← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 84

Sashe 52

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya kalli Daddy yace, “kaji abinda tace, kaje dasu ta yafe.” Daddy ya girgiza kai yace, “A’a, bazan iya ɗauka na tafi dasu ba, yadda na ɗauko na dawo dasu sun bar wajena, duk kadarorin na siyar da asalin su amma duk na mayar dasu ga takardun su zan kuma zo muje da kai na nuna maka duk inda dukiyar take. Akwai company a lagos na shinkafa duk zamu je in Allah ya ara mana rai da lafiya ka.”

Mama ta kawar da kanta gefe bata ce komai ba Daddy ya miƙe tsaye ya kalle ta ya ce, “na gode da karamcin da aka yi min, na gode da aka yafe min ɗin da akayi. Huzaifa mu je” ya faɗa yana yin gaba Huzaifa ya biyo bayan sa suka fita daga gidan.

BDƘB3P31

Bayan fitar Daddy daga gidan su Manal Mama ta kalli Baba tace, “ka mayar masa da takardun sa bani da buƙatar su, kallon su yana tuna min da abubuwa da yawa dana manta a rayuwata. Don Allah ka mayar masa bana so yarana ma basa son dukiyar.” Baba yayi murmushi ya ɗauke takardun ya fita dasu ya adana a wajan sa da niyar zai mayar masa sai ya samu lokaci zai kai masa har gida. Tunda tace ta yafe ai shikenan shi gaba ta kai shi tunda dai dukiya maganar mai ita take ji.

Manal ta dawo daga school tana zaune a falo tana shan ruwa Ayan kuma yana cinyar ta yana shan nono. Lokacin yamma tayi magriba na gab da yi Bebi ya shigo falon da sallama yana kallon ta har lokacin damuwar jiya bata wani bar shi sosai ba, ta amsa sallamar tace, “sannu da dawowa.”

Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita ya yi mata kiss a goshi yana kallon Ayan da take shayar dashi idanun sa a kulle ya shafa gishin sa yace, “ya school ɗin?.”
“Alhamdulillah, sai yanzu na dawo.”

“Gaki nan a gajiye ai.” Manal ta zare Ayan ganin yayi bacci ta gyara rigar ta tace, “ko abinci ban maka ba, bara na tashi na dafa maka.” Ya buɗe ledar hannun sa yace, “kar ki damu, na tahp mana da abinci na san daman zaki jima a school.”

Kallon abincin tayi tace, “yau ba abincin mutuniyar ka bane ba kenan?.” Yayi murmushi kaɗan yace, “Mun yi magana da ita bata yi ba yau, amma kema kin san da nata zan kawo.” Ta kalle shi ta girgiza kai tace, “baka yi min kara wallahi.” Yayi dariya yaja kumatun ta yace, “ƴar lukuta mai kumatu” ya faɗa yana tashi ya shiga ciki ya barta a zaune.

Jin ana kiran sallah sai itama ta shiga ciki tayi sallah ta dawo falon ta ɗauki abincin ta kai microwaves tayi warming ɗin sa yayi zafi sosai ta fito dashi a lokacin ya dawo daga masallaci tace, “ga abincin.”

Zama yayi ta kawo abincin, kasancewar basmati rice ce ga kuma salad tare suka ci a plate ɗaya kamar yadda suka saba in suna shiri. Ya kalle ta yace, “sallar i’sha kawai nake jira ayi in shigo zan kulle gidan nan, babu inda zan sake zuwa sai gobe in sha Allah.” Manal ta kalle shi tace, “Meyasa?.” Ya kalle ta yace, “saboda yau zan kasnace da sabuwar amaryata ta wacce na kwana kusan hamsin ban kasnace da ita ba, ko nace na wuce kwana hamsin ma, saboda tunda cikin ya shiga wata tara shikenan kika fara guduna. Gaskiya na yi ƙoƙari sosaj wallahi, kusan wata biyu fa kenan?. Hmmm ki shirya wallahi, dan wata biyu bazai tafi a banza ba.”

Tayi murmushi kawai tace, “kai Baka jin kunyata wai?.”
“Ke kunyar tawa kije ji? Haka kika kalle ni kika ce nayi miki ciki.”
“Ai suɓutar baki nayi.”
“Ni kuma ba shi nayi ba ina sane na faɗa.” Tayi murmushi tace, “to nidai ba wata amarya a yau ɗin nan, kowa yayi ta kansa.”

“Wallahi baki isa ba, yau zan fanshe dararen da suka wuce ni. Dan haka yau ki ɗauka sabuwar amarya ce aka kawo min ke, ba tausayi ko ɗaga ƙafa wallahi.” tayi dariya kawai bata ce komai ba ta sukunyar da kai ƙasa, yayi dariya shima ya ɗauki wayar sa ganin ana yi masa waya. Tsaki yayi yace, “Huzaifa zai takura min.” Manal ta kalle shi zata yi magana ya dauƙi kiran ya saka a speaker yace, “sarkin takura ya aka yi?.”
“Kai da Yayar matar ka kake magana ya kamata ka dinga nustuwa.” Bebi ya kalle ta ganin tana murmushi sai yayi tsaki yace, “malam lafiya?.”
Huzaifa yace, “Da kai da Manal ake son gani yanzu a gidan ku.”

Bebi yace, “kamar ya ake son ganin mu? wani abun ya faru ne?.”
“To nima dai ban sani ba, an saka na kira ka na kuma kira kowa na gidan mu kowa yazo gidan ku za’a tattauna, ka taho da Manal za’a fara meeting daga nan zuwa bayan sallar i’sha.”

Bebi yace, “to Allah yasa lafiya.” Ya amsa da amin ya kashe wayar ya kalle ta yace, “to kin ji, sai ki shirya mu je.” Manal tace, “me kuma ya sake ya faruwa?.”
“Allah a’alam” ya faɗa yana shan ruwa ya tashi ya fita.

Sai da akayi sallar i’sha sannan suka fita zuwa gidan, lokacin da suka je an taru a falon Abba, abinda ya bashi mamaki ganin Rumana kuma da Maman ta da kuma yayyen Mama. Basu ce komai ba suka zauna Mubeena ma tana nan aka buɗe taro da addu’a kafin Daddy yace,

“Na san kun yi mamakin wannan jira na gaggawa a kuma wannan gidan a karo na biyu. To ikon Allah dai baya ƙarewa a ko yaushe, kuma abinda kayi kai ka manta shekaru da yawa watarana zai bayyana.”

Jin yayi shiru sai Abba yace, “magana ake akan Sumayya ƙanwar mahaifiyar Adnan, wacce mahaifin ku ya aura kafin mahaifiyar Manal. Auren bai wuce shekara ɗaya da wani abun ba ya mutu ba tare da wata damuwa ko matsala ba, ya bar garin kano ya koma asalin garin su Zaria bai san ita Sumayya tana da ciki ba. Har ta haihu yarinya ta girma da komai bai sani ba dan shi har suka rabu bai san akwai ciki ba. Sai ɗazu da yazo ya same ni akan yana so yaje gidan su domin ya nemi afuwar ta haka kawai ya rabu da ita babu dalili, nan yake sanar dani sunan mahaifin ta nace ai sunan mahaifin babar su Adnan ne, ana haka sai ga su sun shigo duba ni a nan ya ganta ta gane shi shima ya gane ta.”

Maman su Huzaifa ce kawai tace, “kuma dai?.” Abba yace, “ƙaddarar kenan ai. Yanzu duk mun kira ku ne dan mu nuna muku ƴar uwar ku gata” Abba ya faɗa yana nuna Rumana da fuskar ta tayi ja alamun ta sha kuka sosai.

A tare kowa ya kalle ta da mamaki sosai da kuma al’jabi, Bebi ya sake kallon Rumana ya kalli Ammi ya sake kallon Manal ya sake kallon Rumana cikin ruɗani. Abba yace, “itama jinin ku ce mahaifin ku ɗaya, duk Allah bai yi nufin za’a san wanna ba tun a baya saboda Alhaji Ali bai taɓa zuwa mun haɗu dashi ba, duk alaƙar Adnan da Huzaifa sai dai mu yi waya amma bai taɓa ganina ba nima ban gan shi ba. Silar rashin lafiya da kuma silar haihuwar Manal ya saka shi yazo ashe duk rabon wannan abubuwan da aka binne ne zasu bayyana.”

Huzaifa ya kalli Abba yace, “Abba kenan itama Rumana ƙanwata ce kamar Manal da Mubeena?.” Abba ya girgiza kai yace, “ƙwarai kuwa, ƙanwar kace itama jinin mahaifin kace.” Huzaifa ya kalli Rumana ya kalli Manal ya kuma kalli Bebi da shima shi yake kallo kafin tace, “ikon Allah.”

Abba yace, “daman shine dalilin kiran kowa ya san ƴar uwar sa saboda halin rai, kar lokaci yayi halin sa ba tare da an nuna ta a gare ku ba.” Maman su Huzaifa ta kalli Daddy tace, “bayan ita babu wata?.” Daddy ya kalle ta yace, “babu, babu wata matar da na aura a duniya iya wannan ukun ne kawai. Na san baki san da Sumayya ba amma ita ta san dake, kamar yadda ya faru a ɓangaren Zahra.” Mama ta kawar da kai gefe tana sake kallon Daddy ɗin tana girgiza kai.

Alhaji Mustapha yace, “shine daman maganar kowa ya san da juna kafin rai yayi halin sa. Manal, Mubeena, Rumana duk Alhaji Aliyu ne ya haife su kuma duka ƙannen ka ne Huzaifa. Shine abinda aka tara ku asanar daku daman.”

Bebi da ya kasa magana sai a lokacin ya kalli Abban su daƙyar yace, “kenan da Manal da Ruman mahaifin su ɗaya ne?.” Abba ya girgiza masa kai alamun haka ne, da sauri ya kalli Mumny da take kallon sa ya sake kallon Rumana da ita shi take kallo zuciyar sa na bugawa sosai.

Mummy ta kalli Abba da Daddy tace, “Rumana ta kasance a hannuna tun daga yaye har ta girma ta kai minzalin aure a wajena take. Sun shaƙu da Adnan sosai, kasancewar tare suka tashi in ya girme ma bai shekara uku zai bata, kuma girman mace da namiji sai ya zama duk tare suka tashi gabaɗaya har ita Farida ɗin kusan a cikin su take. Shaƙuwar Adnan da Rumana har ta niye ta koma soyayya tunda suka yi hankali suka tabbatar da babu alaƙar ta jini a tsakanin su, kuma ban shayar da ita ba balle ya zama babu aure a tsakanin su ya fara son ta ta fara son sa. Babu wanda bai yi tunanin Rumana ba Adnan zata aure ba, duk da baya nan ya tafi karatu ba amma shaƙuwat su bata taɓa yin baya ba a kullum ƙaruwa take. Yana karatu a wata ƙasar tana karatu a nan har ya kammala digester ɗin sa na farko, ya dawo a lokacin har an fara tunanin zai aure ta ne sai ƙaddarar zata yi aure ta gifta a tsakanin su, a lokacin Rumana ta nuna akwai wanda zata aura ba Adnan ba.”
Chapter 52 · 0% Book details