Sashe 51
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Mustapha Yayan su Mama yace, “to wannan ai ba wani abun bane, daman ƴar sa ce bai sani ba kuma gata yanzu a zaune.” Daddy ya kalli Rumana da take kallon sa ta kalli Ammi ta ɗaga mata kai tace, “Shine mahaifin ki, na faɗa miki daman ban sani ba ko yana da rai ko baya da rai, yau gashi kin ganshi.” Daddy kallon Rumana yake yi cikin faruwar gaba ya kalli Sumayya kafin tayi magana Yayar ta Umma tace, “babu wanda ya san da ciki a lokacin da ka sake ta, sai bayan kwana biyu sannan aka tabbatar dashi, gashi kuma ka ɓace balle a sanar da kai akwai rabo tsakanin ku. Wannan dalili ne ya saka aka ajjiye batun ka har ta haihu ta raine ta da ta tashi yaye ta ta bawa Yayar ta Hauwa, a nan gidan Rumana ta girma a nan ta rayu a hannun yayar babar ta.”
Rantse ido Daddy yayi tare da yin shiru, shi muka tasa ƙaddarar kenan, karkasuwar yaran sa wanda ya sani da wanda bai sani ba saboda auren mata a waje daban-daban. Mama ta kasa magana tayi shiru kawai gabaɗaya tsoro ya mamaye mata zuciya. Abba ya kalle shi yace, “aka sake samun karuwar ƴa, daga biyu sun zaka uku.” Daddy ya rasa me ma zai ce yayi shiru kawai ya sunkuyar da kai cikim sanyi jiki. Yaya Mustapha yace, “rabon zasu ga junq ne ya kawo mu yanzu, da rabon Rumana zata san mahaifin ta.”
Wajan yayi shiru babu wanda yake magana saboda tashin hankali, Daddy ya kasa ko motsin kirki kunya gabaɗaya ta dabaibaye shi, bai yiwa Sumayya komai a lokacin auren su ba, bai wulaƙanta ta kamar yadda ya yiwa Maman su Manal ba, ita cikin ruwan sanyi suka rabu bayan yace mata tayi haƙuri wani dalili ya saka zai rabu da ita.
Rumana dai kallon sa kawai take yi cikin tashin hankali gabaɗayq wani iri take ji a zuciyar ta. Ta kalli Mama. Tace, “Mama da gaske shine mahaifina?.” Mama bata amsa ba sai Umma da tace, “shine Rumana.” Rumana ta kalli Daddy da ya sunkuyar da kai bai ce komai ba ta sake kallon Babar ta. Abba yace, “kar ki damu zai warware miki komai, Aliyu ya kamata ace a sanar da iyalan ka kowa ya san Rumana ya kuma san labarin Rumana da mahaifiyar ta. Rai ba a hannun mu yake ba ko yaushe rai zai iya yin halin sa, gwara kowa ya san ta kafin mutuwa ta ratso tsakiya.”
Sumayya ta taɓe baki ganin sai wani sauke kai ƙasa yake yi, duk da ita baza tace ga abinda yayi mata ba, kawai dai auren ta auren bai kai shekara biyu ba suka rabu shine kawai matsalar. Mama ta kalli Dady tace, “Bayan Sumayya kuma sai wacece? Tunda na lura auren mata ka ke yi kana sakin su kana barin ƴaƴan ka, tun a shekarun baya daman akwai irin ku?.”
Daddy bai iya magana ba Yayan Mama ya kalle ta yace yace, “meye haka Hauwa? Wacce irin magana ki ke yi haka? Bakya ganin ga ƴar sa nan a zaune?.” Mama ta kau da kai gefe Daddy yace, “barta ta faɗa, gaskiyar ta ne haka lamarin yake, suke nan matan da na san na aura a rayuwata, kuma dukkan su babu wacce ban yi nadamar bari ba, ban san kuma cewa Sumayya akwai ciki a lokacin ba da ba’a kawo wannan lokacin ban san ƴata ba” ya faɗa yana kallon Rumana da idon ta ya cika da hawaye.
Yaya Mustapha yace, “aure ai rai ne dashi, rabon zata je wani gidan tayi aure har ta haifi yara huɗu bayan Rumana ne ya saka auren ku ya mutu. A shekarar da auren ya mutu bayan ta haihu tana yaye Rumana Allah ya bata miji tayi aure dalilin da ya saka Rumana ta tashi a hannun Yayar ta kenan, to ni ban ga abin damuwa a nan ba, rashin sanin ƴar ka ne daman kawai matsalar kuma ka ganta, kaga shikenan sai ka nuna ta ga iyalan ka a cigaba da zumunci.”
Abba yace, “haka ne, amma don Allah ku tsaya a kira iyalan nasa gabaɗayq su zo nan a sake maimaita maganar nan. Ya kamata ayi komai da hanzari kar rai yayi halin sa, gwara ka sanar dasu su san tun a yanzu” ya faɗa yana kallon Daddy da ya kasa magana.
Daddy ya girgiza kai ya goge idanun sa yace, “haka ne, kira Huzaifa.” Yaya Mustapha yace, “wannan gaskiya ne, ni dai yanzu akwai meetingin da zan yi amma zuwa dare zan iya dawowa in an mayar da taron zuwa dare.” Abbba yace, “Babu komai Alhaji Mustapha, Allah ya nuna lokacin za’ar sanar da kowa ya zo zuwa dare a tattauna abinda ya kwnata.” Ya amsa ya tashi ya fita duk suka bi bayan sa har Rumana da take kuka.
Daddy ya kalli Abba bayan fita yace, “Duk wannan kunyar duniyar da nake ji haƙƙin mahaifiyar Manal ne fa, haƙƙjn ta ne saboda itace marainiya gaba da baya kuma na wulaƙanta ta. Wannan shine kwatankwacin kunyar duniya kenan, ina ga kunyar lahira?. Ni dai zan je yanzu na kai nata documents ɗin nan ko zan samu hankalina ya kwanta. Kaga fa ashe ina da wata ɗiyar bayan su Mubeena, gwara su na san dasu tun farko, amma ita ban san da ita ba. Wacce irin rayuwa nayi a baya ne? Wanne irin kuskure na dinga aikatawa?.”
Abba yayi murmushi takaici yace, “kuskuren da kayi ba komai bane akan wanda nayi, na faɗa maka kai kan ka da zaka ji abinda na aikata tabbas da zaka yi baya dani, zaka tsana ni ka kuma tsani halayya ta. Nayi abubuwa da yawa wanda yanzu nake dana sani bayan na fara ganin sakamakona tun a duniya. Wallahi na gwammaci mutuwa a akan wannan rayuwar da nake ciki.”
Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace, “duk kuma da ilimin mu a lokacin, Mun san gaskiya muka dinga bi muna saka ƙafa muna takewa. Allah ka yafe mana, Allah ka raba mu da jin kunyar lahira, ta duniya dai mun ji ta.” Abba ya amsa da amin Daddy ya miƙe tsaye yana jiri ya dafe kai yace, “zan kira Huzaifa yazo muje gidan su Manal ɗin, ayi komai a gama.” Kai kawai Abba ya ɗaga masa ya fita ya shiga mota driver ya fita dashi.
A ƙofar gidan su Manal suka haɗu da Huzaifa da yace ya same shi a a ƙofar gidan su Manal, Huzaifa ya kira Baba a waya ya sanar dashi baya nan amma yanzu zai dawo. Suna zaune a motar kuwa sai gashi ya dawo Daddy da Huzaifa suka shiga ciki da ispm Baba.
Mama ce kawai a gidan Mubeena tana can gidan ƴan uwa, Mubeena bata zama itace nan itace can ana gaisawa da ƴan uwa. Su Abba suka shiga cikin gidan da sallama. Mama ta amsa tana kallon su tace, “A’a sannun ku da zuwa.” Suka amsa har cikin falon suka shiga Huzaifa ya gaishe ta amsa kamar ko yaushe suka gaisa da Daddy kafin yace, “Fatima haƙƙin ki da yake rataye a wuyana shine yake ɗawainiya dani, abubuwa daga wannan sai wannan suna ta faruwa. Shiyasa nazo na sauke haƙƙin ki da yake kaina.”
Mama bata ce komai ya fito da taron takardu a babbar jaka ya ajjiye a gaban Baba yace, “wannan shine takardar duk wani abu da na mallaka wanda yake Kano da wajan kano, takardar company da komai suna ciki. Gidan da na mallaka a Qatar ne kawai babu shi a nan saboda shi yana can, amma in na koma duk zan tattaro na kawo mata zan kuma tashi daga gidan, kuɗi kuma suna da yawa zan turo maka duka a cikin account ɗin ta, tunda haƙƙiin ta ne ba nata ba.”
Baba bai ce komai ba ya kalli Mama da take jin abinda yake cewa tace, “ni nace maka dukiyar tana gabana ne?.” Daddy yace, “baki ce ba, amma haƙƙin ki da na raba ki dashi yanzu na dawo dasu. Nazo naje na samu Alhaji Ahmad ma sai akace min ya koma Abuja, shiyasa nazo da wakilan kema ga wakilin ki ayi komai gaban su, na dawo miki da dukiyar ki da na ɗauka na tafi da ita a wancan lokacin.”
Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, “ka ɗauke documents ɗim ka ni bani buƙatar wasu dukiyar ka, da ka ɗauka Allah yayi zasu zaɓa rabon ka, kawai ka tabbatara ka koma dasu tunda ban neme su a baya ba a yanzu da Allah ya sake rufa min asiri ƴan uwana suka bayyana bani da buƙatar amfani da wata dukiya, dukiyar ƴan uwana ta ishe ni yin duk abinda nake so nayi, dan haka ka ɗauka kaje ka cigaba da kasuwancin ka.”
Daddy ya girgiza kai yace, “bazan iya komawa dasu ba saboda haƙƙim ki ne, in na tafi dasu haram nake ci saboda naki ne ba nawa ba, don haka ko bakya so zan tafi na bar su a nan zan kuma tashi daga duk gidan da na kawo miki takardar da, abubuwan da na mallaka kafin auren ki sune nawa, amma daga lokacin da na aure ki dukiyar ki da siya na cigaba da amfani ba tawa ba. Gabaɗaya dukiyar tawa bata taka kara ta karya ba, shiyasa na tabbatar da komai na mallaka naki ne ba nawa ba.”
Mama tace, “na sani, amma ina faɗa maka bani da buƙatar su ne ka tafi dasu kamar yadda suke a wajan ka, ni na yafe.” Daddy yace, “bazan iya ba, a hannun ki zan barsu saboda haƙƙin ki ne ba haƙƙina ba.”
Mama ta kalli Baba da yake jin abinda ake yi tace, “ka sanar dashi ya ɗauke dukiyar sa bani da buƙayar ta a cikin rayuwata, yaje ya cigaba da harkokin za komai ya wuce har dukiyar na bar masa. Bana so ba kuma na so a dinga tuna min da abinda ya riga ya wuce, yadda na manta da komai a bar ni a na manta ɗin, tunawa zai iya jawowa na furta wata kalma mara daɗin ji.”