← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Isma’l ne da Yaya Bilal da Adnan a zaune wajan Daddy kamar yadda ya kira su, suna zaune a gaban sa yana amsa waya suna jira ya ƙarasa wayar dan su ji kiran da yake musu. Sai da ya kashe wayar sannan yace, “na kira ku kuma ina amsa waya. Na san kuna ta tunanin dalilin kiran ko?.”

Yaya Isma’il yace, “ba abin Mamaki bane ba ai Daddy.” Daddy yayi murmushi yace, “Magana ce akan ƴar uwar ku Maryam, tsohon mijin ta Kamal shekaran jiya ya dawo ya same ni akan yana son mayar da Maryam ɗakin ta. Yazo cikin yanayi na damuwa da nuni da nadamar sa a bayyane yana kuma burin mayar da ita ɗakin ta. Bayan ya tafi jiya sai ya aiko min Yayan sa da ƙanin mahaifin sa akan shi dai yana son a sake bashi auren Maryam. Shiyasa ba kira ku naji ya ku ke gani?.”

Yaya Bilal yace, “Kamal!, Kamal ne yake son auren Maryam duk abubuwa da suka faru Daddy?.”
“Eh Bilal, yazo a kan yana neman auren ta a karo na biyu. Yazo ya same ni cikin sanyin jiki da tsantsar nadama a bayyane.”

Yaya Isma’il ya ce, “Amma abin da mamaki Daddy.” Daddy yace, “nima nayi mamaki, amma abun ne a bayyane, nadama yayi ya gane kuskuren da ya aikata ya dawo ya gyara. Kuma ni a wajena indai har da gaske mayar da ita zai yi daman babu wanda ya cancanci ta komawa kamar sa, taje can su gyara abinda suka ɓata sannan ta cigaba da rainon yaran da Allah ya basu. Tare suka aikata kuskuren da suka aikata shi da ita, yanzu kuma ko wanne a cikin su yayi nadama yana kuma son a sake bashi dama ya gyara kuskuren sa. Ni a wajena indai har dai har Maryam tana ji a zuciyar ta zata komawa Kamal daman babu wanda ya kamata ta komawa kamar sa. Amma ya ku ke gani?, Shine dalilin kiran da nayi muku.”

Yaya Isma’il yace, “gaskiya ne Daddy, in da wanda ya kamata ace Maryam ta aura bai wuce Kamal ɗim ba. Amma abinda ya kamata muyi ita Maryam ɗin zamu tambaya, in tana da ra’ayin komawa sai ta koma, in bata dashi sai ta zauna Allah ya kawo mata wani.”

Yaya Bilal yace, “haka ne, amma duk wanda yazo neman auren ta ya bincika ya samu labari irin wanda Mahmud ya samu babu lallai ya aure ta. Komawar ta wajan Kamal shine yafi saboda ta riga ta ɓata rayuwar ta, ko ya ya aka zo bincike a kanta abinda ake gudu shine zai sake faruwa.”

Daddy yace, “duk maganar ku a kan gaskiya take, amma kune yayyen ta ky ya kamata ku zaunar da ita ku nuna mata hakan, in Allah ya yi wajan sa zata koma sai kaga silar rabuwar ta da Mahmud ɗim kenan.”
“A yadda muka sani duk wacce mijin ta yayi mata saki uku a addinance koda zata koma masa sai bayan tayi wani auren auren ya mutu, sannan kuma sai mijin da ta aura ya ɗora mata idda. Shi kuma Mahmud bayan kwana biyu da ɗaura musu aure yazo yace ya sake ta ba tare da ta tare ba. Kun ga kenan in har bata yiwa Mahmud idda ba dole sai ta sake wani auren kafim ta komawa Kamal. Amma zamu iya tambayar malamai wataƙila akwai wata fatawar da wannan ba.”

Daddy yace, “eh da gaskiya ka Bilal, gaskiya a yadda na sani nima sai sabon mijin ta ya kwanta da ita sun rabu ko ya mutu tayi idda sannan zata komawa mijin ta na baya da yai mata saki uku, amma kun san shi ilimi kogi ne, abinda na sani wani bashi ya dani ba, kullum ilimin sake yawaita yake. Kun ga kenan in bata yi idar Mahmud ba babu zancen komawar ta wajan Kamal.”

Yaya Isma’il ya kalli Adnan da tunda suka fara magana bai ce komai ba yace, “Adnan baza ka yi magana ba?.” A sannan ya kalli Daddy yace, “Daddy Maryam tayi idar Mahmud, ta sanar da ni da kanta tun bayan rasuwar Abba.”

Daddy yace, “to ya ka ke ganin maganar koma masa?.” Adnan yace, “da farko bincike ya kwnata a tsannanta a kansa a tabbatar da abinda yayi mata ba halin sa bane, wataƙila ita kaɗai ya yiwa wataƙila suna da yawa. In dai akan ta ya fara ya kuma gama dan ta koma masa ba wani abun bane tunda daman daga wajan sa ta taho.”

Daddy yace, “wannan in sha Allah duk za’a yi. Abinda ya kamata ku zauna da ita Maryam ɗin in zata koma masa shikenan sai ku san abinda za’a yi, in kuma bata da ra’ayi ai babu dole.” Suka amsa masa da to kafin ya saki murmushi yace, “Sai kuma maganar abokin ka Adnan” ya faɗa yana kallon Adnan da shima shi yake kallo.

Daddy yace, “Usman nake maka magana. Wato ashe duk wannan zaman da yayi babu aure ƴar gida za’a yi. Sati biyu kenan yana yi min magana akan shi fa Kausar yake so, nace to kaje ka samu Adnan ko Isma’il ko Bilal kayi musu magana mana. Sai yace ai gwara su Bilal ɗin da dai yazo wajan ka neman auren gwara ya fasa, nayi dariya nace daman son da kake mata bashi da ƙwari.”

Suka yi dariya gabaɗayan su har Adnan ɗin kafin yace, “ai kawai Daddy ka bar ni dashi, ba dai yace sai dai ya fasa ba?, zai fasa ɗin kuwa.” Daddy yana dariya yace, “Wallahi haka yace, amma ya kasa daina min maganar, ɗazu ma da zai fita sai da yace don Allah Daddy ka barni na je wajan ta kai tsaye kamar wani baƙo.”

Yaya Bilal yace, “da gaskiyar sa, kamar wani baƙo ace sai an sanar damu mun bada izinin ganin Kausar?.” Daddy yayi dariya yace, “ai neman aure sunan sa neman aure, babu ƴan uwantaka a fannin neman aure, yadda za’a yiwa na waje haka za’a yiwa na gida. Nace masa yaje ya samu Adnan in ya gama yi masa first interview sai ya tafi wajan ka kaima kayi masa taka sannan yazo wajena.” Suka yi dariya jin abinda Daddy ɗim yace.

Adnan yana murmushi tace, “da dai ban yi niyar faɗa ba, akwai abokin aikina Dr Yasir a asibitin mu yake, yana zuwa a kai a kai musamman in aka samu aikin da yayi shafi zuciya yana zuwa mu yi aiki tare dashi. Tunda yazo yi min gaisuwar rasuwar Abba ya ga Lubna yake yi min maganar ta, da farko na share batun sa saboda kamar ba serious bane dan an ɗauki lokaci bai sake min zancen ya ba saboda ba ya ƙasar gabaɗaya. Yanzu ya dawo ya takura min akan shi da gaske yake yana son Lubna kuma auren ta zai yi, ya san komai akan abinda ya faru da ita yace min shi ita yake so ba wani abun ba. Kuma Alhamdulillah na san komai na sa Daddy, bashi da wani bad background a iya sanin da nayi masa gaskiya, yana da kirki sosai wallahi. Dan yau ko gobe ma zai zo ya same ka akan neman auren Lubna duk da ko ita bata sani ba.”

Daddy ya faɗaɗa murmurshi yace, “Alhamdulillah! Kace ƴan matan namu duka lokaci ɗaya zasu tashi. Nan ma Fadila da Yusra Allah ya kawo mazajen ana tunanin ma bazai ɗauki lokaci ba.” Yaya Isma’il yace, “lokacin yazo, gaskiya abin farin ciki ne wannan sosai. Allah ya tabbatar mana da alkhairi.” Aka amsa da amin kafin ya Adnan ya kuma cewa, “Na tabbatar zai zo wajan ka Daddy.”

Daddy yace, “Allah ya kawo shi, ai abin yayi min daɗi sosai. Kaga Allah ya yi lokaci ɗaya ya kawo mata miji na gari mai nagarta, dan tunda har ka buɗe baki ka yabe shi na san nagartar sa ta kai. Da an biye ta yayyen ka da yanzu sun bata Mujahid.” Yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Yaya Isma’il yace, “gaskiya dai Adnan yana da kaifin tunani Daddy, gashi dai shine ƙaramin mu amma yafi mu hangen abinda zai je ya dawo. Muna matuƙar farin cikin samun sa a cikin ahlin mu gabaɗaya.”

Yaya Bilal yace, “gaskiya ne wannan, Adnan ya zama kamar garkuwa a gidan mu. Sai dai muce Allah ya tabbatar da farin cikina rayuwar sa.” Daddy yace, “wannan gaskiya ne. Adnan na daban ne yana da hangen nesa da kaifin tunanin da yafi na wasu manyan mutanen. Allah ya jiƙan mahaifin ku ya sa yana aljanna.” Suka amsa da amin kafin su yiwa Daddy sallama su ka tafi.

Kai tsaye gida suka wuce a tare suka shiga da mota suka ajjiye, kai tsaye suka wuce wajan Mama da niyar gaishe ta. A nan suka samu Mamy ma a zaune da Maryam suna ya hira. Ganin shigar su tare sai Mamy tace, “daga ina haka na ganka gabaɗayan ku?.” A tare suka gaishe su suka amsa Yaya Isma’il yace, “Mun je wajan Daddy ne shine muka biyo mu gaisa.”

Yaya Bilal yace, “Daman akwai maganar ma da muke so zamu tattauna daku” ya kalli Lubna da Kausar da suke zaune yace, “Lubna ku shiga ciki.” Suka amsa da to suka tashi suka shiga ciki.

Yaya Isma’il yace, “Daddy ne ya kira mu akan maganar auren Maryam.” Gaban Maryam ya faɗi matuƙa ta sunkuyar da kai ƙasa. Mama tace, “to wani abun ne ya faru?.”
“Kamal ne yaje wajan Daddy akan yana son mayar da Maryam ɗakin ta, kafin yaje wajan Daddy ma ashe ya fara zuwa wajan Adnan bai saurare shi ba shine yaje wajan Daddy. Yana son mayar da ita ɗakin sa su gyara abinda suka ɓata, shine Daddy ya kira mu ya sanar damu ya muke ganin lamarin.”

Mama ta girgiza kai tace, “Kamal dai? Lallai bashi ma da kunya.” Mamy tace, “to yanzu me ku ka yanke ku?.” Yaya Bilal yace, “sai abinda ku ka ce ai Mamy, shiyasa muka zo mu sanar daku.”
Chapter 72 · 0% Book details