← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 84

Sashe 37

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba yace, “Ta faɗa miki ne kawai, amma wannan shine asalin wanda ya haife ki.” Mubeena ta sake kallon Daddy tana sake maimaitawa abinda Baba yace mata kafin ta girgiza kai tace, “to Baba in ma da gaske shine mahaifin na mu me yazo yayi mana?.”

Baba ya kalle ta yace, “wacce irin magana ki ke haka kema?, mahaifin ki fa nace miki?.”

“Da gaskiyar ta ai, me yazo yayi mana?.” Baba zai yi magana suka ji murya Mama tace, “yanzu ba anjima ba bana son sake ganin wani a cikin gidan nan, don Allah a fita daga cikin sa bana son ganin wanda suka shigo” Mama ta faɗa tana sake komawa ciki dan ganin da take musu ji take kamar ta yi hauka saboda ɓacin rai.

Daddy ya sauke numfashi ya kalli Abba da yayi shiru shima, Daddy ya kalli Mubeena da take kallon sa amma ya kasa cewa komai. Baba yace, “Alhaji Mu’azzam ku yi haƙuri, ku tazo mu koma waccan ɗakun mu tattauna a can, Ku yi haƙuri” ya faɗa yana kallon su. Daddy yace, “wannan ba abinda za’a bamu haƙuri bane, me akayi mana da za’a bamu haƙuri?.”

“Duk da hakan muje mu yi magana.” A tare suka tashi zuwa ƙaramin falon baba jikin su a sanyaye.

A falon Baba suka zauna Baba ya kalle su ya ce, “Alhaji Mu’azzam Ku yi haƙuri da abinda Mubeena da mahaifiyar ta suka yi, amma zan so ka sake yi min bayani yadda zan fahimta, tana magana a juye cikin fushin da ta jima da binnewa a zuciyar ta.” Daddy ya kalle shi cikin sanyin jiki yace, “in akwai abinda yafi fushi ya kamata ace Zahra tayi shi, bamu cancanci ta zauna damu ayi magana ba wallahi. Ni kunya duk ta rufe ni.”

Baba ya sauke numfashi yace, “Kenan da gaske kaine mahaifin su Mubeena, kaine wanda na san labarin ka a bakin ta.” Ya girgiza kai yace, “ƙwarai ni ne, na san baka san labarina mai daɗi a bakin ta ba.” Baba ya girgiza kai yayi shiru bai ce komai ba dan bai san abinda zai ce ba, kan sa ya kulle gabaɗaya ganin abun yake kamar a mafarki.

Baba ya sake kallon su yace, “Dani da ita da yaran ta duka tana ce mana ka rasu ne, a haka muka ɗauka gabaɗayan mu, a yanzun ma ba dan da Alhaji Mu’azaam kazo ba kafin na amince kaine mahaifin su gaskiya za’a ɗauki lokaci sosai. Amma yanzu na gasgata kai ne mahaifin su, kuma kazo kayi magana da ita ne ko?.”

Daddy ya goge idanun yace, “nazo nayi magana da ita, domin akwai abubuwa da yawa da nake so na faɗa, ina so na bata haƙuri daga ita har yaran nata.”

Baba yayi shiru bai ce komai ba Daddy yace, “Bani da idanun da zan iya kallon ta ni na sani, bani da bakin da zan yi mata magana ta amince dashi. Ta dauƙi yarda ta bani ni kuma naci amanar ta a lokacin da take matuƙat buƙatar kula daga gare ni, ban ji komai a lokacin da zan aikata ba, ban ji ɗar na tsoran yaudarar ta ba a ba sai bayan na aikata. Wallahi Allah ne shaida na neme ta daga baya amma ban same ta ba, amma yanzu ko me zance baza ta amince ba.”

Baba ya sauke numfashi yace, “gaskiya a yanzu ko me zaka ce mata baza ta amince ba, a yanzu baza ta tsaya ayi magana da ita ba, a yanzu baza ta sake sauraron wanda zai yi magana da kai ba balle kai da kan ka. A kaf duniya babu abinda take tunawa take zubar da hawaye kamar wannan maganar, babu abinda take tunawa ta kwanta a gadon asibiti sai wannan. Tana yawan cewa da ana goge abinda ya wuce tabbas da ta goge abinda ya faru a rayuwar ta da kai, ba kai kaɗai ba ba hatta ƴan uwan ta na jini tace bata son sake haɗa ido dasu, magana da ita ba yanzu ba gaskiya, sai zuciyar ta tayi sanyi. Iya Alhaji Mu’azzam kawai ta gani ta tayar da hankalin ta har taso raba auren ƴarta da ɗansa ina kuma ga kai?.”

Daddy cikin rauni yace, “na sani, hukuncin da ya kamace ni kenan daman. Ni ba mutum na gari bane a idon ta, ni ba mutum mai adalci bane a idanun ta, ni mutum ne mai son kansa wanda bashi da tausayi ko kaɗan. Ni naje har gidan su na karɓi auren ta na baro ta da asalin jahar ta da dangin na taho da ita inda nake, amma da na tashi barin ta banyi wani tunani ba na tafi na bara. Ban yi tunani abinda ta haifa a lokacin ba, dan a lokacin ƴar mu ta farko ma ƙaramar yarinya ce sannan ga ta biyu wacce ta kasance jaririya. Ban yi tunanin inda zata kwana ba, ban yi tunanin ina zata nufa ba, ban yi tunanin halin da zata faɗa ba,  ban yi tunanin babu wanda ta sani sai ni kawai….gaskiya ban cancanci ta haɗa idanu dani ba, na cutar da ita” ya faɗa yana sake cire glasses ɗin idanun sa yana share hawaye.

Baba ya sauke numfashi  cikin sanyin jiki yace, “kar ka damu Alhaji Aliyu, zata saurare ka in sha Allah, amma ba yanzu ba sai dai abi komai a hankali.” Abba da yayi shiru tunda aka fara maganar yace, “in dai muna da tsahon rai zamu dinga bin ta har ta yafe mana dukkan mu, duk da mu ba mutanen kirki bane a wajan ta.”

Baba yace, “Allah ya kaimu lokacin, Allah ya sassauta mata zuciyar ta, ku da ku ka yi nadama Allah ya yafe gabaɗaya.” Suka amsa da amin Daddy ya mayar da glasses ɗin idanun sa yace, “Mubeena itace Nusaiba?.” Baba yayi murmushi itace, “itace.”

“Ina Fatima?.”

Baba yace, “Manal kenan, itace matar Adnan a yanzu” ya faɗa tana nuna masa Bebi da yake zaune kansa a ƙasa kamar baya wajan.

Daddy ya kalli Baba da mamaki ya kuma kalli Adnan ya sake kallon Baba ya ce, “kenan yarinyar da muka je barkar abinda ta haifa a matsayina na mahaifin abokin mijin ta itace Fatima?.” Baba yace, “Tabbas!, Itace fatima wacce muke kira Manal.” Daddy idanun sa suka sake cikowa da ƙwalla yace, “kenan abinda ta haifa jikana ne?.” Baba ya sake ɗaga masa kai yana murmushi tare da cewa, “ƙwarai kuwa, rashin sanin kenan.”

Daddy ya dafe kai kawai ya fashe da kuka mai ciwo yana cewa, “ban cancani Zahra ta kale ni ba, wallahi ban cancanci ta haɗa ma idanu da ni ba. Bayan na auro ta na raba ta da dangin ta a lokacin da take ciki maraici, na kawo ta inda babu wanda ta sani, na zauna da ita na wani lokaci daga baya na kwashe kaf dukiyar da ta gada wajan iyayen ta na gudu bayan na sake ta. Na tafi na barta ba tare da nayi tunanin yaran da na bari tare da ita ba, banyi tunanin babu wanda ta sani sai ni ba, ban yi tunanin ina zata nufa ba, banyi tunani rayuwar ta da ta yaran ta ba. Abinda ya kai ni ga auren ta na samu na kuma tafi na barta a inda babu wanda ta sani ni. Yanzu kuma yara sun girma har ɗaya ta haihu kuma sai nazo bace nawa ne?, Ban isa ba” ya faɗa yana girgiza kai yana kuma zubar da hawaye.

Abba ma kukan yake yi  sosai, Adnan da Huzaifa gabaɗaya jikin su ya gama yin sanyi ganin iyayen su maza suna kuka kamar yara ƙanana, sun kasa furta komai kan su yana ƙasa amma Allah kaɗai ya san abinda suke ji a zuciyar su. Adnan ne ya tafi ya fita dan bazai iya jure ganin hawayen mahaifin sa ba, ganin haka Huzaifa ma ya biyo bayan sa ya same shi a zaune a mota ya kifa kansa a kan sitiyarin motar.

A mazaunin gaba ya zauna jiki a sanyaye ya ce, “Bebi na kasa fahimta abinda yake faruwa? Su waye su Manal a wajen Daddy? Wacece Maman Manal a wajan Daddy?. Ya akayi suka ana ta?. Sannan me yasa suke kuka akan abinda suka aikata?.”

Bebi ya ɗago ya kalle shi bayan yayi ajiyar zuciya yace, “Mama matar Daddy ce a wasu shekaru da suka wuce, Manal da Mubeena duka ƴaƴan sane kuma ƙannen ka.”

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Meyasa baka taɓa sanar dani ba sai yanzu?.”

“Nima yanzu na san da hakan.”

Huzaifa ya kasa cewa komai sai ƙirjin sa da yake bugawa sosai ya kalli Bebi da ya kulle ido ya buɗe yace, “Amma akace mahaifin Manal ya rasu.” Bebi ya kalle shi yace, “Yana nan da ran sa, gashi nan a ciki tare da Abba.” Huzaifa yace, “to me ya shigo da Abba maganar? Ya akayi suka haɗu har suka rabu? Meyasa bai sake waiwayon Maman ba har su Manal suka kawo wannan matakin?. Wacce dukiya Daddy yake magana a kai Bebi? Kaina ya kulle ka warware min abinda ban sani ba don Allah.”

Bebi yayi murmushi mai ciwo yace, “zaka fahimta in lokacin ka fahimta ɗin yayi, yanzu ka cigaba da zama da kullewar kan har sai ka tambayi Daddy.”

Hango su Baba suka yi sun fito suna ƙarasowa wajan motar hakan ya saka suka dakata da maganar, Daddy da Abba suka shiga motar bayan sun yiwa Baba godiya. Bayan sun shiga murya a dashe Abba yace, “Adnan mu tafi.” Kunna motar yayi ya tafi amma hankalin sa baya jikin sa shi kansa.

Babu wanda yayi magana kowa yayi shiru tafiya kawai suke yi. Bebi yace, “ina zamu je?.” Abba yace, “mu koma gida.”

BDƘB3P21

A harabar gidan su Bebi aka faka motar Abba ya ce, "mu wuce mu yi sallah sai mu shiga ciki." Haka kuwa aka yi sallah suka yi suka dawo cikin gidan suka zauna shi da Abba. Bebi Abba ya kira a waya yana ɗauka yace, "ka kira min kowa a cikin ƴan uwan ka, har Mimi da Farida in suna da damar zuwa a yanzu su zo ina son ganin ku."
Chapter 37 · 0% Book details