Sashe 10
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk a gidan suka yi sallar i'sha saboda kiran Abban, suna idarwa ya dawo gidan burin sa kawai yaji me yayi zafi haka har Mama take son raba su?. Yana shigowa harabar gidan wayar sa ta fara ƙara, ya ɗauko ta daga aljihu ya duba ganin sunan Manal ya saka shi ɗauka da hanzari.
Daga can ɓangaren Mubeena tace, "Dr Mubeena ce dai." Da hanzari yace, "ina jin ki."
"Manal ce babu lafiya, yanzu haka muna asibiti. Kamar yana gaban ta ya wara idanu yace, "hasbunalalahu wa'inmal wakil! Me ya same ta? Wanne asibiti ne? Me suka ce yana damun ta?. Ki min bayani ya jikin nata?."
Mubeena tace, "muna nan asibitin freedom" kafin ta ƙarasa yace, "gani nan zuwa" ya faɗa yana yanke wayar ya ƙarasa wajan mota da sauri ya shiga ya fita daga gidan a guje.
Asibitin ya nufa gabaɗaya hankalin sa a tashe yake sai bayan ya shiga ya sake yi mata waya ta faɗa masa inda suke ya nufi inda take ya tarar da ita a tsaye a ƙofar ɗakin tana jiran sa.
Ya kalle ta yace, "a wanne hali take ciki?." Mubeena tace, "da yake tun ɗazu muna nan har tayi bacci ta tashi, sun ce yunwa ke damun ta da kuma rashin samun bacci, in aka cigaba da tafiya haka jinin ta zai iya hawa saboda rashin bacci, sannan za'a iya rasa babyn." Adnan ya sauke numfashi yace, "tana ina?."
Mubeena ta nuna masa ɗakin ya ya wuce ta ya shiga ya hango ta a kan ɗaya daga cikin empty ɗin gadajen ɗakin guda uku a zaune, ta zubawa waja ɗaya ido tana kallo, kana ganin ta ka ganta kasan tana cikin damuwa.
"Partner!" Ya faɗa yana ƙarasawa inda take. Da hanzari ta dago tana kallon sa kawai sai ta fashe da kuka ya ƙarasa da sauri ya zauna a gefen ta ta rungume shi tana kuka sosai. Shima riƙe ta yayi a jikin sa yana shafa bayan ta a hankali cikin kewa da soyayya mai nuni da tsantsar kulawa. Yadda ta cukuwikwiye shi ne ya saka ya sake riƙe ta gam-gam a jikin sa, babu wani space da iska zata ratsa tsakanin ƙirjin su. "Ki daina kuka partner, ki bar kuka baki da lafiya" ya faɗa yana riƙe kanta a ƙirjin sa.
Kuka take yi sosai cikin so da ƙauna da kuma kewar mijin ta, ta rasa ina zata saka ranta taji daɗi komai ya tsaya mata cak a lokacin da bata yi tunanin haka ba. Sassauta riƙon da tayi masa tayi ya ɗago ta daga jikin sa ya riƙe fusksr ta da duka hannayen sa guda biyun yace, "jikin ki akwai zafi har yanzu, Meyasa bakya son cin abinci?." Kallon sa take yi shima kallon ta yake ta lumshe ido ta sake komawa jikin sa ta kwanta tana kuka ƙasa-ƙasa.
Bayan ta yake shafawa a hankali yace, "bana so naga kina kuka, ki nutsu mu yi magana." Zagayawa tayi da hannaun ta ta sake riƙe shi tana cusa kanta a ƙirjin sa, kewar mijin ta take ji sosai musamman ƙhamshin sa da tayi missing kwana biyu, ta kasa boye abinda take ji hakan ya saka take sake maƙale masa
Ganin yadda take riƙe shi sai yayi shiru yana riƙe da ita bai ce komai ba itama bata ce komai ba. Ɗago kai tayi tana sake kallon sa shima ita yake kallo ido cikin ido kafin tayi magana yace, "ina son ki Manal, bazan iya jure rashin ki ba." Lumshe ido tayi taji yana goge mata hawaye yace, "Meyasa bakya cin abinci?." Buɗe ido tayi bata ce komai ba ya yi mata kiss a goshi, ya sake yi mata wani a wuyan ta, ya sake yi mata wani a kumatu ya riƙe fuskar ta yace, "meyasa?." Muryar ta na rawa tace, "bana iya ci."
"Amma hakan zai iya cutar dake ai, in wani abun ya same ki ya zanyi? Don't forget your my life partner, ciwon kai in kika yi bazan so ba sai dan babu yadda zanyi, ki dinga cin abinci shine zai saka lafiyar ki ta inganta sosai."
Manal tace, "kasan bana iya ci ko? Ko a gida bana iya ci ka san da hakan."
"Shiiii! to daina kuka shi ne bana son gani" ya faɗa yana sake mayar da kanta jikin sa.
"Babu abinda zai raba mu Manal, in sha Allah komai zai wuce kamar bai faru ba." Manal jin haka sai ta janye jikin ta tace, "i'm sorry partner!." Kallon ta yake yi alamun me ya faru tace, "kayi haƙuri, bazan iya ƙin yiwa Mama abinda take so ba, zan yi amma ba dan bana son ka ba. Wallahi Ina sonka, ina ɗaunar ka, Amma zan iya rabuwa da kai saboda Mama."
A firgice ya kalle ta yace, "What! Manal me kike cewa?."
"Abinda kaji nace, zan iya haƙuri da son sa nake maka nayi abinda Mama take so. Mama tace ba dan bata son ka dank ba, kawai tana so na rabu da kai partner..!" Ta faɗa tana kuka mara sauti.
Ya girgiza kai yace, "ki daina faɗar haka, ki daina faɗa Manal, babu abinda zai raba mu sai mutuwa." Ta ja numfahsi tace, "kayi haƙuri, Kayi haƙuri!." Hannun sa ya saka a bayan ta ya riƙe ta sosai a ajikin sa kamar zai mayar sa ita ciki saboda yadda ya riƙe ta sosai. Itama haka take so dan duk da tana jikin sa amma kewar sa take ji kamar basa tare.
"Zaki iya rabuwa dani partner? Zaki iya zama ba tare dani ba?." Bata ce komai ba sai sake gyara kwanciya da tayi a jikin sa yace, "Nasan baza ki iya ba, kina ƙauna ta kamar yadda nake ƙaunar ki. Wallahil azim lokacin da nake tunanin ke ƙanwata ce Allah kaɗai yasan irin damuwar da na shiga, Allah kaɗai yasan irin tashin hankalin da zuciyata yake ciki. Bana iya cin abinci, bana iya bacci, bana iya aiki, bana iya komai sai tunanin ki partner. Na tabbatar kece rayuwata, in na rasa ki rayuwata zata shiga wani hali Manal, don Allah kar ki rabu dani ki zauna dani har abada, rashin ki babbar illa ce a gare ni."
"Nima ina son ka Partner, ina son ka!" Abinda tace kenan tana kwance a jikin sa.
"Kar ki rabu dani Manal, duk runtsi duk wahala ki kasance dani, zaman ki tare dani shine kwanciyar hankalina." Numfashi take saukewa a hankali cikin azabar so da kewar mijin ta. Ɗan knocking ƙofar akayi a hankali hakan ya saka ya ɗago ta daga jikin sa ya kalli ƙofar, Mubeena ta shigo tace, "ga abinci ka bata kai zata ci."
Ƙarasowa tayi ta ajjiye abinci ta juya tana aiyana dole ma tayi aure wannan soyayyar da Manal da Adnan suke yi ta saka mata son yin aure da gaggawa. Ɗaukar abincin yayi ya buɗe ya zuba mata ya ƙara da salad sosai ya kai, ya ɗebo ya kai bakin ta ta girgiza kai shima ya girgiza kai yace, "Sai kin ci." Turo baki tayi ya nata kiss a bakin ya fara bata abincin tana ci a hankali.
Taci sosai kaɗan ta rage ya ƙyale ya ajjiye ragowar, sake kwatar da ita yayi a jikin sa yan shafa kanta zuwa bayan ta a hankali bacci ya ɗauke ta tana jikin sa. Ganin tayi bacci ya kwantar da ita a kan gadon yana kallon ta.
Numfashi ya sauke ya taso ya fito a nan ya tarar da Mubeena a zaune ya ƙarasa yace, "Don Allah duk abinda ake buƙata ki kira ki sanar dani, in akwai wani abun duk dare ki faɗa min. Yanzu taci abinci sosai kuma tayi bacci, koda zata farka ki sanar min ɗon Allah."
Mubeena tace, "in sha Allah zan faɗa maka." Yayi murmushi yace, "na gode da taimakon ki." Tayi murmushi kawai ya wuce ya fita ita kuma ta koma ta zauna.
Kai tsaye gida ya wuce yana ajjiye mota ya shiga ɓangaren Abba a nan ya tarar da gabaɗaya ƴan gidan suna nan har lokacin da alama jiran sa ake yi. Ya shiga da sallama aka amsa Abba yace, "shikenan gashi nan ma, kowa ya zauna mu yi abinda ya tara mu."
Bebi yace, "ayi min haƙuri naje asibiti ne." Abba yace, "an yi maka, zo ka zauna na warware maka wacece mahaifitar matar ka wajena." Jiki a sanyaye Bebi ya zauna yana jira yaji abinda Abba zai ce.
BDƘB3P07
Abba ya kalle su gabaɗayan har dasu Mama da suke zaune ya sauke numfashi ya dafe kansa, nauyi yake ji a zuciyar sa musamman in ya tuna da abinda ya faru da Maryam da kuma Lubna. Hankalin sa tashi yake yi sosai ya rasa inda zai saka ransa shiyasa gabaɗaya ya shiga damuwa sosai.
Daƙyar ya kawar da tunanin zuciyar sa yace, "A wani lokaci a baya shekara ashrin da wani abun da ya wuce, na kassane ina tafiye-tafiye daga wannan gari zuwa wannan gari don kasuwanci musamman siyan gonaki da dabbobi da sauran abubuwa masu daraja a wancan lokacin. Ina shiga garuruwa da yawa musamman garin fulani, na shiga na saro dabbobi na tawo dasu Kano na siyar. Ko na siyi gona a can bayan wani lokaci na siyar da ita ko na bada hayaa dinga yin noma ga mutanen ƙauyen."
"Akwai wani abokina wanda muka haɗu a harkar siye da siyarwa ɗin nan da nake faɗa muku, muka saba dashi sosai dan mutum ne mai faran-faran da saurin sabo, kuma ya fini sanin harkar kasuwanci sosai wani abun shine yake buɗe min ido a kai, sabon mu yayi nisa har ya zama tare muke zuwa mu dawo tare. Shi yana zaune a Zaria ne ni kuma ina zaune a Kano, in gabas zamu yi zan je tashar Zaria mu haɗu dashi daga nan mu tafi, in yamma zamu yi zai zo tashar Kano mu haɗu mu tafi. Aliyu yana da ɗabi'ar son kuɗi sosai, dan a harkar kasuwancin mu ma ƙarara zai nuna zai yi maka wayo saboda ya fika cin riba, fara'ar sa da saurin sabon sa wani lokacin ya kan juye ya zama na cuta in ya samu dama."