← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 84

Sashe 6

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hamza ya zagaya inda yake ya dafa shi yace, "Kwana biyu yawan shiga damuwar nan taka tayi yawa, me yake faruwa ne Bebi?." Bai ɗago ba bai kuma ce komai ba Huzaifa yace, "ka sanar damu in zamu iya taimaka maka mu taimaka, in baza mu iya ba sai mu yi maka addu'a. Amma bama jin daɗin ganin ka a wannan hali ko kaɗan."

Ɗago kai yayi ya jingina da kujerar da yake kai yace, "abubuwan da suke damuna suna da yawa."
"Faɗa mana mu ji, Muna da lokacin sauraren ka" Hamza ya faɗa yana kallon sa. Bebi ya sauke numfashi yace, "zan faɗa muku amma ba yanzu ba, in na faɗa yanzu sake dagula min lissafi zai yi."

Huzaifa yace, "Shikenan, Allah ya kawo maka mafita."
"Amin na gode, ku taya ni addua allah yasa kar abinda nake tunani ya tabbata. In hakan ya tabbata Allah zaku iya rasa ni gabaɗaya, bana tunanin zuciyata zata iya ɗaukar abinda nake hasashe, bazan iya ɗauka ba, bazan iya ba" ya faɗa yana sake jefa kansa cikin damuwa mai tsanani.

Hamza ya kalli Huzaifa shima shi yake kallo kafin ya sake kallon Bebin yace, "to baka faɗa mana ba balle mu san abinda zamu ce maka a kai." Bebi ya kalle su yace, "kar ku damu."
"Yanzu har abin ya kai ka fara ɓoye mana damuwar ka? Haka kayi mana wancan lokacin yanzu ma gashi ka ɓoye, a ganina babu abinda muke ɓoyewa junan mu saboda mu zama tamkar jini ɗaya" Huzaifa ya faɗa yana kallon sa.

Bebi ya kulle ido bai ce komai ba ganin haka sai suka bashi waje dan ya huta. Ya jima a wannan yanayi sallah ce kawai take tayar dashi, ya kira Manal yafi a irga amma bata ɗauka hakan ya saka saka shi a damuwa matuƙa dan bai san a wanne hali take ba.

Sai gab da magriba ya koma gida shi da Maryam da Lubna suka shiga cikin gidan shi kuma ya shiga wajan Mama. Tana kallon sa tace, "Subahanallahi! Bebi kaga yadda ka koma?, Anya kaci abinci yau?." Zama yayi baice komai ba ta kalli Kausar tace, "kawo masa abinci yaci." Ya kalli Mama yace, "bana jin yunwa bazan iya cin komai ba, Abba yana nan?."

Mama tace, "Yana nan. Amma kaci wani abun Adnan ka faɗa lokaci ɗaya."
"Zan ci sai anjima." Mimi ce ta fito daga ɗaki ta kalle shi ta kalli Mama tace, "Mama bashi da lafiya?." Kallon ta yayi ya kalli Kausar ya tashi tsaye yace, "in anyi sallah ina neman ku, ku kira Lubna ina san magana daku" yana faɗa yana fita.

Mama ta girgiza kai tace, "Allah ya kawo mafita a lamarin nan, in Bebi ya rasa Manal zai iya samu matsala. Allah kar ka tabbatar da abinda zuciyar mu take hasashe, ya Allah kar ka saka Manal da Adnan su kasance mahaifin su ɗaya, Allah kar ka rubuta wannan ƙaddarar a shafin ƙaddarorin sa, Allah ka canja ta da mafi alkhairi."
Duk sai a lokacin su Kausar suka gane abinda yake damun sa, suka yi shiru kawai su kansu maganar ta shige su balle kuma shi.

Kamar yadda yace bayan magriba suka je ɗakin sa wanda a yanzu babu wanda yake zama a ciki duk yayi ƙura. Da sallama suka shiga yana tsaye yana kallon window ya amsa yana kallon su. Sai da suka shigo dukkan su sannan yace, "ba sai kun zauna ba wajan akwai ƙura sosai. nasiha nake so nayi muku wacce nake fatan zata shiga jikin ku har girman ku. Ko yanzu ko nan gaba kar ku amince soyayya ta ɗauki hankalin ku har tayi nasara a kan ku wajan ɗaukar hotunan tsaraicin ku turawa miji ko saurayi."

Kallon su yayi yana karantar yanyin su yace, "ban ce turawa miji ya zama kamar haramci ba, Amma shawarar da nake baku matsayina na jinin ku har mijin kar ku turawa, kar kuma ayi video call ana nuna tsairaici domin shima za'a iya recording. Masoyi yana komawa maƙiyi, haka maƙiyi na komawa masoyi. Ku ji tsoran masoyin da ya koma makiyi, yafi illa saboda ya san komai naka yana da komai naka a hannun sa saboda da farko ya kasance masoyin ka. Mimi, Lubna da Kausar kar ku yi wannan gangancin a cikin rayuwar ku, ku duba goben ku da goben ƴaƴan ku, babu tozarcin da ya kai a yaɗa hotunan tsaraicin ka a duniya. Kar ku dinga gani a social media ku ɗauka baya faruwa a gaske, yana faruwa sosai ana blackmailing da abinda ka tura da kan ka koda mijin ne kuwa."

"Wani mijin in ya rabu dake neman hanyar da zai tozarta ki yake, a ganina babu tozarci kamar wannan hotunan a duniya. Kar ku aikata koda wasa, a kiyaye domin wata rana zaka yi dana sani indai ka aikata wannan shirmen, ba soyayya bace hauka ne da rashin sanin darajar kan ka. Ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, wani mijin koda ka tura masa bai ajjiye dan saboda ya tozarta ki koda ya rabu dake, amma akwai sace wayar, akwai ƙwancen waya. Ko iya wanda ya ƙwace wayar ne ya gani ya cuce ki. Ni kawai a shawarata kar ayi kar a fara."

Jin yayi shiru sai Mimi tace, "in sha Allah Yaya zamu kiyaye."
"In kuma akwai wacce ta taɓa aikatawa ku faɗa min, kar ku ji tsoro in da wacce ta turawa saurayin ta ta sanar dani." A tare suka haɗa baki suka ce, "wallahi bamu taɓa ba." Ya girgiza kai yace, "duk saurayin da zai tambayi ki turo masa wani sassa na jikin ki ba auren ki zai yi ba, ku kula. Lubna da Kausar da ku nake." Lubna tace, "in sha Allah."
"Zaku iya tafiya" ya faɗa tana kallon window Lubna tace, "mun gode Yaya." Bai kalle su ba suka fita ko wacce na tunanin kenan abinda ya faru da Yaya Maryam kenan tunda gashi yana yi musu nasiha akan hakan.

Yana nan tsaye ya sake kiran wayar Manal akayi sa'a aka ɗauka bai jira anyi magana ba yace, "laifi nayi ne nima? Manal ya kike so nayi kin ƙi ɗaukar wayata? Dame zan ji?."
"Ba ita bace, Yayar tace Mubeena." Jin haka sai ya gyara tsayuwa Mubeena tace, "Manal yanzu haka bacci take, bata da lafiya sosai dan rabon ta da abinci ina jin tunda kafin tazo gidan nan, taƙi cin komai sai tea da ta sha kawai. Jikin ta yayi zafi sosai, bata da aiki sai kuka, ko bacci tayi ta tashi kuka zaka ga tana yi. Kai likita ne kasan damuwar nan zata iya sakawa cikin ta ya zube."

"Hasbunaallahu wani'imal wakil!" Ya furta a sanyaye Mubeena tace, "A nan ɓangaren bamu san komai ba har yanzu, in da dama zaka iya tambayar mahaifin ka ko kai zaka samo wani dalili da ya saka aka aikata hakan kodan kwnaciya hankalin ka da nata, dan gaskiya Manal bata da lafiya sosai, yau wuni tayi kuka ga zazzaɓi. Shiyasa na zaɓi na amsa wayar ka na faɗa maka ko zaka samo mafita."

Daƙyar ya iya cewa, "zaki iya yi min wani taimako?."
Mubeena tace, "ina jin ka."
"Zan kawo mata magani yanzu, kizo ki karɓar mata." Mubeena tace, "babu damuwa." Yana jin haka ya yanke kiran ya ɗauki key na mota ya fita da sauri.

Sai da ya tsaya a pharmacy a hanya ya siyi maganin ya sannan tsaya a wani babban store ya shiga ya siyo duk abinda yasan zata iya ci a lokacin sannan ya ƙarasa gidan su Manal ɗin. Wayar Manal ɗin ya kira ba a ɗauka ba babu jimawa sai ga Mubeena ta fito ta ƙaraso wajan da yake, ya fito daga motar ya miƙa mata ledar yace, "ki tabbatar ta sha don Allah, sannan tana yawan son shan sugar a kwanakin nan kar ki bari hakan ta kasance, yanzu haka sugar ta is too high in ta kuma sha abin zai yi worst. In ta takura baza ta sha tea ba sai da sugar ga wannan" ya faɗa yana sake miƙa mata leda mai girma yace, "zata iya amfani da komai na ciki."

Karɓa Mubeena tayi tace, "in sha Allah. Amma ka nemi mafita shine maganin wannan damuwar, Kwana na biyu kawai aka yi ga abinda ya faru, in kwanakin suka yi nisa abin bazai yi daɗi ba."
"In sha Allah. Na gode, ki gaishe ta in ta farka, in da hali ki kira in ta tashi duk dare." Mubeena ta amsa tana wucewa gida shi kuma ya hau mota ya koma gidan su.

Sai da yayi sallar Isha sannan ya shiga gida yana shiga kai tsaye wajan abba ya wuce, ya samu Abban da ƴan uwan sa maza guda biyu a zaune da alama magana mai mahimmaci suke yi. Yana shiga da sallama suka amsa ya zauna bai ce komai ba. Daddy ya kalle shi yace, "Adnan ya dai?."
"Daddy ku saka baki Abba ya warware min abinda ya ɗaure min kai don Allah."

Daddy yace, "me kenan adnan?."
"Abba ina so na san wacece mahifiyar Manal matata a wajan Abba." Daddy ya kalle Abba yace, "ka sanar dashi wacece ita a wajan ka." Abba ya kulle ido ya buɗe ya sauke numfashi yace, "ita bata faɗa maka ba?."

Bebi yace, "naje jiya, amma ta tabbatar min da babu aurena da Manal, ta kuma tabbatar min da kai ne matsalar ta ba ni ba." Abba ya sauke numfashi cikin damuwar da tayi masa yawa a zuciyar sa yace, "dole tace maka haka, domin kuwa yadda ka ke ɗana haka itama take ƴata Adnan!."

BDƘB3P05

A firgice Bebi ya kalli Abba cikin tashin hankali da faɗuwar gaban da tazo masa lokaci ɗaya mai haɗe da tashin hankali, yadda ya wara idanun sa kawai zai tabbatar maka da yadda yake cikin tashin hankali a wannan lokacin. Tabbas in za'a auna bugun zuciyar sa a wannan lokacin za'a ga zuciyar sa bata bugawa daidai, sannan jinin sa za'a tarar ya hau saboda tashin hankali.
Chapter 6 · 0% Book details