← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 84

Sashe 53

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kowa yayi mamaki abinda tace saboda kowa yasan irin son da suke yiwa junan su. Adnan yaji babu daɗi soaai dan yana son ta kowa ya shaida amma lokaci ɗaya ta bar shi, tana yin aure ya sake komawa karatu inda ya juya ɓangaren karanta zuciya. Auren Rumana bai wuce shekara ɗaya ba auren ya mutu ta dawo ta cigaba da karatu a lokacin Adnan ya dawo. Rumana taso alaƙar su ta cigaba daga inda ta tsaya a wannan lokacin, Amma Adnan ya nuna shi baya da buƙatae ta a rayuwar sa a fannin soyayya, yana kula ta matsayin ƙanwar sa ne amma ba da sunan soyayya ba, a haka aka cigaba da zama har kawo yau.”

Mama ta kalle su tace, “Da farko ban bashi goyan bayan auren Manal ba, saboda ni Rumana kawai nake da burin ya aura ya sani kuma yayi min alaƙawarin auren ta. Sai da yaje ya haɗa ni da mahaifiyata akan Rumana sannan tace babu ruwan na ƙyale shi ya auri wacce yake so kamar yadda aka bar Rumana ta auri wanda take so a farko. Na amince da auren sa na farko amma na saka masa sharaɗin da yayi min alƙawarin cikawa ko bani da rai.”

“Na faɗa masa dole zai auri Rumana bayan shekara ɗaya da auren sa da Manal, yaso ya turje ya nuna ƙin amincewar sa amma na tabbatar masa da haka za’a yi ko bani da rai, ya amince da hakan ya kuma yi min alƙawarin auren ta ko ina da rai ko bani da rai. Shirye-shirye bikin sa da aka fara sai ya jefa Rumana a damuwa mai yawa, har abin ya kai ya kawo da Rumana ta kamu da ciwon zuciya saboda soyayyar da take yiwa Adnan. Son da ta yiwa Adnan a baya ba komai bane akan wanda ta ke yi masa yanzu, hakan ya saka hankalin ta ya tashi har ya kai ta ga ciwo. Daga nan Adnan ya fara rarrashin ta yana bata baki amma duk da haka ciwon baya yin baya sai gaba. Ranar da aka ɗaura auren Adnan matar sa ta tare ranar a asibiti Rumana ta kwana babu numfashi.”

Mama ta sauke numfashi tace, “bayan ta samu lafiya hankalina ya tashi, ganin yadda na damu akan lamarin ciwon Rumana Adnan ya sake jadadda min alƙawarin da yayi min akan auren Rumana, ni kuma wannan damuwar da rashin lafiyar nan nata sai ya dame ni, saboda babar ta haihuwar ta tayi kawai amma ni ce uwar ta. Naje na samu mahaifin Adanan ina kuka da kuma Yayana na sanar dasu halin da Rumana take ciki, suka tambaye ni me nake so ayi nace kawai ina so a ɗaura auren Rumana da Adnan a washe garin ranar.”

Gaban Adnan ya faɗi ya kalli Mummy a lokacin itama shi take kallo tace, “da farko Yayana yaƙi amincewa da auren, amma na dinga yi masa magiya har ya amince. Washe gari bayan sallar azahar mutanen da suke cikin masallacin da Abban sa da kuma Yayana suka ɗaura auren Adnan da Rumana. Aka kawo min rogo da alewa da sadakin ta farin cikina ya kasa ɓoyuwa na sanar da Rumana abinda ya faru, na tabbatar mata da ita matar Adnan ce a wannan lokacin wallahi a ranar ta wartsake.”

“Bayan ni da Ita da Abban su da kika Yaya babu wanda ya sam maganar ko mahaifiyar ta. Ni nace mata ta koma Abuja gidan Yaya ta cigaba da zama da zarar Manal ta shekara ɗaya zata dawo, a lokacin kowa zai san da maganar auren su sai ta tare a gidan ta. Haihuwar Manal ce ta dawo da ita suka zo garin nan da matar Yaya, lokacin da muka je gidan Adnan a ranar a asibiti Rumana, sai ta kwana biyu a can sannan ta tashi. Na sake maimaitawa Adnan magana akan auren ta yace yana sane ya kuma san yayi min alƙawari tunda shi bai san an ɗaura musu auren ba.”

Mama ta kalle su dukkan su tace, “na baku wannan labari ne saboda kowa ya sani, ga shaidun ɗaurin auren Rumana da Adnan nan a zaune. Dalilina na bada wannan labari shine; yanzu Manal da Rumana mahaifin su ɗaya, kuma addini ya haramta namiji ya auri ƴan gida ɗaya. Dole sai dai Adnan ya ɗauki ɗaya ya bar ɗaya a cikin su. A yanzu Manal da Rumana mun shaida mahafin su ɗaya, kuma mijin su guda ɗaya ne, dole sai dai ɗaya ta haƙura ta barwa ɗaya, ina so ku tuna da wannan” ta faɗa tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta tashin hankali ya bayyana a ƙarara a tare dashi.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Tabbas haka ne Hauwa, Tabbas anyi haka ni shaida ne mahaifin sa ma shaida ne. Mun yi abu ba tare da mun san hakan zata kasance ba” Yayan Mama ya faɗa yana kallon ta.

Abba yace, “ƙwarai anyi haka, yanzu kenan Rumana ma matar Adnan ce kamar yadda muka san Manal matar sa ce” ya kalli Adnan yace, “yanzu dole ɗaya zaka ɗauka ka bar ɗaya haka addini yace, in Manal ka ɗauka zaka saki Rumana, ina in Rumana ka ɗauka zaka saki Manal.”

BDƘB3P32

Bebi gaban sa faɗuwa yake yi sosai, ya runtse ido ya buɗe ya kalli Mummy da take kallon sa ya ɗauke kai daga kallon ta, ya kalli Rumana yaga ta kulle idanun ta ƙirjin ta yana up and down, ya kalli Manal yaga ta kifa kanta a kafaɗar Mubeena ko ba a faɗa masa ba yasam kuka take yi. Ya kalli Huzaifa da yake kallon sa shima kawai ya sunkuyar da kai saboda bai abinda zai yi ba.

Abba tace, "Adnan ƴan uwa ne su biyun, dole ka gaggauta ɗaukar hukunci ran mu duka ba hannun mu yake ba. Babu kara ko tunanin wani abun ka ɗauki abinda ka ke ganin zaka iya, ka ajjiye wanda baza ka iya ba."

Bebi ya kalli Alhaji Mustapha kamar zai yi kuka, ya buɗe baki zao yi magana ya kasa ya sake mayar da kansa ƙasa gabaɗaua ya shiga ruɗani, wa zai ɗauka wa zai bari a cikin su?.

Shiru wajan ya saka yi babu mai magana a cikin su kowa da abinda yake damun sa a zuciyar sa, Alhaji Mustapha ya sake cewa, "Adnan wannan ba magana bace ta wasa, yana da kyau ka gaggauta furta wacce zaka zauna da ita a ka kuma sauke nauyin auren ka da yake kan ɗayar, wannan ba abinda za'a baka lokaci bane, kayi ka furta kawai a wuce wajaan." Bebi ya sauke numfashi ya kalli Mummy yaga shi take kallo ya sake runtse idon sa, sai a lokacin yake ji ina ma babu alaƙar jinji a tsakanin Manal da Rumana, ina ma babu alaƙa ta jini a tsakanin su da ya cigaba da zama dasu matsayin mata sa, yanzu ya shiga wani hali wanda bai san ya zai yi ba.

Ɗago kai yayi yana salati a zuciyar sa ya sake kallon Rumana ya ganta yadda numfashin ta yake yi, ya san tana da ciwo komai zai iya faruwa da ita, ya kalli Manal itama tana jikin Mubeena tana kuka, suka haɗq ido da Mubeena yaga itama kallon sa take yi tana so taji me zai ce. "Hasbunallah!" Ya furta a snayeye yana sauke kansa ƙasa.

Kowa yayi shiru shi ake saurare ya ɗago ya kalli Alhaji Mustapha yace, "Daddy ni..." sai ya kasa magana yayi shiru ya dafe kansa. Alhaji Mustapha yace, "ina jin ka, faɗi abinda yake zuciyar ka kar kaji tsoro, kowa ya san ƙaddara babu wanda zai tsallake ta, in ba dan haka ba da dukkan su zaka zauna dasu ne matsayin matan ka. Amma yanzu bazai yu ba saboda kasancewar su ya da ƙanwa dole ka bar ɗaya ka ɗauki ɗaya."

Bebi ya sake ɗagowa ya kalli Huzaifa yayi masa alamun ya nutsu ya ɗauke kai ya kalle su, ya kulle ido ya buɗe kafin yace, "Daddy ni ban san da an ɗaura aurena da Ruman ba, ban san akwai aurena a kanta ba. Sannan kuma Manal..." sai ya kasa ƙarasawa ganin irin kallon da Mama take masa dole yayi shiru.

Alhaji Mustapha yace, "eh mun san baka sani ba, daman ba ayi niyar faɗa ba sai matar ka ta shekara a gidan ka, an yi hakan ne saboda yanayin ciwon da ita Rumana Allah ya ɗora mata ba dan wani abun ba. Amma yanzu kana da ikon zaɓar wacce zaka zauna da ita, Bawai dan bamu san wa kake so a cikin su ba, sai dan haka addini yace ayi. Dan haka ka zaɓi abinda yake ranka ko ne ya faru haka Allah ya rubuta, duk wacce ka zaɓa dole ɗayar ta ɗauki ƙaddara."

Kukan da Ayan ya fara ne ya saka shi ya juya ya kalle shi a hannun Mubeena tana ɗago Manal dan ta ta karɓw shi amma taƙi ko motsawa shi kuma kukan nasa ƙara gaba yake yi. Maman Adnan ce tace, "Bani shi Mubeena." Mubeena ta janye Manal a jikin ta ta bawa Mama shi ta saka shi a kafaɗa tana jijjiga shi sai kuwa kukan ya ragu.

Dawo da kallon sa yayi ga Mama ya sauke ajiyar zuciya ya kulle ido ya buɗe ya daure ya fizgo maganar yace, "na yanke hukuncin zan zauna da...." Kallon Mama yayi yaga ta ɗauje kai daga kallon sa ya kalli Alhaji Mustapha ya sake yin shiru. Alhaji Mustapha yace, "Adnan da Manal uwar ɗan ka zaka cigaba da zama?." Kamar nai ciwon wuya ya ɗaga kai alamun eh, Alhaji Mustapha yace, "to ka warware auren Rumana da yake kan ka."

Ya kulle ido ya sake yin ƙasa da kansa yace, "Na sake ta" ya faɗa murya na rawa soaai. Alhaji Mustapha yace, "ka saki wa?."
"Ruman!" Ya furta yana rufe idanun sa ya buɗe akan Rumana da ta rintse idon ta tana sauke numfashi a hankali.
Chapter 53 · 0% Book details