Sashe 24
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, "to bara naje naji" ta faɗa tana tashi ta shiga kitchen ta haɗa kunu flasks sannan ta fito ta fita. Da sallama ta shiga falon Abban ya amsa yana kallon ta ta ajjiye abinda tazo dashi ta zauna kusa dashi tace, "Alhaji ga kunun gyaɗa kai ne mai son sa" ta faɗa tana zuba masa a kofi ta bashi ya karɓa yace, "ai kam na gode."
Sai da ta bari ya sha rabin kofin sannan tace, "don Allah me yake damun ka? Damu da yaran ka mun shiga damuwar wannan chanjin naka, ka sanar damu damuwar ka ko zamu iya maka magani, in kuma baza mu iya ba sai mu taya ka addu'a."
Abba ya ajjiye kofin a kan center table ya kalle ta yayi shiru baice komai ba tace, "ko dai maganar babar su Manal ɗin ce har yanzu? Akwai wani abun ne bayan abinda ka faɗa mana?." Ya girgiza kai ya ce, "wallahi abinda na faɗa muku shine iyakacin abinda ya faru kenan, bayan wannan babu abinda ya faru." Mama ta tausasa murya tace, "meye silar damuwar ka?."
"Hauwa abinda yake damuna jin sa bazai miki daɗi ba, zai ƙara miki damuwa ne a zuciyar ki, gwara kar ki ji dan jin sa bazai miki daɗi ba." Mama tace, "ina so na sani indai har zaka faɗa ɗin."
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "kawai Allah ne yake hukunta ni tun a duniya kafin naje gare shi, na aikata laifuka masu yawa sosai, na saɓawa Allah ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, ni kaina bazan ce ga sau adadi ba. Gashi Allah yana hukunta ni tun a duniya, duk da nayi nadama da zuciyata da gangar jikina, na kuma tuba amma duk da haka sai na girbi abinda na shuka. Ki duba sau biyu ana zuwa auren Lubna amma da nace an taɓa mata fyaɗe ba a sake dawowa, shiyasa ko Bebi ban bari ya sani ba saboda zai fi ni shiga damuwa saboda ni na haife su amma yadda yake ni damuwa dasu zai fi ni shiga tashin hankali. Ga Maryam ma, yanzu duk wanda yaji ta taɓa yin ciki da tsohon mijin ta don Allah zai aure ta?."
Mama ta girgiza kai tace, "auren zai wahala, amma za'a yi indai akwai rabon ta sake yi ɗin."
"To duka fa laifina ne Hauwa, duka ni na jawo musu da hannuna matsayina na uba a gare su, da na zauna a gida kamar sauran iyaye da yanzu hakan bata faru ba. Da ace bana bin yaran wasu a waje nima da ba'a bi nawa yaran ba. Maganar ki gaskiya ce na fifita na waje akan ku, Hakan ne kuma maganar ki gaskiyar ce, a duk sanda nace muku zan yi tafiya wallahi Hauwa wani lokacin ina cikin garin Kano cikin ɗaya daga cikim gidajena, ina ciki tare da ƴan mata in wannan tazo wannan ta tafi" ya faɗa hawayen yana sakkowa daga idanun sa.
Gaban Mama ta faɗi ganin hawaye a idanun mijin ta, duk wani haushin ko takaicin sa da take ji a zuciyar ta sai taji babu shi, duk da yana faɗa mata abinda yake aikatawa ne amma sai taji rauni ya mamaye mata zuciya ta kalle shi tace, "Hawaye fa ka ke yi."
Ya shafi hawayen fuskar ta sa yana kalla ya ce, "na yi shi yafi sau babu adadi, daga maganar da kika faɗa min bayan abinda ya faru da Maryam hankalina ya dawo jikina. Bayan nan na fita ranar juma'a huɗubar da akayi a ranar akan zina ne, gabaɗaya abinda kika faɗa gaskiya ne wani abun ma kin rage baki faɗa ba. Ina killace nawa a gida ina ganin babu abinda zai same su, ban san da cewa alƙhawari ne duk wanda yayi zina da ƴar wani sai anyi da ta ko da da mai gadin gidan sa ne. A ranar naji illolin ta da kuma tsantsar haramcin da yake tartare da ita. Hauwa a ranar naji koda ka shekara ɗari a duniya kana aikin alkhairi zinar kwana bakwai sai ta rinjayi wannan aikin alkhairin. Bayan na dawo gida na dinga turawa manyan malaman da na sani message akan illar zina amma abun da naji shi aje sake maimaita min, yadda wani zai faɗi azabar da Allah ya tanadarwa masu aikatawa tafi ta wani malamin zafi. Daga lokacin na fara gani ni na cuci Maryam da Lubna, basu da laifin komai laifina ne, dole sai hakan ya faru dasu saboda nima na yiwa yaran wasu."
Kuka Abba yake yi mara sauti mai nuni da nadama ƙarara a tare dashi ya ce, "ina zan kai wannan zunubin Hauwa? In wani abun ya sake tsallakowa ya same ku ya zanyi?. Ban san adadin matan da aka kawo min ba, wasu suka kawo kansu wasu kuma ni na nemo su. da yawan lokaci indai a Abuja ne ban cika mu'amala da karuwa ba, Hauwa sabuwa ake ɗauko min wacce ni zan fara sanin ta, wata daga wannan lokacin bazan sake ganin ta ba wata kuma zata yi kwana biyu daga nan na sallame ta saboda haka tasarına yake. Wasu kuma neman taimako ne zai kawo su gare ni, da zarar sun yi min bazan taimaka musu ba sai sun bani kan su, wasu su amince wasu su faɗa min baƙaƙen maganganu su tafi. Amma daga baya na daina neman masu son taimako a wajena saboda gudun tonan asiri na. Wallahi Hauwa wasu matan ma ni ne silar shigar su bariki, na san Allah bai gama hukunta ni ba akwai wani abun da zai same ni yanzu ko nan gaba" ya faɗa yana kuka mai ƙuna.
Ita kanta Maman kuka take yi sosai jin abinda bata taɓa ji ba, ta san mijin ta yana neman mata amma bata san abin nasa yayi yace tsanani haka ba. Cikin muryar kuka ya ce, "Ina zan kai wannan zunubin nawa Hauwa? Ina zan kai wannan tashin hankalin da na saka kaina a ciki?. Ina dake ina da Jamila amma na ke tsallake ku na tafi wajan na banza, wallahi duk nishaɗin da zaka samu a wajan karuwa bai kai rabin na wajan matar ka ba, amma mun ajjiye wannan sanin saboda shaiɗan da kuma son zuciya."
Mama kuka take yi mai sauti dan abin ya shige ta sosai hankalin ta ya tashi bata da mafita sai kukan. Abba ya ce, "to ba dole na shiga damuwa ba? Ba dole na shiga tashin hankali ba?, ba dole ku rasa abinda yake damuna ba?. Hauwa ba dole na zama haka ba?. Anya bazan kai kaina kotu a yanke min hukuncin da addini ya tanadarwa irin mu ba?." Bata ce komai ba sai kukan da take yi sosai kafin ta tsayar da kukan tana jan numfashi tace, "ka gode Allah ka fahimci hakan tun kana da rai ka kuma nemi tuba daga wajan Allah, Allah ya so ka da rahama da ya saka ka gane laifin ka yanzu kafin ka koma gare shi."
Ya kalle ta ya ce, "Lokaci ya ƙure min Hauwa, na fi shekara goma a bariki, raina ba a hannuna yake ba, amma na san bazan kai shekara biyar masu zuwa da rai ba. Laifin da aka aikata a cikin shekaru sama da goma kina ganin a cikin sauran numfashin da ya rage min har ya ishe ni na tuba?."
"Allah mai yafiya ne a ko yaushe, indai ka tsarkake zuciyar ka kar ka fitar da ran a yanzu ma ya yafe maka."
Yayi murmushi ya ce, "su kuma yaran fa? Zasu yafe min?." Mama tayi shiru bata ce komai ba Abba ya ce, "na cutar da ku, ku yi haƙuri na cuce ku na tabbatar da ko haƙƙim ku bazai bar ni ba." Mama kuka take yi shima kuka yake yi, itace take iya rarrashin sa dan kukan da yake yi ne ne yake karya mata zuciya, duk da duk abinda ya faɗa gaskiya ne amma ganin hawayen sa babban tashin hankali ne a wajan ta dan bata taɓa gani ba, ko iyayen sa da suka rasu bata ga hawayen sa ba.
"Allah ya so ka da rahama da ya haka ikon tuna a yanzu, indai ka tabbatar ka daina kayi nadama Allah zai yafe maka."
"Wallahi na daina Hauwa, na daina aikata komai Hauwa, komai ya gama fita daga raina, a yanzu babu abinda nake hange sai lahira ta Hauwa."
Mama tace, "Allah zai amsa, in sha Allah zai yafe maka ka cigaba da addu'a. Indai ka daina shikenan Allah yana kallo." Ya girgiza kai ya saka tissue ya goge idanun sa yayi shiru bai ce komai ba amma shi kaɗai yasa abinda yake ji a zuciyar sa.
Mama ta goge idon tace, "ina zuwa." Ta faɗa tana tashi ta fita.
Kamar yadda tayi zato Bebi jiran ta yake yi yana ganin shigar ta ya taso yana kallon ta ganin alamun kuka tayi sosai ya ce, "Mummy lafiya?."
"Babu komai, kaje gida dare yayi ka bar mai tsohon ciki a gida."
"Mummy ga alamun kuka ina gani a tare dake kice min babu komai, me ya faru don Allah?."
Mama tace, "babu komai nace maka, ka tafi gida kuma yanzun nan kar na dawo na tarar da kai" ta faɗa tana sake fita ta koma ɓangaren Abban.
Tana shigata zauna tace, "Bebi ne ya damu, shi naje nace ya tafi gida saboda ya bar matar sa a gida ga tsohon ciki." Abba ya kulle ido ya buɗe tare da sauke ajiyar zuciya, yana son faɗa mata abinda ya haɗa su da Mubeena amma ya kasa saboda nauyin abin yake ji shi kansa.
Waya aka yi masa ya saka hannu ya ɗauka ya saka a kunne, salati kawai Mama tajj yana yi kafin ya yanke wayar jikin sa har rawa yake yi. Mama hankalin ta ya tashi tace, "me ya faru kuma?." Abba ya ce, "company na na Lagos shine yake gobara."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Garin ya hakan ta kasance?."