← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 84

Sashe 39

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abba ya girgiza kai kawai bai ce komai ba Daddy ya kalle su ya kalli Mamy yace, "Me ma kika ce?, Bamu cancanci yafiya ba ko? Nima na sani, nasan bamu cancanci a yafe mana ba. Kuskuren da muka aikata baza mu taɓa goge shi ba, mun ci amanar yarda da amincewa, Mun kuma cutar da marainiya."

Yaya isma'il yace, "kuskure an yi shi Daddy, an aikata kuskure sosai fiye da tunanin mai tunani. Amma in sha Allah zata yafe komai ya wuce kamar bai faru ba, Sai an bi komai a sannu an nemi yafiyar Allah ba iya ta ta yafiyar ba." Abba yace, "ta ina komai zai wuce? Komai bazai wuce ba isma'il."

Shiru ya biyo baya babu wanda ya sake magana a cikin su, kowa da irin abinda yake zuciyar sa wanda yake tunani. wayar Bebi ce take ƙara ya ɗauko ya duba ganin Manal ce sai ya mayar da wayar ya ajjiye bai ɗauka ba, Daddy ya kalle shi sai  ya kulle ido ya buɗe bai ce komai ba.

Fitowar suka yo daga falon masu kuka suna kuka masu ƙunar zuciya suna jin raɗaɗin a ransui Abba da Daddy dai sun jima a cikin suna magana kafin Daddy ya fito sauran matan su fito su hau mota su tafi kowa jiki a sanyaye kamar an yi musu dukan tsiya.

Bebi wajan Mama ya shiga ya same ta a zaune da yaran ta mata ko wacce yanayin fuskar ta zaka kalla ka san abinda suka ji ya shiga ran su, ya kalli Mimi da Farida yace, "baza ku tafi bane?."

Yadda yayi maganar ma tausayi ya basu Farida tace, "yanzu zamu tafi." Ya kalli Mama yace, "zan wuce gida Mummy, ki tabbatar Rumana ta sha maganin ta." Mama ta girgiza kai tace, "to Allah ya kiyaye hanya. Amma Adnan magana ta gaskiya ko; ko nice mahaifiyar su Manal sai na raba auren ku, domin ba zan bar ƴata tana auren ɗaga irin mahaifin ku ba."

Kallon Mama yayi fuskar sa babu walwala kana gani kasan yana da damuwa sosai, kamar zai magana sai kuma ya fasa yayi murmushin yaƙe, Mama tace, "ban san a shekarun baya akwai macuta irin iyayen ku ba." Bebi ya sauke kai ƙasa ya sake kallon Mama yace, "Sai da safe, Mimi ki kira mijin ki wuce gida ita waccan ta saba" ya faɗa yana fita bai sake cewa komai ba amma zuciyar sa mugun bugawa take yi sosai, tashin hankalin sa yafi ko yaushe dauriya kawai yake yi.

BDƘB3P22

Lokacin da ya shiga cikin gidan babu kowa a falon har nata falon bai ji motsi ba alamun sun kwanta kenan, bai shiga ciki ya shiga ɗakin sa yana cire lins ɗin jikin rigar sa tare da cire agogo ya ajjiye. Buɗe ƙofar aka yi aka shigo ya kalle ta itama shi take kallo tace, "Sannu da zuwa."

Maimakon ya amsa sai ya zuba mata ido yana kallon ta yana so ya ga ko tana kama da ƴan gidan su Huzaifa ko Daddy, kallon ta yake yi har ta tsargu bai ga kama da kowa a cikin su ba dan ita da Maman ta take kama gabaɗayan ta. Kallon sa take yi cikin mamakin kallon da yake mata tace, "Lafiya?." Ɗauke kai yayi daga kallon ta ya ce, "na jima ko? Muna tare dasu Abba ne da Daddy shiyasa."

Manal tace, "sannu da zuwa, abinci fa?." Ya girgiza kai yace, "ƙyale abincin nan bazan ci ba."
"Amma yau gabaɗaya baka ci komai ba."
"Naci ɗazu tare dasu Huzaifa." Ta matso kusa dashi tace, "Shikenan baza ka kuma ci ba?."

Ya kalle ta yace, "bana jin zan iya gaskiya, ki saka a fridge gobe sai a bayar dashi tunda dare yayi" ya faɗa yana wuce ta ya shiga banɗaki. Zama tayi a kan stool ɗin da yake gaskiyar ɗakin, tayi shiru tana tunanin abinda yake damun sa haka duk yabi ya canja ko abinci baya ci sosai. Tana nan zaune ya fito ya shirya ya samu waje ya zauna, ya ɗauki wani littafi yana dubawa wanda yake dauke da hoton zuciya a bangon sa.

Shiru yaji  tayi bata ce komai ba sai ya ɗago ido ya kalle ta yaga shi take kallo ya ajjiye littafin shima ya zuba mata yana kallon ta bai ce komai ba ita bata ce ba. Katse shirun tayi ta hanyar cewa, "akwai abinda ka ke so ka faɗa min ka ƙi ka faɗa min, tun ɗazu na lura da hakan amma kace babu komai."

Jin abinda tace ai ya tuno da maganar Rumana dan maganar Daddy ta danne ta ta, ya kulle ido ya buɗe yaji ta zauna kusa dashi tace, "baka son faɗa min damuwar tunda nazo gidan nan a matsayin matar ka, in zan tambaya sau ɗari baza ka faɗa min damuwar ka sau ɗaya ba. In baka faɗa min damuwar ka ba wa zaka faɗawa? Ni ce a kusa dakai yanzu sama da kowa, ko kana ganin bani da hankalin da zan iya baka shawara akan abinda yake damun ka?." Ya girgiza kai ya ce, "A'a ni ban ce haka ba, babu abinda yake damuna ɗin ne shiyasa ban faɗa miki ba."

Manal ta yi murmushi tace, "Hmmm haka kake cewa daman ai, ko yaushe kace babu abinda yake damun ka bayan kuma a zahiri ana ganin ka an san kana da damuwa. Shikenan Partner, bazan sake tambayar damuwar ka ba, kayi haƙuri tunda baka so naji na daina tambayar ka, na daina tambaya balle kace min babu naji haushi" ta faɗa tana niyar tashi, ya riƙo hannun ta ya dawo da ita ta zauna.

Ya kalle ta yace, "Kar ki canja min magana don Allah, babu abinda yake damuna in akwai kece ta farko da zan faɗawa. Kar wannan tunanin ya shiga zuciyar ki in kika ce haka baki min adalci ba."

"Ka taɓa faɗa min damuwar ka ne? Ka taɓa buɗe baki kace min ga abinda yake damuna?. Ko yaushe ce min ka ke yi babu kuma wallahi akwai, Kaga tambayar bata da amfani tunda nice baka so na sani." Ya kalle ta ya riƙe fuskar ta da hannun sa yace, "in akwai babu abinda zai saka na ɓoye miki my life partner. Ni yau wani na gani mai matuƙar kama dake." Jin ya canja maganar sai ta share shi itama bata ce komai ba.

Yayi murmushi yace, "Haba partner meye na fushin kuma?." Ta kalle shi idanun ta a buɗe tace, "ni fushi nayi? Akan me zanyi fushi to?." Yadda tayi magana tana juya idanun ta sai yayi murmushi ya yiwa idanun nata kiss yace, "Wannan ido suna da kyaun gani."

Nan ma tayi masa shiru bata ce komai ba ya sake cewa, "Seriously yau naga mai kama dake Manal, kuma babban mutum ne har nake tunanin anya ba mahaifin ki bane ba, har zan je na yi masa magana dan na san zaki murna in kika gan shi, Sai kuma na fasa saboda Abba yana kira na lokacin."

Manal ta taɓe baki tace, "gwara ma da baka je ba." Ya kalle ta yace, "Meyasa?, kefa ki ka cemin kina son ganin mahaifin ki."
"Yanzu bana so. Kuma lallai ne dan ya kasance muna kama sai ya zama maahifina?."
"Kama fa sosai na gani, ko ba mahaifin ba kuna da alaƙa ta jini dashi."

Kafin tayi magana yace, "bana shakka ma mahaifin ki ne, kuma zan je na nemo shi ko dan ke." Manal ta kalle shi tace, "wallahi kar ka fara, haka aka ce maka ina da buƙatar ganin maahifina ne?." Da mamaki yace, "haka kika ce min mana, kin manta muna tafiya a mota kika ce kina so ki ganshi?."
"Yanzu bana so wallahi, bana so ko kaɗan."
"bakya son ganin sa?."
"Ko a mafarki kuwa, shi yanzu in ma aka nuna masa ni akace ni ƴarsa ce sai ya kalle ni matsayin wacce ya haifa?." Bebi yace, "to me zai hana? Ba mahaifin naki bane."

Manal tace, "amma akwai rashin ta ido ma a cikin abun, ya tafi ya bar mu a wajan mahaifiyar mu bayan ya kwashe dukiyar ta bai yi tunanin daga inda ya karɓo ta ba, bai yi tunanin bata da kowa sai shi ba, bai yi tunanin halin da ya barta ba, bai yi tunanin a inda zamu rayu ba. ya tafi sama da shekaru masu yawa yanzu kwatsam sai ya dawo yace mu ƴaƴan sa ne?."

Kallon ta yake yi kafin yayi magana tace, "bai san komai namu ba ya tafi ya bar mahaifiyar mu da wahalar mu, bai san ci da shan mu ba, karatun mu da suttura, tarbiyya da kula damu duk bai sani ba, rana ɗaya sai yazo yace ai shine ya haife mu?." Bebi yace, "to ai ba ƙarya bane shi ɗin ne ya haife ku."
"Shi ya haife mu kuma ya bar mu ba, ya haife mu ya tafi ya barmu tunda ya samu abinda yake so. To yaje ya sha zaman sa da shi da iyalan sa wanda ya zaɓa ya kuma gina rayuwar su da dukiyar Maman mu, mu kuma ya bar mu mu cigaba da rayuwa yadda muka saba, babu shi a rayuwar ba babu abinda muka fasa sai cigaba ma da mu ke yi."
Chapter 39 · 0% Book details