka fita ba."
"Fitar ce ta same ni dole sai naje. Kinga tunda bana nan ki sha abinda kike so kin ji, duk abinda kika ga kina so Manal ki sha son ranki" ya faɗa yana hararar ta ya ɗauki wayar sa ya fita ya barta a zaune.
Kukan ta ta cigaba da yi sai da ta gaji ta tashi ko kayan bata ɗauke ba ta shiga ɗaki ta kwanta ta jawo waya kawai ta kira Mama. Mama na ɗauka ta sake ƙara ƙarfin kukan ta ba tare da tayi sallama ba, daga can ɓangaren Mama tace, "ke wai yaushe zaki hankali ne? Ba sallama ba komai sai kuka?." Murya na rawa tace, "ina kwana."
"Lafiya lau."
"Mama partner ya daina sona, yayi tayi min faɗa akan abinda ba laifina ba ne." Mama tayi tsaki tace, "Ke wai ban faɗa miki ki daina saka ni a cikin maganar dake tsakanin ku bane?."
"To Mama ya zanyi? Ke nake iya faɗawa abinda yake raina. Mama laifina ne dan ina sha tea da sugar?, Mama ji nake yi in ban sha ba kamar zan yi hauka, kamar na dinga dukan kaina haka nake ji, a gida ma dan bani da lafiya ne kuma ina ɓuya Ina sha baku sani ba. Shine fa dan yaga ina sha da safe yake ta yi min faɗa ya kuma yi fitar sa bayan yace min bazai fita ba, kuma ko kira na bai yi ba har yanzu."
Mama tace, "yayi daidai ai, tunda ke bakya jin magana baki san illar ciwon da kike dashi ba, gwara da ya fita ɗin Allah ya sa bazai dawo ba sai dare."
"Mama ina so na daina, kuma ba laifina bane."
"Kar ma ki daina kin ji, sannan kar ki sake kirana ki faɗa min wani abu da yake tsakanin ki da mijin ki, gargaɗi na ƙarshe kenan. In zaki gyara ki gyara da kan ki in baza ki gyara ba ke kika sani" Mama na faɗa ta kashe wayar Manal ta sake fashewa da kuka mai sauti.
Bebi kuwa yana sane ya fita ya barta babu abinda zai yi a asibitin, kawai dan ta ɓata masa rai ne bata san hatsarin da yake tattare da ɗaukar ciki ga mai ciwo irin ta bane shiyasa take abinda take so. Asibitin yaje bai jima sosai ba ba ya fita ya shiga restaurant ɗinsu a can ya sosai suna hira da Usman kafin ya ɗauko hanyar dawowa gida.
Da ya shiga falon bata nan an gyara shi dai yayi kyau ya wuce ɗaki ya ajjiye abinda ya taho dashi ya fito ya shiga ɗakin ta amma bata ciki. Motsin ta ya jiyo a kitchen ya shiga ya ganta a tsaye tana ta aiki kamar ba ita ba. Ƙarasowa yayi inda take tsaye yace, "aikin me kike yi?."
Kallon sa tayi maimakon ta bashi amsar tambayar tace, "emergency ɗin kenan?." Banza ya yi mata kamar bai ji abinda tace ba ganin haka sai tace, "Mummy nake yiwa da Hajiya tunda kace zamu je, kaga ban taɓa kai musu komai ba."
Bai ce komai ba ya juya ya fita ta kashe gas ɗin ta biyo bayan sa da meatpie a hannun ta tana ci, ta zauna a nesa dashi ta ajjiye meatpie ɗin a kan table tace, "Bana sane nake shan tea da sugar wallahi, ɗazu ma ji nayi in ban sha ba zan iya mutuwa shiyasa ka ga ina sha. Ka tambayi Yaya Huzaifa a da sugar na baya high saboda bana cin duk abinda aka hana ni ci.tunda na samu cikin nan shikenan nake shan wahala, in na sha tashin hankali in ban sha ba tashin hankali, shiyasa nace maka ni bana son cikin nan amma ka kasa ganewa" ta faɗa tana kuka shi dai kallon ta yake, kuka gabaɗaya baya yi mata wahala ko gajiya bata yi.