← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 84

Sashe 11

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya kalli Mamy yace, "in zaki iya tuna shi ya taɓa zuwa wancan gidan, kuma a lokacin da ke kaɗai ku ka gaisa, a lokacin ina tunanin haihuwar Maryam ne ko Farida dai na manta. Amma kamar lokacin Hauwa bata nan basu haɗu dashi ba gaskiya." Mamy tace, "bazan iya tunawa ba tunda ba sanin kirki nayi masa ba gaskiya."

Abba yaja numfashi ya kalle su yace, "na san da yawan ku musamman Bilal da Ismal'i da kuke ƴan kasuwa zaku san sunwn Alhaji Muhammad Jalingo, ko baku san shi ba nasan kun san wani baban mutum mai ƙarshen suna Muhammad Jalingo ko?." Yaya Bilal yace, "sosai ma kuwa Abba, family Muhammad Jalingo ba ɓoyyayyu bane a fannin kasuwanci. Kowa yasan Alhaji Ahmad Muhammad Jalingo, Wanda yake shine na uku a africa a fannin kuɗi na kasuwanci.

Abba ya girgiza kai ciki gamsuwa yace, "Marigayi Muhammad Jalingo ɗin da kansa nake magana a kai yanzu, Allah ya gafarta masa yasa yana aljanna." Aka amsa da amin kafin Abba yace, "Garin Taraba state gari ne na mazauna yare kala-kala, baza ka keɓance yare guda ɗaya kace ai garin Taraba zamuna cikin sa wannan yaren ne kawai suke yi ba, yana da yaruka daban-daban wanda suke zaune a cikin sa."

"Garin Taraba gari ne na kasuwanci musamman abinda ya shafi harkar noma da kasuwanci, tun a shekarun baya garin yana karɓar baƙi kala-kala wanda suke shiga don kasuwanci. akwai wani da yawon kasuwancin mu ya kai mu garin Taraba state cikin babbar birnin su Jalingo. Bamu san ko ina ba mu dai mun je da niyar kasuwanci kamar yadda muka saba, an sauke mu a tasha mu kuma mun shiga cikin gari. kasnacewar garin ya kasance yana da Fulani sosai, a wancan lokacin muka ɗari-ɗari saboda rashin yardar da Fulani basu dashi na lokacin baya."

A cikin unguwar Gadi wacce take a cikin tsakiyar birin Jalingo muka samu wani babban masallaci don yin sallar azahar dan da wuri muka sauka a garin. Mun yi salla a babban masallacin mun fito dani da Ali muna tattauna inda zamu je mu kwana, bamu san ko ina ba haka bamu dan kowa ba karon farko da ya kai mu garin. Har gwara sauran garuruwan da muke zuwa muna da ido a can, dan akwai mutanen Ali a can sosai saɓanin Jalingo. Muna ta tattauna abinda zamu aai ga marigayi ya fito daga masallacin."

"Mutane suna ya bin sa a baya kamar sarki saboda yadda ake girmama a lokacin, yana da fara'a da yawan murmushi a ko yaushe, ga sadaka da ɗaukar baƙo tamkar ɗangida. Kai da ka gashi kaga asalin bafulata ni, yanayin jikin sa da kyau da Allah yayi masa kawai zaka kalla ka san wannan tsatson fulani ne. A lokacin ya manyanta amma in ka kalle shi sai ka kuma kallo saboda kamala da kyaun da yake dashi. Alhaji Muhmmad Jalingo attajirin mai kuɗi ne kuma babban malami, yana da dukiya mai tarin yawa a garin da ma wajen garin, ya tara dukiya da kuɗi na halak ga kuma ilimin addini da Allah ya bashi."

"Ganin ana girmama shi kuma ganin sa dadtijo da yazo gifta mu sai muma muka gaishe shi da girmamawar da ake yiwa masu furfura, Sai ya kalle mu bayan ya amsa gaisuwar yace amms dai baƙi ne ku, muka amsa da eh shigowar mu garin kenan bamu zan ko ina ba. Yayi murmushi yace mu ɗauko kayan mu biyo shi." Abba ya bisu da kallo bayan ya dakata da abinda yake faɗa ganin alamun gajiya a tare dasu da alama basa jin dadin labarin burin su kawai aje ga inda suke so.

Abba yace, "ina baku asalin labarin ne, daga nan zaku fahimci abinda yake faruwa." Ya sake cewa, "muka bi bayan sa kamar yadda yace zuwa gidan sa, ashe almajirai ne dashi sosai wnda yake koyarwa a cikin gidan sa, gidan tun a wancan lokacin babba sosai, yana da girma matuƙa soro-soro haka zaka dinga bi kafin ka shiga gidan. Aka sauke mu a wani ɗaki da ake saukar baƙi irin mu in mun je, ya kalle mu bayan ya saka an nuna mana ɗakin yana murmushi yace zaku iya zama a nan daga nan har zuwa lokacin da kuke so, zaku iya tambaya ta duk abinda ku ke so a duk sanda buƙatar hakan ya taso. Muka yi godiya sosai da addu'a ya amsa ya fita."

"Bayan mun yi wanka muna huta gajiya sai muka ji ana sallama daga bakin ƙofa ba tare da an shigo ba, jin muryar mace kuma yarinya sai kuma taso gabaɗaya muka fito bakin ƙofar, yarinyar da aka aiko gani da ƙwaryar damammiyar fura nono a hannun ta, bayan ta kuma wani yaro ne da akushi a rufe da kuma ruwa a kwanon sha. Har ƙasa ta ɗurkusa ta gaishe mu cikin harshen hausar ta wacce bata fita sosai,muka amsa da fara'a ta bamu abinda aka bata ta juya ta koma."

Abba ya kalli Bebi yace, "wannan wacce ta kawo mana abin shan itace Zahra mahaifiyar matar ka." Da sauri kowa yake kallon sa da mamaki Abba ya girgiza kai cikin son gamsar dasu tace, "ƙwarai kuwa itace. Bayan mun shiga ciki sai Ali yake cemin yarinyar nan da ta kawo mana fura akwai nutsuwa da kuma tarbiyya, gata da kyau. Nayi mamaki sosai saboda zama dashi na san shi mata ko kyaun su ko wani abun nasu baya gaban sa, shi kuɗi kawai ya sani, a kan kuɗi kuma zai iya aikata ko meye, yana da son kuɗi sosai yana kuma so yayi kuɗi ta ko wacce hanya ma in ya samu dama. Shiyasa nayi mamakin jin yana yabon mace wacce bata wuce ace mata yarinya a wannan lokacin ba."

"Tun daga wannan rana bamu sake ganin ta ba, kwanan mu biyar a gidan bamu sake ganin ta ba kuma kullum sai Ali yayi maganar ta. A zaman mu na kwana biyar mun je mun gaisa da iyalan gidan, a bakin almajiran gidan muka san matan Alhaji Muhammad huɗu ɗaya ta rasu saura uku, da kuma ƙwarƙwara guda biyu ɗaya ta rasu saura ɗaya. Kun san masu kuɗin da ko manyan malamai ko sarakai suna ajjiye ƙwarƙwara a gidan su har ta haihu, hakan ya samo asali tun daga kan annabawa na san kun san da hakan. Abinda muka ji wanda ya girgiza mu tun a lokacin, Kaf gidan sun tsani wannan ƙwarƙwarar saboda ta kasance tana da kyau sosai, kuma ta fisu yarinta sai ya zama har matan auren ta fisu fada a wajan Alhaji Muhammad, ma'ana yafi son ta akan mataan sa na aure. Mu kan mun shaida kyaun da take dashi a gani ɗaya da muka yi mata, a yadda muka ji labari in tazo shan ruwa a kwanon sha hancın ta sai ya taɓa ruwan saboda tsahon sa."

Ya kalle su yace, "Ita ƙwarƙwarar Alhajin wacce akace mana bayan rasuwar matar sa ya ƴanta ta ance kamar ruwa biyu ce, dan a hannun sarkin musulmi na sokkoto aka bashi ita amma asalin ta larabawan Sudan ne. Abinda zaka fahimta ita wacce ta kasance ƙwarƙwara duk da ancr ƴanta ta ta koma matar aure bata sakewa dasu, ware kanta take daban haka ma ƴar ta. Mutanen gidan basa son ta basa ƙaunar ta ita da yar ta, komai nasu iya su da taran su suke banda ita da ƴar ta. Haka muka bar gidan bayaan mun san labarin mutanen gidan musamman a bakin almajiran gidan. Abin mamakin Ali bai daina maganar wannan yarinyar da ko sunan ta bamu sani ba a wannan lokacin, haka muka rabu dashi yayi Kaduna nayi kano."

"Cikin ikon Allah dabbobin da muka saro daga Jalingo suka ƙare, mun ji daɗi sosai dan mun samu riba dasu hakan ya saka bamu yi ƙasa a guiwa ba muka sake komawa bayan wata biyu zuwan mu. Gidan muka sake komawa dan marigayi yace duk sanda muka zo muna da masauki a gidan sa. Muka yi masa tsaraba a hanya muka kai masa dan yaji daɗi, ai kam yaji daɗi sosai ya kuma nuna mana hakan ta hanyar yi mana addu'a. Muka cigaba da zama muna fita muna siyan abinda zamu siya har lokacin bamu sake ganin wannan yarinyar ba sai da muka kwana biyu muka haɗu da ita a soron gidan ta dawo daga makarantar islamiyya. Ta gaishe mu ta wuce ciki Ali ya cigaba da kallon ta har sai da na riƙe shi, Sai yake cewa shi kam kawai yarinyar ta shiga ransa ne sosai."

"A wannan zuwan muka san sunan ta Zahra mun ji mahaifiyar ta na kiran ta dashi. Mu ka sake dawowa gida muka cigaba da harkokin mu, in dai muka yi waya da Ali ta landline ko na tura masa saqo zai min maganar Zahra har na gaji nace kaje a baka ita mana, yayi dariya yace tafi ƙarfina nida nake da aure dan ma yaran nawa suna komawa ga Allah, Bamu sake komawa Jalingo ba sai da aka kusa shekara sannan muka je."

Abba ya sauke numfashi yace, "a wannan zuwan mun yi baƙin zuwa domin mun je mun tarar da matar Muhammad Jalingo ko nace ƙwarƙwarar sa mahaifiyar Zahra kenan Allah yayi mata rasuwa. Mun ji rasuwar ta sosai duk da ba sabawa muka yi ba, nan muka yi musu gaisuwa har ita kanta Zahra dan ita za'a yiwa gaisuwa sai mahaifin ta. Da tausayin ta muka yi kwanakin da zamu yi muka bayan ɓun fahimci irin kular da take samu daga mahaifinta saboda rashin idon mahaifiyar ta, ya san yadda mutanen basa son ta. Sai da muka kammala komai na mu sannan muka sake dawowa Kano."

Kowa na falon kallon sa yake yi a lokacin Abba yace, "Wallahi naji rasuwar mahaifiyar Zahra a wannan lokacin kamar mun saba da ita, kwata-kwata sau biyu kawai na ganta amma sai naji mutuwar ta a jikina sosai. Abinda ya saka na sake jin rasuwar ta saboda ita Zahra, yaram gidan kaf basa ƙaunar ta sai guda ɗaya wata Halima. Rashin mahaifiyar ta babban rashi ne a rayuwar ta, duk da mahaifin ta yana da rai amma ba kamar uwar ba."

"Haka muka dawo kowa ya koma ga iyalan sa kowa zuciyar sa cike da tausayin Zahra."
Chapter 11 · 0% Book details