← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 84

Sashe 15

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi mai sauti yaja numfashi yace, "babu wacce na kalla, ni da nake da ke wacce mace ce zata burge ni har na kalle ta?." Ta ɗago ta kalle shi tcae, "to na san an kalle ka ai ko?."
"Sosai ma, da yake na shiga asibiti kafin nazo nan, harda wacce ta bani number ta tafe don Allah na kira ta." Ta wara ido tace, "kuma zaka kira?."
Shima ya wara ido kamar yadda tayi yace, "Da gudu ma, daman ina cikin kewa in na kira sai mu yi hira."

Kawai ta tashe da kuka tana cewa, "Allah ya isa in ka kira ta, Allah bazai yafe ba kuma itama bazan yafe mata ba. don Allah kar ka kira,Kayi min rai kar abin yayi min yawa." Kuka take amma cikin faɗa take maganar, yayi dariya ya sake matse ta a jikin sa ya riƙe ta gam-gam yace, "shiii wasa nake miki, babu wata mace da zata ga fuskar da zata bani number ta a wajena. Kin manta waye mijin ki ne?."

Ta sake ƙamƙame shi tace, "ban manta ba, amma don Allah kar ka kula su nasan akwai masu son ka sosai."
"To naji, ki daina kuka sarkin kuka."

"Wai Manal baza ku fito bane an...." Tsayawa maganar Mubeena tayi ganin su ma rungume da juna sun barta a tsaye a waje ga shashasha marw abin yi.

Haushi suka bata ta ja dogon tsaki ta bar wajan, jin hakan sai Manal ta bar jikin sa tace, "mun bar Yaya Mubeena ita kaɗai har tazo ta gan mu a haka."
"Laifin ki ne" ya faɗa yana yafa mata mayafin da yake ajjiye a gefen, ta tsaka takalmi suka fito.

A tsaye ya hango Mubeena girgiza kai tana gefe bata ce musu komai ba, ya saka Manal a motar ya kalle ta yace, "Yaya muje ko?." A fusace ta juyo ta kalle shi, har zata yi magana sai ta fasa ta shiga motar shima ya shiga suka tafi.

BDƘB3P09

Suna shiga gidan kasancewar safiya ce Mama da Baba suna zaune a inda suka saba zama wato ƙasan bishiya suka shiga d asallama. Kafin Mama tayi magana Mubeena tace, "kai nayi mantuwa" ta faɗa tana fita da sauri.

Baba ya kalli Manal da ta ƙarasa ta zauna yace, "Fatima jiki yayi sauƙi? Yanzu muke shirin zuwa sai ga ku." Manal tace, "Naji sauƙi sosai Baba, ina kwana."
"Lafiya lau, ya jikin naki?."
"Sa sauƙi" ta kalli Mama tace, "Mama ina kwana."

Mama tace, "lafiya lau, ya jikin naki?." Ta amsa sai ga Mubeena ta shigo Mama ta kalle ta tace, "kin samu mai adaidaita sahun?."
"Da yake a mota muke, mijin ta ne ya dawo damu" Mubeena ta faɗa da biyu dan tana so Mama ta san suna son junan su sosai. Bata ce komai ba Manal ta tashi jiki a sanyaye ta wuce ciki Mubeena ta wuce itama.

Baba ya kalli Mama yace, "Fatima don Allah ki bar yarinyar nan ta koma gidan mijin ta, meye na wannan abubuwa da kike yi ne? Meye amfanin raba su?. So kike ta dawo ta cigaba da zama tare dake bayan kun rabu ta tafi gidan mijin ta?, zaman gidan mijin ta ba shine darajar ta a duniya ba?. Meyasa kika kasa yafewa ne? Naji an yi miki laifi, amma shi Adnan ɗin meye laifin sa? Lokacin da abin ya faru ko da an haife shi yaro ne, to meyasa laifin Baban sa zai shafe shi?."

Mama bata ce komai ba tayi shiru yace, "tunda kin nuna min ba matsayin uban nake a wajan su Manal ba, ina roƙon ki ki barta ta koma. Tana son mijin ta mijin ta yana sonta, in kika raba su samun irin sa wahala zai baki, kinga kin cutar da ita kin kuma cutar da kan ki da abinda yake cikin ta."

Mama tace, "matsayin uban ka ke a wajan Manal wallahi."
"Wallahi ba haka nake ba, dan inda ni na haife su da bazan ce ki barta ta koma ki ƙi ji ba, inda ni na haife su bazan tsaya jiran umarnin ki ba, zan yanke hukunci ne kawai tunda kema a ƙarƙashina kike. Sunan Baba kawai nake amsawa a wajan su amma ba mahaifin ba shiyasa kika nuna min iyakata a kan su. Ko gudun bakin mutane bakya yi, auren da kwata-kwata bai wuce wata biyar ba ace yarinyar ki ta dawo gida?, ko ina zancen ake yi barin cikin gidana da kin san basa son Manal basa son ki. Amma ke hakan bai dame ki ba, tunda a wajan ki daidai ne shikenan."

Mama ta kulle ido ta buɗe tace, "raba ni da dukiya ta da suka yi wannan bai dame bi ba, wulaƙanta ni suka yi da ni da yarana suka barni a titi an kore ni daga gidan haya. Ruwa a kaina yake ƙarewa da Manal da Mubeena saboda bani da inda zan je. In  ba dan rayuwar baya ba irin ta yanzu bace da a lokacin wani abun ya same ni, ko a sace ni ko a sace ƴaƴana. Bani da komai sai kayana da kuma kayan yara na. Waye ya taimake ni a garin Zaria in ba kai ba? Su kaɗai na sani a Zaria ina zanje? Zan komawa ƴan uwana ne a lokacin..? Bazai yu ba" ta faɗa hawaye na sakko mata daga idon ta.

"Ƴan uwana na jini sune suka aurar dani a gare shi saboda kawai basa sona basa son mahaifiyata, ba bincike babu komai haka aka bashi ni ya tafi dani inda basu sani ba. Su kuma suka ci amanar halaccin da maahifina yayi musu, suka zalunce ni suka wulaƙanta ni basu yi tunanin maraicina ba. Ko da yake yake ƴan uwana ma suka rabu dani balle su?."

Baba yace, "wannan ya wuce Zahra ya kamata ki manta."
"Wallahi bai wuce ba, ina jin zafi da raɗaɗi a zuciyata. A lokacin da na haifi Manal ko shekara ashirin ban yi ba a duniya, basa tunanin akwai yarinta a tare dani suka barni a inda babu wanda na sani?. Taya zan so jinin Mu'azzam da Ali? Har abada."

Mama ta sake cewa, "in ba dan kai ba da yanzu ina ina? Wataƙila na mutu har su Manal ɗin. Amma kai ka taimake ni ba tare da ka san ni ba, ka taimake ni har ka dawo dani nan wajan mahaifiyar ka nake zaune tamkar mahaifiyata, ta umarce ka da aurena baka ƙi ba ka aure ni ka riƙr min yara kamar wanda ka haifa. Kai akwai hisabi ranar lahira, tsakanina da ƴan uwana sai Allah yayi mana hisabi, akwai kallo a ƙiyama" ta faɗa tana goge idanun ta.

Baba ya murmusa yace, "Hisabi tsakanin ki da Ali da Mu'azzam kika ce ba tsakanin ki da Adnan ba, laifin su bai kamata ace ya shafi Adnan da Manal ba. Raba su ba mafita bace lalacewa ce domin kuwa zaki musu illa dukkan su musamman ita Manal ɗin da ta kasance mace, in kika yi tunani zaki gane Manal bata cancanci haka daga wajan ki ba. Manal ta bar burin ta na son karatun dafa abinci saboda ke, saboda baza ta iya tafiya ta barki ke kaɗai ba a lokacin bakya gani ta haƙuraa ta zauna. Manal ta saudaukar da komai saboda ke Zahra, kar ki saka ta sadaukar miki da farin cikin ta a wannan lokacin don Allah. Nasan zata iya barin mijin nata saboda abinda kike so shi take so amma bai kai zuciyar ta ba, zata dinga ɓoyewa a zuciyar ta saboda kar ki gane bata ji daɗi ba har hakan yazo ya zamar mata babar illa. Ko ta samu ciwo ko wani abun ya faru, kinga ke kika jawo saboda baza  ta iya ce miki a'a ba. Wannan soyayyar ya kamata ki duba, shi kansa Adnan ɗin babu abinda ya haɗa ki dashi sai alkhairi. Ta silar sa kike gani a yanzu har kika gane mahaifin nasa da taimakon sa na samuwar ganin ki, ta silar sa lafiyar ki ta inganta har aka zo wannan mataki, bai cancanci wannan hukunci ko nace sakayyar daga wajan ki ba."

Baba ya sauke tausasa murya yace, "Kin ce saboda shi kin yafewa mahaifin sa ko?." Ta girgiza kai alamun eh yace, "to ki bashi matar sa, yana buƙatar hakan daga gare ki dan babu yadda zai yi miki ne, in kika ganshi yanzu sai kin tausaya masa saboda damuwar rashin ta. Abin alfaharin ki ne ace ƴar ki ta samu mijin da yake son ta har haka, abin alfahari ne ƴar ki ta samu miji mai nagarta kamar Adnan." Mama ta katse shi tace, "amma ba abin alfahari bane zama sirikar Mu'azzam, wallahi ba abin alfahari bane a wajena."

"Mantawa zaki yi da wannan ki kawar da kai kamar komai bai faru ba, sun so ki wulaƙanta amma Allah bai wulaƙanta ki ba. Duk dukiyar da suka kwashe basu kwashe duka ba sun bar ragowa basu sani ba, gashi da ita kika yiwa ƴar ki komai duk da haka basu ƙare ba. Kuma shi yace wallahi ko sisi bai ci a kuɗin nan ba, in ma ƙarya yake yi tunda yace wallahi yaci mu yarda, rantsuwar sa shi zata cutar bamu ba."

Baba ya kuma cewa, "indai na isa da Manal kamar yadda kika ce ina so yau ta koma gidan ta." Mama ta girgiza kai tace, "shikenan."
"Amma ina so ta koma saboda ra'ayin ki ba don bakya ra'ayi ba. Sannan bana so canjin fuska ya maye gurbin fara'a tsakanin ki da Adnan, komai ya wuce don Allah."

Mama tace, "ka wuce ka nemi abu ban maka ba, babu komai wallahi ya wuce. Ko yanzu ka kira Adnan ya tafi da Manal har zuciyata ya wuce."

Baba yayi murmushi yace, "Alhamdulillah! Na gode na kuma na ji daɗi hakan. Allah yayi albarka ya warware mana dukkan matsalar mu." Ta amsa da amin kafin ta miƙe tsaye tace, "bara naje yau na sanar da su Manal wacece mahaifiyar su." Baba cikin jin daɗi yace, "da kin kyauta kuwa, abinda suka jima suna so su ji kenan." Mama tayi murmushi ta wuce zuwa ciki.
Chapter 15 · 0% Book details