Sashe 48
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“A cikin dukiyar da na gada a wajan Baba akwai abinda ya rage guda biyu wanda ban rasa ba, na farko takardar gona ce a Jalingo, sai takardar gida shima a Jalingo. Na bashi wannan takardun yaje har Jalingo ya gano wajan ya tabbatar suna nan gonar aka bada ita haya, gidan kuma da yake babu kowa aka siyar dashi a lokacin, amma ita gonar tana nan duk da an siyar da rabi saboda hidimar auren Manal. Ya riƙe min Manal da Mubeena hannu biyu, ya saka su a makarantar kuɗi sun samu ilimi mai kyau tun a wancan lokacin, ya saka su a islamiyya babu wacce bata sauke alkur’ani a cikin su ba, ya basu tarbiyya matsayin mahaifin su babu abinda nake siya musu komai shi yake musu kamar yadda ko wanne Mahaifi yake yiwa yaran sa. Hatta auren Manal da kayan ɗaki ta wani abun duk shine yayi. wallahi bani da kamar aa a duniya, bai taɓa nuna banbanci tsakanin su da yaran sa ba, ko yaushe a cikin basu tarbiyayya yake yana kuma kula da rayuwar su kamar suna gaban mahaifin su ne. Basu taɓa kukan rashin mahaifi ba, shiyasa ko a makaranta nace ya saka musu sunan sa a gaban sunan su dan basu da mahaifin da ya wuce shi a duniya, ba dan shi ba da yanzu ban san inda nake ba, ban san inda yaran suke ba.”
Muryar Mama rawa take yi kuka yaci ƙarfin ta akayi shiru tana kuka, sautin kukan kawai ake ji kafin ta tsayar da kukan tace, “Daga shi sai Balaraba babar ƙawar Manal Surayya, tunda nazo unguwar nan a nan na san gidan ta, Manal da Surayya ƴar ta sa’anni ne tana son Manal ta ɗauke ta kamar wacce ta haifa. Ganin ta nake kamar Yayara, duk abinda ya dame ni zuwa nake yi na sanar da ita ta bani shawarar ta kuma rarrashe ni dan ta girme ni, ta san komai a labarina amma bata guje ni ba ta riƙe ni hannu biyu tana nuna min so da qauna. Ko rashin lafiya nayi itace ke zama wajena, itace ke kawo min abinci, maganar da nake muku ma yanzu itace a gidan Manal tana kula da ita tunda ta haihu. Da auren ta amma ta bar gidan mijin ta taje dan ta zauna da Manal kawai, dame zan sakawa waɗannan mutane don Allah?” Ta faɗa tana kuka sosai tana kallon ƴan uwan ta.
Maman Surayya da shigowar ta kenan taji ana maganaar tace, “Haba don Allah, kamar wani abu wannan ai ba komai bane an zama ɗaya.” Alhaji Ahmad yace, “ai gwara ta sanar damu duk mu sani, alkhairi ai ba a ɓoye shi duk ƙanƙantar sa.” Mama ta sake cewa, “A fannin rashin lafiyata da ta Manal, na san baku san ina da diabetics ba Manal ma tana dashi, ni abun sai ya haɗu da ciwon zuciya da na ido har idona ma ya kulle bana gani. Amma ta silar Huzaifa da Adnan mijin Manal na samu lafiya har idona suke ganina yanzu, da yake Allah ya ƙulla auren Manal da Adnan ta silar rashin lafiyata suka san jyna har Allah ya kai su ga samun rabon haihuwa. Sun bamu gudumawa sosai ta fannin lafiyar mu, magani da komai kyauta Huzaifa yake bawa Manal saboda kawai yana kallon ta kamar ƙanwar sa ce, ashe Allah ne ya saka masa ƙaunar ta kasancewar ta ƙanwar sa, da gaske ita ɗin jinin sa ce.”
Alhaji Ahmad yace, “gaskiya ne wannan, duk inda jinin ka yake sai ka ji shi a jikin ka, ai jini ba wasa bane. A kan fuskar mutum kana iya gane wannan jinin ka ne.” Mama tace, “sai Haruna ɗan wajan Baban su Manal, shima bai taɓa banbanta Manal da ƙannen sa ba, komai yana yi mata kamar yadda yake yiwa ƴan uwan sa.”
Alhaji Ahmad ya kalli Baba zai yi magana Baba yace, “don Allah kar kace komai, Mubeena da Manal tamkar ni na haife su haka nake kallon su nake kuma jin su a jikina. A wajena suka tashi kaga kenan uba ne ni a gare su, maganar godiya ko wani abun duk bai tashi ba, dan ba’a godewa uba dan ya yiwa yaran sa hidima.”
Alhaji Ahmad ya girgiza kai yana murmushi yace, “Wannan gaskiya ne. Allah ya saka da alkhairi.” Aka amsa da amin kafin Alhaji Ahmad yace, “duk bamu da abinda zamu iya biyan ku dashi sai addu’a, amma ina muku albishir da aikin hajj bana daku za’a yi in sha Allah. Balaraba dake da iyalan ki kaf nayi miki wannan alkƙwarin, kulle gidan ki zaki yi ki tafi saudia a can zaki yi babbar sallah. Haka Malam Usman, kaima da kai da matan ka da yaran ka mata dasu za’a yi wannan tafiyar nan in sha Allah.”
“Allahu akbar! Gaskiya wannan Babban tukwuci ne a gare mu da kuma ahlin mu gabaɗayaa. Na gode Allah ya nuna mana wannan lokaciin, ya kuma tabbatar da zuwan namu.” Baba ya faɗa da farin ciki aka amsa da amin. Mama dai ta kasa magana saboda farin ciki sak kallon Maman su Manal take yi dan ta kasa furta komai.
Mama tayi dariya kaɗan tace, “Balaraba ta kasa magana.” Aka yi dariya gabaɗaya Alhaji Aliyu yace, “kar ki damu, an zama ɗaya ba sai kince komai ba. Ni ma kuma na yiwa Haruna alƙawarin sabuwar mota, sannan Alhaji Usman Baban Manal kenan na yi masa alƙawarin mota da kuma gida, in kuma nasa yake so a gyara duk zan ɗauki nauyi. Balaraba kuma na yi mata alƙawarin mota itama, sannan duk nauyim karatun ƴaƴan ta zan ɗauka.”
Nan da nan waje ya sake zama wajan farin ciki ana ta murna, Alhaji Bello shima yayi nasa alƙawarin duk dan su nuna sun ji daɗin yadda aka riƙe musu ƙanwa da ƴaƴan ta.
Waje ya dawo wajan farin ciki sosai kamar komai bai faru ba, ana ta tuna baya labarim ƙuruciya ana dariya. Mama ta kalli Manal ta kalli Huzaifa tace, “Huzaifa ka ɗauki ƙanwar nan taka ka mayar da ita gida darw yayi, sannan daga yau kar na sake ganin ki a gidan nan.” Manal ta kalli Mama tace, “Allah Mama bakya sona yanzu.”
“Eh bana son ki.”
Yaya Bara’atu tace, “tunda bata son ki ai mu Muna son ki, taho wajena ma ki ƙyale ta.” Manal ta koma kusa da ita ta zauna ta riƙe kafaɗun Manal. Mama tace, “Adda har yanzu ko kwana arba’in bata yi bafa da haihuwa, Sai yawo take yi, ko gidan nan tazo yafi sau biyar.”
Tace, “to kwana arba’in ai ta bahaushe ce, tunda ta samu lafiya ai zance ya ƙare ko Manal?.” Ta faɗa tana kallon Manal ita kuma tana kwance a jikin ta ɗaga mata kai.
Baba ya kalli Mubeena yace, “Mubeena ki bi Daddyn ki ki kwana cikin ƴan uwan ki ko?.” Mubeena ta kalli Daddy taga alamun yana son hakan sai tace, “To Baba.” Ta tashi ta shiga ciki tana ji ana ta tsokanar Manal ta fito ta tarar Daddy da Huzaifa sun fita sai ƴan uwan Mama kawai kamar ba manya ba sai hira ake ana dariya.
Manal ta kalli Maman Surayya tace, “Mama muje?.” Ta kalli Manal tace, “Sai gobe zan zo miki zuwan sassafiya, saura aje a sha sanyi da abu mai zaƙi.” Manal tayi dariya tace, “ai na daina.” Maman Surayya ta fita Manal ma suka fita suka tarar Huzaifa da Daddyn suna jiran su, suka shigar motar huzaifa ya ja suka bar wajan.
BDƘB3P29
A motar shiru babu wanda yake magana Ayan yana hannun Mubeena tana yi masa wasa ita kuma Manal tana kallon gefen ta. Daddy jin shiru yayi yawa sai yace, “Mubeena an ina kika tsaya a karatu?.” Mubeena ta kalli Daddy din da yake kallon ta tace, “Na fara Digree a Yusuf mai tama sule na samu matsala na daina zuwa.”
Daddy yace, “Manal fa?.” Manal ta kalle shi tace, “ni saboda Mama daman ban fara zuwa ba, kuma ni ko wanne karatu baya burge ni nafu son culinary school, yanzu haka ina yin diploma a kai.” Daddy yayi murmushi yace, “ma sha Allah, ashe muna da professional chef bamu sani.” Manal tayi murmushi Daddy yace, “Mubeena ya kamata ki samu wata school ɗin ki fara, abinda zai faru zan saka a duba ko private school ce sai ki shiga.”
Mubeena ta amsa da to suka sake yin Shiru suna tafiya har gidan Daddy. Manal da Mubeena suka fito daga motar suka shiga cikin gidan gabaɗayan su. Duk suna falon ana ganin su aka fara musu sannu da zuwa. Har Daddy ya zauna a falon yana murmushi ya kalli sauran matan yace, “Ummimi, Aysha, Ayra, Baby, Sultan da kuma Amir ga Yayar ku Mubeena da kuma Manal.”
Ayra ta dawo kusa da Manal tace, “ƙawata” ta faɗa tana bawa Manal hannu suka tafa. Manal ta kalli Ayra ta kalli Aysha Mubeena tace, “Yaya kamar ke.”Mama da take zaune tayi dariya tace, “Wallahi kamar su ɗaya.” Aka yi dariya Daddy yace, “a nan zata kwana damu yau.”
Mama tace, “ma sha Allah kace yau nuna da babbar baƙuwa duk da ba baƙuwa bace ba.” Dariya aka yi kafin Huzaifa ya shigo yace, “Manal muje na kai ki gida, dare yayi.” Manal ta kalle shi tace, “dama ka masa waya kace zan kwana a nan.”
Daddy yace, “A’a ban amince ba, tashi ku tafi.” Ta kalli Mubeena tayi mata gwalo, Manal cikin shagwaɓa tace, “Daddy kaga tana yi min gwalo ko?.” Daddy cikin farin ciki ya kalli Mubeena yace, “A’a Yaya Mubeen, kar ki saka aurar Mama kuka.” Mubeena tayi dariya tace, “Daddy ta cika shagwaɓa ne.” Aka yi dariya Manal da Huzaifa suka fita.
Har gida Huzaifa ya kai ta ya samu Bebi ya dawo shima a lokacin ya ajjiye motar sa, ganin su sai ya tsaya har suka fito daga motar ya ƙaraso ya karɓi Ayan a hannun ta yace, “ina kiran ki bakya ɗauka, nayi zaton kin dawo gida.”
“Yayan ta ya dawo da ita, akwai damuwa ne?” Huzaifa ya faɗa yana kallon sa da sigar tsokana. Bebi yayi tsaki yace, “ba da kai nake ba ai.” Huzaifa yace, “Manal nuna masa waye ni a wajan ki yanzu.” Manal tayi murmushi kawai bata ce komai ba.