← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 84

Sashe 74

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da baccin nata yayi nisa ya tashi ya ɗauki Ayan da ya fara kuka ya fita daga ɗakin a bayyane yana cewa, “kar fa naje Manal na da ciki, to kwata-kwata kwanan Ayan ɗin nawa da zata yi ciki?. Dole ayi test in ta farka” ya faɗa yana yana ta rarrashin Ayan da yake ƙananun koke-koke.

Manal ta jima tana bacci har magriba sannan ta farka, tana tashi ya shigo ɗakin ya kalle ta yace, “ya jikin?.” Ta tashi zaune tace, “naji sauƙi, naji alamun zuwan period ɗin ma yanzu.” Ajiyar zuciya yayi cikin jin daɗin hakan amma bai nuna mata ba, ta kalle shi tace, “da ina ta fargaba kar naje ciki ne dani.” Yayi yar dariya tace, “matsoraciya.” Bata ce komai ba ta tashi ta shiga banɗaki shi kuma ya fita yana cewa, “ki yi sauri ɗan ki yunwa yake ji.”

Bayan kwana biyu da maganar Maryam da Kamal yazo gidan wajan Maryam, shi kansa kunya yake ji dole ce ta kawo shi gidan da bazai iya zuwa ba. Bai iya gaisawa da Mamy ba a harabar gidan ya tsaya Nabil ya sanar da Maryam tare suke. Nauyin fitowa ta dinga ji dan bata san saka tozali dashi, zuciyar ta rawa take yi cikin tsananin tashin hankali.

Yaya Bilal ne ya same shi a tsaye nan yayi masa iso har babban falon Abba ya ce zai turo masa Maryam ɗin. Babu yadda Maryam ta iya ta amsa kira ta ahiga falon zuciyar ta ma bugawa hawaye yana sakkowa daga idanun ta.

Tunda ta shiga taja ta tsaya sai kuka da take yi, jikin Kamal yayi sanyi sosai ya sunkuyar da kai ya rasa abinda zai ce mata. Sun kwashe mintina sama da ashirin a haka kafin yayi ƙarfin halin cewa, “ina sake baki haƙuri a karo na babu adadi Maryam, ki yafe min ki bani dama na gyara kuskure na. Na san na cutar da ke cuta mai yawa, ki yafe ni ki bani dama a karo na biyu.”

Bata iya magana ba kuka take yi sosai shi kansa hawaye yake yi ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “ki yafe min Maryam, na yi nadamar abinda na aikata miki tun ba yau ba.” Cikin kuka tace, “saɓon Allah da ka saka na aikata shi ka ke na yafe maka Kamal?. Me na yi maka ka zaɓi yi min wannan hukuncin? Me na aikata maka ka zaɓi wulaƙanta ni?.”
“Baki yi min komai ba sai alkhairi, sharrin shaiɗan da son zuciya ne ya kaini ga abinda na yi.”
“Daman kana da niyar hakan, kana sane ka saka na dinga tura maka makaman da ka yi amfani dasu wajan lalata min rayuwa.”

Kamal ya goge idanun sa ya ce, “babu lallai ki amince da abinda zan ce miki, amma wallahi na yi nadamar duk abubuwan da suka faru. Ko wani na gani zai aikatawa wata makamancin abimda na yi miki ni mai hana shi ne.” Maryam tayi murmushin takaici tace, “wai ni ka dinga tozartawa da hotuna, ni ka ɗauki hotona ka saka a duniya duk dan saboda na saɓawa Allah.”

Kamal ya ce, “Wallahi Maryam bazarana ce, bazan taɓa iya aikata abinda nake faɗa miki ba. A status ɗin da na saka wallahi sai da na cire number kowa na bar ki ke kaɗai ce zaki gani. Maryam in da ace da gaske zan yi posting da na yi tun farko, wallahi ba zan iya aikawa ba.” Bata ce komai ba sai goge ido da take yi ya ce, “ki yafe min.”
“Wataƙila ka mayar da neman mata sabuwa halayyar ka yanzu.”

“A’a wallahi, bayan ku mata na guda biyu wallahi ban taɓa bin wata mace ba har yanzu.” Maryam ta kalle shi kallo irin na takaici tace, “wata zaka bawa wannan labarin ta yarda ba ni ba Kamal. Tun farko ni ce na bada fuskar faruwar komai, da na ji maganar ɗan uwana da hakan bata faru ba. Na dinga biyewa zuciyata nake zama tare da kai. Laifina ne ba naka ba.”

Kamal ya zube guiwa biyu a ƙasa ya ce, “ki yi haƙuri, ki yafe min na san nayi miki ba daidai ba amma ki sake bani dama na gyara abinda na ɓata. Ina son kare martabar ki ta ɗiya mace da ta yaran ki, bana so a sake samun matsalar da aka samu a auren ki da Mahmud. Ni na jawo miki, ni na shafa miki baƙin fenti. Na dawo yanzu da ƙarfin guiwar goge wannan tambarin da nayi miki Maryam.”

Kallon sa take yana durƙushe yana hawaye ta ja numfashi bata iya sake magana ba ta fita daga falon. Tashi yayi cikin jiki dan ya san daman hakan zai faru ya fito ya tafi.

Bayan wani lokaci.

Lokaci yana ta gudu Maryam da Kamal cikin ikon Allah sun daidaita kan su da taimakon zaɓin da ta barwa Allah, har antsayar da lokacin auren Kausar da Lubna, Maryam kuwa ba a ɗauki wani lokaci ba ta koma gidan mijin ta. Mujahid ya shiga tashin hankali jin wannan labarin amma daga baya ya tabbatar da sharrin sa ne yake bibiyar sa ya koma kansa.

Rumana ma da take garin Abuja ta samu mijin da take ganin zata iya rayuwar aure dashi. Mama ta kira ta fara faɗawa labarin, Mama tayi farin ciki sosai kafin ta kira Manal ta faɗa mata. Tana zaune suna waya da Rumana ya shigo ya zauna a lokacin Manal na cewa, “Na taya ki murna Yaya Rumana, Allah ya sanaya alkhairi.”

Rumana tace, “amin ƙanwata. Kin yi nisa sosai shiyasa ba’a haɗuwa, ko yaushe muna tare da Mubeena, ɗazu na dawo daga gidan ta.” Manal tace, “nima ina nan zan zo Abuja saboda bikin ƴar Daddy, zan biyo mu sha hira.” Rumana tace, “Allah ya kawo ki, ki gaishe da Bebi in ya dawo.” Ta kalle shi tace, “zai ji in sha Allah.”

Kallon ta yayi bayan ta kashe wayar kamar zai yi magana sai ya fasa tace, “An saka auren Yaya Rumana.” Ya girgiza kai tace, “Mummy ta faɗa min, Allah ya sanya alkhairi” ya faɗa yana yanayin fuskar sa yana canjawa. Manal ta kalle shi tace, “Amin. Lafiya naga ka canja?.” Ya ɗan kulle ido yace, “lafiya lau. kice muna da biki sosai. Ga lubna, ga Kausar, ga Ruman, ga Ummi, ga Yusra da Fadila. Duka ƴan matan ƙannen namu zasu yi aure, kuma tsiran auren nasu bai wuce sati ɗaya zuwa biyu ba.”

Manal ta girgiza tana murmushi tace, “gaskiya ne. Ina so naje Abuja gidan Yaya Mubeena sannan naje na duba Daddyn Jalingo, Mama tace min yayi rashin lafiya sosai. Sannan ga gida Daddyn mu ma, tunda suka dawo Abuja sau biyu kawai naje. Kuma kaga har da biki Ummi, ya kamata muje shirye-shirye.”

Ya girgiza kai yace, “sai ki shirya ki je ki yi kwana biyu ki dawo. Ɗazu ma mun haɗu da adda Halima tace nace miki ta dawo Kano zata shigo.” Manal da murmushi tace, “da gaske? Ai kam da daddare zan je mu gaisa.” Ya ɗaga mata kai tace, “Allah ya nuna mana lokacin.” Ta amsa da amin tana kwantar da kanta a jikin sa.

Da daddare suka je gidan adda Halima suka gaishe ta kafin su wuce gidan Mummy. Mimi da Farida suna nan saboda shirin biki da ake ta yi, suka shiga da sallama aka amsa suka samu waje suka zauna.

Munmy ta kalle su tace, “barka da zuwa, gwara da kika zo a tattauna daku. Ga shi nan ya faɗa muku nauyin me mai ɗaukar muku da bikin ku.” Yayi murmushi kaɗan yace, “Mummy duk abinda suke so ai sai su faɗa min.”

Mimi tace, “Yaya daman ina ta so na kira ka, Akwai wata allura da aka rubuta min akace wai na tabbatar na siye ta.” Ya kalli Mimi yace, “a ina aka rubuta miki?.”
“Anc ɗin da nake zuwa,ka ganta” ta faɗa tana miƙa masa takardar da take hannun ta.

Karɓa yayi ya kalla ya kalle ta yace, “jinin ki wanne group ne?.” Mimi tace, “AA ce ni.”
“ba genotype nake nufi ba, blood group.”
“Oh B positive ne.” Ya girgiza kai yace, “Shi kuma Tahir fa?.” Mimi tace, “AB negative.”

Ya bata takardar ya ce, “shine matsalar, jinin ki positive ne nasa negative shine matsalar da aka samu.” Farida tace, “matsala kamar ya? Bamu gane ba.” Ya kalle su yace, “ba wata damuwa bace ba ai, kawai kin taɓa ganin inda wuya da ruwa suka haɗu waje ɗaya?.” Farida tace, “A’a, ai dole sai ɗaya ya kashe ɗaya.”
“To shine matsalar da yaron cikin ta yake ciki, jinin ta positive ne na mijin ta negative, kuma jinin su ne yake cycleting a jikin yaron. Ya jan nata positive, ya jan nasa negative a ganin ki me zai faru?.”

Farida tace, “taya zan sani?, amma yaron zai iya mutuwa yaron.” Adnan yace, “Wannan shine amfanin yin wannan allurar da aka baki. Amma kar ki damu fa bawai babyn zai mutu bane, kina haihuwa za’a yi miki wannan allurar kuma zaki raini yaron lafiya. Tunda har aka baki allurar ai babu damuwa, ana yi miki ita shikenan. Hatsarin ma yafi ga babyn na biyu ko na uku, na farko bai cika mutuwa ba.”

Mimi tace, “yanzu yaushe kenan za’a siyi allurar?.”
“A’a sai kin haihu, in kika siya yanzu zata lalace ne. kar ki damu fa ba wani abin damuwa bane wannan.”
Mama tace, “ikon Allah, tsirfa dai kala-kala.” Yayi murmushi bai ce komai ba ya tashi ya fita. Hira suke ta yi yadda biki zai kasance har dare yayi yazo suka tafi.

Bayan wasu shekaru.

BDƘB3P47

A cikin shekarun walwala da kwanciyar hankali ta wanzu a ahlin gabaɗaya. An yi shagalin biki  dukkan su babu wacce bata haihu ba a cikin wanda aka aurar. Daddyn Jalingo ya cika alƙawari,duk wanda ya yiwa alƙawarin aikin hajji yaje ya sauke farali ya dawo. Babu sauran matsala ko damuwa a tare dasu rayuwa suke hankali a kwance.
Chapter 74 · 0% Book details