← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 84

Sashe 64

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin ya shigo falon yana daga tsaye Rumana tace, “ni zan wuce, gobe Abuja zan tafi in Allah ya kaimu. Zamu dinga gaisawa a waya.” Manal tace, “Allah ya kiyaye hanya, a gaishe da mutanen Abuja.” Rumana ta amsa da amin ta bata Ayan tana cewa, “Zan yi kewar Baby Ayan.” Manal bata ce komai ba Rumana ta kalli Bebi tace, “na tafi.”
“Allah ya kiyaye hanya, ki cigaba da kula da shan maganin ki komai zai zama tarirhi in sha Allah.” Tayi murmushi zata wuce shi tayi tuntuɓe da carpet zata faɗi ya yi saurin riƙo hannun ta yace, “ki bi a hankali, daman kin zama kamar kara ba dole komai yayi ƙoƙarin kayar dake ba.”

Tayi dariya ta kalli Manal tace, “ƙanwata mijin ki baya girmama ni.” Manal murmushin yaƙe tayi tace, “kun fi kusa ai.” Ta sake yin dariya tayi hanyar fita Manal ta raka ta har harabar gidan ta shiga mota driver ya ja suka tafi.

Shima a nan suka rabu ya hau mota ya fita, haka Manal ta koma ciki ranta duk babu daɗi a haka ta kai dare har lokacin da ya dawo. Bai lura da yanayin ta ba dan bai jira tazo ta zuba masa abinci ba da kansa ya zuba yaci dan yunwa yake ji. Sai bayan ya shirin kwanciya ya fito suks haɗu a falo tana niyar shiga ɗakin sa. Kallon sa tayi tace, “Mummy tace tana kiran ka baka ɗauka, in kazo ka kira ta.” Kai ya ɗaga yana kallon ta wuce shi bata sake magana ba.

39

Bebi bayan ya gama wayar ɗaki ya same ta a zaune a gefen gado ya kalle ta yace, “lafiya ki ke?.” Ta ɗaga kai tace, “lafiya.”
“Ban yarda ba, tun daga zuwan Ruman kika canja.” Ta runtse ido ta buɗe ta kalle shi tace, “ka kasa daina cire harafin ƙarshe na sunan ta, na faɗa maka bana so amma ka kasa.” Ya dafe kai yace, “i’m sorry, na riga na saba ne ba ina sane nake faɗa ba. Kar ki ce min da Yayar ki kike kishi Manal?.”

“In nayi kishin ma ai ba laifi nayi ba, tunda ka ganta ka rikice kamar ba kai ba, kace wannan kace wancan kamar wanda aka sakawa battery. Harda riƙe mata hannu a gabana” ta faɗa tana kallon sa tare da nuna kanta da yatsa. Ya sauke numfashi ya ce, “Manal Rumana fa yayar ki ce uba ɗaya, meye na kishi da ita don Allah?. Kuma laifi ne dan na tambayi lafiyar ta?, baki ga yadda ta koma bane?.” Ta kawar da kai gefe tana goge idanun ta tace, “yanayin yadda ka ke tambayar ta ta daban dana sauran mutane, tunda ta shigo ka ke kallon ta har ta fita.”

Yayi murmushi ya ce, “Manal kar ki manta nima ƴar uwata ce, nuna damuwa akan damuwar ta ba laifi nayi ba. Sannan kar ki manta tsananin son da take yi min ne ya saka mata ciwo, in ban rarrashe ta ba waye zai rarrashe ta taji daɗi?.”

Manal ta kalle shi jin abinda yace tana yi masa wani kallo kafin tace, “eh gaskiya kai ɗin ne kawai. Faɗa min tana yi maka son da ya saka mata ciwo, cigaba da faɗa min son da take yi maka ni ban yi maka irin sa. Tunda ni son ka bai saka min ciwo ba ita ya saka mata, kaga kenan yadda take son ka ni bana son ka haka. Ina jin ka cigaba.” Dafe kansa yayi jin ta canja maganar dan shi dariya take bashi ya ƙaraso ya zauna ya ce, “ni na isa nace haka? Waye Adnan da zai cewa Manal haka?. Ni ba da wani abun na faɗa ba ina faɗa miki ne dan ki fahimci tausayi take bani.”

“Hmmm! Tausayi yana komawa soyayya” ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba. Ya ce, “to ke banda rigima irin taki ina ni ina soyayya da ita? Yayar ki ce fa.”
“Hmmm kuma ita ka fara so kafin ni ba.”
“Manal kina da tayar da zaune tsaye wallahi, meya kawo batun ita na fara so kuma yanzu?. ni da nake kishi da Huzaifa ki ke ganin laifina kema gashi yanzu kina kishi da Yayar ki.”
“Har abada babu aure a tsakanina da Yaya Huzaifa, ko mazan duniya zasu ƙare bazan aure shi ba saboda Yayana ne. Kai kuwa ko yau akace babu Manal zaka iya auren ta domin ba maharramar ka bace, kaga kenan na fika hujja akan kishi da ita.”

Ya riƙo ta jikin sa ya ce, “to naji, yanzu dai wannan maganar ta wuce. Kin sani, na sani maganar ta ya riga da ya wuce gabaɗaya.”
Ta kalle shi tace, “Ni da Yayana ya riƙe min hannu a gaban ka nunawa kayi kana kishi da hakan, amma kai a gabana ka ke riƙe hannun wacce ba maharramar ka ba.”
Da mamaki “Baki ga faɗuwa tazo yi ba? Kenan sai na bari ta faɗi?.”
“Ba sai ka jira na taso na riƙe ta ba? Lallai sai ka nuna min ita ka fara so bani ba?.”
“Na shiga uku na!. Allah ya baki haƙuri, shikenan?.”

Ta kawar da kai bata yi magana ba sai goge ido da take yi ya ce, “na ce ki yi haƙuri ba shikenan ba?.” Ta sauke numfashi ta kawar da kai gefe tace, “taya zan yi haƙuri bayan har yanzu sunan da ka ke faɗa mata daban dana mutane?. Nunawa ka ke har yanzu ita ta musamman ce a wajan ka.”

Yayi murmushi ya ce, “in sha Allah na daina cewa Ruman sai Rumana daga yau, shikenan dai ko?.” Kai ta ɗaga yayi dariya yace, “Manali na mai sona.” Tayi dariya itama ya ja hancin ta yace, “rigimar ki bata ƙarewa.” Murmushi take yi tana jikin sa a kwance kafin su tashi suje su kwanta cikin soyayya da shauƙin junan su.

            Bayan wasu kwanaki.

Komai ya lafa a cikin family, Rumana ta samu lafiya sai abinda ba a rasa ba, ta karɓi ƙaddara dan har gidan Manal din taje sannan kuma taje gidan su Huzaifa da na ƴan uwan su kowa ya ganta aka gaisa kafin ta koma Abuja da zama.

Bebi da Manal soyayya akwai suke sha a cikin kwanakin, in ba aiki ne dashi ba baya zuwa ko ina itama kuma a satin aka bata certificate na zaka professional chef. A cikin kwanakin ya takura mata sai ta shiga wata school ɗin ta cigaba da karatu ita kuma tace bata so dan baza tayi jamb ba yace zata fara private university. Ba yadda ta iya haka ya nemar mata makaranta ta ɗora daga inda ta tsaya.

Ranar juma'a suka tashi da farin ciki kasancewar ranar da za'a ɗaura auren Maryam da sabon mijin ta Mahmud, inda kuma a ranar aka karɓi kuɗin auren Lubna da ita da saurayin ta Sani.

Dukkan su suna gidan saboda farin ciki har Manal tana gidan suna tare dasu Mimi suna hira, har Mama suna falo a zaune gabaɗaya ana hira. A gidan suka wuni har dare kafin kowa ya tafi gida dan ba ranar Maryam zata tare ba.

Ɓangaren Maryam farin ciki take yi da sabon auren da tayi, duk da sabon mijin nata bai san da badaƙalar da ta aikata ba amma tana addu'ar Allah yasa bazai sani ba. A ranar da aka ɗaura auren da yamma angon ta yazo ya ɗauke ta suka fita yawo basu dawo ba sai dare sannan ya kawo ta gida ya tafi. Kwana biyu da ɗaurin auren ango shi da amaryar sa soyayya suke yi, a cikin kwana biyu zasu fita baza su dawo ba sai dare.

Ranar litinin ya kama ranar Maryam zata tare ƴan gidan gabaɗaya suna nan harda Manal, suna zaune a falon Mama ana hira Bebin  ya shigo da sallama yana amsa waya Mama ta kalle shi tace, "Sarkin amsa waya, kuma a wayar bashi da magana kuma sai ta aiki."

Bai zauna ba sai da ya kammala wayar sannan ya zauna yace, "Mummy Hajiya tace nace miki akwai bikin ko ƴar gidan gwaggo wa dai na manta." Mama tace, "jiya tace ka faɗa min ai ka manta sai yanzu?."
"Na manta wallahi, sai yanzu na tuna shiyasa ma nazo na faɗa miki kafin na kuma mantawa."
Farida ce ta fito tana cewa, "Mama Mun yi magana da likitan ranar laraba zamu je." Ya kalli Farida yace, "wanne likita?."

Ta zauna tana cewa, "ina ruwan ka?." Mama tace, "zamu je a kai Mimi ne wajan likitan da zai duba ta."ya kalli Mimi da take gefe yace, "bata da lafiya?." Mama tace, "eh kusan hakan, tana matsalar infertility."
"Infertility!" Ya maimaita yana kallon Mimi Mama tace, "eh."

"Mummy har yaushe akayi auren da za'a fara jawo mata problem na infertility?." Mama ta harare shi tace, "Kun wuce shekara ɗaya da aure fa, ga Ayan nan har ya fara gane babar sa da baban sa saboda yayi wayo. Ita kuwa ko missing period bata taɓa yi ba, kuma sai mu zauna ba za'a ga likita ba?."

Bebi yace, "amma Mummy shekara ɗaya ne fa kawai, ai lokacin bai yi tsahon da za'a fara zancen infertility ba."
"Kai baza ka gane ba ai."
Yace, "ba sai taje taga likita ba akwai maganin da za'a bata ta sha shima Tahir ɗin ya sha and akwai...." Sai kuma ya fasa faɗar maganar yace, "zan dai duba dai, in likitan zata gani akwai Hamza in kuma bakuwa son na gida akwai wacce zan haɗa ku da ita daga india take zuwa." Mamma tace, "A'a Bebi, na san halin ka kar ka shiririntar da maganar fa."

"Bazan manta ba, anjima da daddare zan je asibitin zan kawo mata in sha Allah."
"Allah sa a dace."
"Amin Mummy. kar ki damu fa, wannan ba abin damuwa bane,  just one year a fara zancen infertility" ya faɗa yana tashi tsaye yana kallon Farida yace, "duk ke kika shirya wannan abun." Farida tayi dariya tace, "tunda taka ta haihu ai haka zaka ce, dole na shirya saboda bana son ƙanwata ta shiga matsalar dangin miji."
Chapter 64 · 0% Book details