Sashe 58
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mummy ce ta buɗe ƙofar ta shigo ɗakin hakan ya saka ya kalle ta, ganin kallon da take yi masa ya saka gaban sa ya faɗi sosai , Mama ta kalli Rumana ganin da hawaye a fuskar ta kalle shi tace, "Ka tashi ka fita daga ɗakin nan yanzu."
Rumana ta kalli Mama gani yadda ranta yake a ɓace sai tayi murmushi tace, "Mummy babu komai fa, hira kawai muje yi nida shi ba wani abun da kike tunani bane." Hararar sa tayi sai ya tashi tsaye a lokacin wayar sa take ƙara bai duba ba ya wuce ya fita.
BDƘB3P35
Bebi ko da ya fita bai ɗauko wayar daga aljihu ba da yayi sallah ya fito daga masallaci ya ɗauko wayar yana dubawa, ganin sunan Mubeena sai gaban sa ya faɗi matuƙa, hankalin sa ya dawo jikin sa akan Manal, da hanzari ya sake kiran number ta amma bata shiga ya dafe kai yace, “na shiga uku, ina yarinyar nan ta shiga ne?” Ya faɗa gaban sa yana faɗuwa sosai.
Mubeena ce ta sake kira ganin kiran ta yana shigowa ya daure ya amsa da sallama ta amsa tace, “ina yini.”
“Lafiya lau, ya Mama? Ina fatan tana lafiya.”
“Tana nan lafiya. Don Allah ina Manal? Tun jiya nake neman number ta bata shiga na yi mata magana ta WhatsApp duk a banza.”
A hanzari ya wara idanun sa waje gaban sa ya faɗi sosai har sai da ya dafe ƙirji yace, “bata zo gidan ba?.” Mubeena tace, “rabon Manal da zuwa nan ai ta kwana biyu, bata zo ba kuma Mama ce take son magana da ita shiyasa ma ba kira ka. Don Allah in ka koma gida tana nan ka haɗa ni da ita.” Hankalin sa ya tashi tsoro ya mamaye masa zuciyar sa daƙyar tace, “to in sha Allah, ki gaida Mama.” Ta amsa tana kashe wayar.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Ina Manal taje?, Kenan bata gidan Mama?. Meysa ma na bari ta fita a daren nan?” Ya faɗa yana dafe kansa, da sauri ya nufi inda motar sa take zai shiga aai ga Kausar ta leƙo tace, “Yaya kazo in ji Mama.”
Motar ya kulle ya shiga gidan amma hankalin sa gabaɗaya baya jikin sa. Yana shiga falon ta bishi da kallo ita kanta taga kamar ba a nutse yake ba amma bata nuna masa ba ya zauna a kan carpet yace, “Mummy gani.” Ta kalle shi tace, “lafiya ka canja haka? Me ya faru?.”
“Babu komai Mummy, an kira ni daga asibitin ne kiran gaggawa shine zan je.”
“To kaje, daman ba wani abun bane akan maganin Rumana ne in akwai wanda zaka canja mata sai ka bata, dan kamar maganin da ka bata da farko yafi na wannan arnen likitan. Amma kaje sai ka tawo dashi.”
Kamar jira yake ya miƙe ya fita da sauri ya shiga mota ya bar unguwar. Tafiya yake yana tunani ina Manal taje tunda bata gidan Mama, hankalin sa gabaɗaya ya tashi, laifin kansa yake gani da ya bari ta fita bai bi bayan ta ya dawo da ita ko da a wuyan sa ba ne.
Tunawa da gidan Daddy Sai ya ɗauko waya hannu na rawa ya kira mahaifin Manal yana yi yana tuƙa motar, daga can ɓangaren Daddy ya ɗauka yace, “Adnan ya aikin?.”
“Lafiya lau Daddy, ya ƙarfin jikin?.”
“Alhamdulillah, ashe an sallami Rumana sa ɗazu da yaran suka je akace ai tana gidan ku.”
“Eh daddy, an sallame ta suna gida da Mama yanzu.”
“Allah ya ƙara lafiya, abin ne sai a hankali yazo a yadda ba a yi tunani ba, a yadda aka bamu labarin ta zata ji babu daɗi musamman in ta tunda da ta rasa ka har abada.”
Bebi yace, “haka ne, amma in sha Allah komai zai wuce” ya faɗa yana faka motar saboda baya cikin nustuwa gashi yana waya. Daddy yace, “haka ne kam, Allah ya daidaita komai ya haɗa kansu baki ɗaya.” Ya amsa da amin kafin yace, “Daman kira nayi mu gaisa.” Daddy yace, “Allah yayi albarka, a gaishe da Fatima duk da jiya mun gaisa a waya.” Bebi jin haka ya tabbatar da bata gidan ya amsa a sanyaye ya kashe wayar yana dukan sitiyarin motar.
“Ina taje? Tana ina har kwana huɗu?.” Bashi da mai bashi amsa ya sauke numfashi ya saka jan motar ya tafi
Hanyar gidan sa ya wuce ya faka motar a ƙofar gidan Adda Halima yana kallon gidan yana tunanin shiga, kamar wasa sai gata ta fito a mota da alama fita zata yi, Sai ya sauke glass ya fito daga motar ganin sai ta tsaya tana murmushi tace, “A’a Adnan kai ne.”
“Ni ne Mummy. Barka da dare.”
“Barka dai, ya gida dasu Manal?.” Jin haka nan ma sai yayi sak jikin sa yayi sanyi yace, “Lafiya lau Mummy, daman zan wuce ne nace bara na tsaya mu gaisa.”
Tayi dariya tace, “ai kam ka kyauta, gobe ko jibi ma zan zo gidan naku in sha Allah, zan mata sallama zan wuce Lagos.” Bebi yace, “Allah ya kaimu.”
“Amin. Gashi ka tarar zan fita ina ya sauri
“”Babu komai, Allah ya kiyaye” ta amsa tana dariya ta ɗaga glass ɗin sama ta ja motar ta tafi ya koma mota jiki a sanyaye sosai ya zauna.
Kiran Huzaifa ne ya shigo wayar sa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka ya saka a speaker Huzaifa yace, “Bebi gamu kusa da gidan ka nida Hamza, mu ƙaraso kana nan?.”
“Gani nan” ya faɗa yana kashe wayar ya ja motar ya tafi. ya ƙarasa bakin gate ɗin ya danna horn aka buɗe mota yana ajjiye motar suma suka shigo. Yana tsaye suka fito daga motar suka shiga gidan suna bin falon da kallo kana gani kasan babu nace a gidan, kofu nan tea da suke ajjiye akan table, ga plate ga bowl ga jakar ruwan da ta lemo.
Bebi yace, “sorry falon babu gyara.” Hamza yace, “indai wajan ajiyar irin wannan ne ka saba tun kana gida, daman a gajiye muje fa muka tsaya a nan mu kalli ball sannan kuma mu ci girmin ƙanwar mu.” Bebi ya kalle su ya zauna ya furzar da iska yana sake kiran wayar ta amma bata ɗauka.
Huzaifa ya kalla a sanyaye yace, “a cikin gidajen ƴan uwan ku don Allah Manal bata je ba?.” Huzaifa ya kalle shi ganin da gaske yake maganar yace, “kamar ya Manal bata je ba? Yau ko jiya?.” Bebi ya sauke numfashi yace, “tun ranar da abin nan ya faru da daddare, bata je gidan ku ba?.”
Huzaifa yace, “Manal bata je ba gaskiya, kuma bani da labarin taje gidan wasu ƴan uwan mu. Wai kana nufin tun ranar bata gidan nan?.” Ya ɗaga masa kai alamun eh kafin yace, “tun a daren ta fita da mota, nayi tunanin gidan Maman su taje dan nasan babu inda zata iya zuwa in ba’a nan ba, ɗazu Mubeena ta kira tana sanar dani Maman su ma tana son magana da ita ne.”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Kuma baka neme ta ba kai tun ranar Bebi?, Ka kira wayar ta? Meyasa ma ka bari ta fita a da daddare?” Huzaifa ya faɗa yana kallon sa. Bebi yace, “wannan shine kuskuren da na yi, don Allah baka san inda take ba?. Na Kira ta sau babu adadi amma ta saka wayar a dnd na rasa inda zan saka raina, na kira Daddy yadda yayi min magana ya tabbatar da Manal ba a gidan ku take kwana ba.”
Huzaifa ya kalli Hamza da ya saku baki yana kallon Adnan yace, “Hamza kaji fa, yanzu ace Manal ta fita da daddare baza ka tashi neman ta ba sai yau? Wannan wacce irin rayuwa ce? In wani abun ya same su ita da ɗan ta fa?.”
Bebi yace, “babu abinda zai same su don Allah kar ka sake hargitsa ni. A Daren ka san ina cikin ruɗani saboda abinda ya faru da yadda Mummy tayi min, kai kace na taso gida ma daga asibiti saboda na huta da damuwar da take damuna. Ina dawowa ta dinga min banzayen tanbayoyi kuma kun san yanayin da nake ciki in ina cikin bacın rai.”
Hamza yace, “Allah ya sa ba sakin ta kayi ba.” Ya kalli Hamza ya girgiza masa kai yace, “wacce irin magana ce wannan?.”
“Ɓacin rai da zai saka ta fita daga gidan nan ƙarshe sha ɗaya na dare ai ba ƙaramin abu bane, kaima a lokacin zaka iya furta ko wacce kalma ba tare da ka sani ba.”
Huzaifa yace, “kuma in ransa ya ɓaci zai iya furta hakan bai sani ba, ashe duk kulawar taka akan ƙannen ka kawai ta tsaya babu matar ka, dan na tabbatar da ace Kausar ce baza ka barta ta ita kaɗai da wannan daren ta fita ba, duk yadda zaka yi zaka dakatar da ita koda ta fita zaka dawo da ita. Amma ita ta fita yau kwana har huɗu baka neme ta ba sai yanzu da daddaren nan? Gaskiya ka bani mamaki wallahi, ban ɗauka kulawa da kishin naka akan ƴan uwan ka kawai ya tsaya ba.”
A fusace Bebi yace, “Huzaifa ya ishe ka, ina faɗa maka abinda yake damuna ne kawai saboda ka faɗa min inda take ba ka dinga yi min maganar banza ba, in ka sani ka faɗa min, in baka sani ba zan nemo inda take. Na faɗa maka na san nayi kuskure a kan hakan, kuma nayi dana sanin barin ta fita duk da raina ne a ɓace sosai.”
“Dole na faɗa maka domin haƙƙin nemo ta ba a kan ka ya tsaya kawai ba har dani, ina so na tuna maka Manal ƙanwata ce in wani abun ya faru da ita kai matar ka ya samu ni kuma ƙanwata ya samu, kowa yana da matsayin da yake kallon ta yana da kuma kalar damuwar da zai yi a kanta. Wallahi ka bani mamaki, nayi mamaki sosai, ban ɗauka hakan daga wajan ka zai zo, ban ɗauka zaka yi sakaci da rayuwar ta har haka ba.”