Sashe 50
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya Harare ta tace, “ko yau ne ai ya kamata na sani. zazzaɓin jikin sa ya sauka?” Ya faɗa yana taɓa jikin Ayan sai yayi ƙaramin tsaki yace, “har yanzu akwai, Murar nan ta dame shi wallahi.” Manal tayi shiru bata ce komai ba dan da tayi magana zai ce ai itace ta jawo ya sake kallon ta yace, “to Madam muje ko?.” Ta ɗan kalle shi tace, “kai ko jan ajin nan babu?.” Zai yi magana aka kira shi a waya ganin sunan Mama ne sai ya ɗauka.
Hankalin sa ya tashi jin Mama tana kuka yace, “Mummy lafiya? Me ya faru naji maganar ki haka?.” Mama tace, “Adnan Abban ku ne, kazo gida jikin sa yayi zafi yace bazai je asibiti ba, kazo don Allah yanzu.” Kashe wayar yayi yace, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.”
Manal da ta miƙe tsaye tana kallon sa tace, “Meya faru?.” Ya kalle ya ce, “ina zuwa” ya faɗa yana fita da sauri. Hankalin ta ita kanta yaƙi kwanciya saboda bata san abinda ya faru ba, shi kuma Bebi kai tsaye gidan ya wuce.
Yana zuwa ya tarar da kowa yana zaune an saka shi a gaba shigar sa sai Yaya yace, “Yauwa gwara da kazo Bebi, yaƙi yarda a tafi asibiti kuma jikin sa yayi zafi sosai.” Bebi ya ƙaraso ya riƙe hannun Abban jin da zafi sosai yace, “Abba don Allah muje asibiti, zaka fi samun kwanciyar hankalina can.”
Abba ya tashi zaune yace, “ba sai naje ko ina ba Adnan, kawai ku tafi gidan ku zan samu lafiya.” Bebi yace, “don Allah.”
“Ka bar min magiya bazan je ba.” Bebi ya kalli Yaya da yake tsaye yace, “zan je na ɗauko abinda ya kamata ayi masa yanzu na dawo” ya faɗa yanafita ya hau mota da hanzari ya nufi asibiti.
Bai jima sosai ba ya dawo yana higowa ya auna bp ɗin Abban kamar yadda yayi tunani ya hau sosai ya saka masa ruwan da zai saukar dashi har da lalurar bacci yayi masa. Suna zaune kusa dashi ana yi masa sannu har bacci ya ɗauke shi, duk suka fito aka bar shi dan ya samu yayi baccin sosai Mamy ce kawai ta rage a wajan sa.
Lokacin sha biyu na dare har ta gota ya hau mota ya tafi gida gabaɗaya jikin sa yayi sanyi akan lamarin damuwar da Abba yake sakawa a zuciyar sa. Haka ya shiga jiki a sanyaye ya kulle gidan gabaɗaya ya shiga ciki. A ɗakin sa ya same ta a kwance tana ji ya buɗe ƙofar ta tashi zaune tace, “baka faɗa min abinda ya faru ba, na kira ka yafi sau a irga baka ɗauka ba, me ya faru don Allah?.”
Ya ƙaraso yace, “Jikin Abba ne ya tashi, amma yanzu yayi bacci.” Manal tace, “amma shine ka ƙi faɗa min? da sauƙi dai ko?.” Ya ɗaga kai yace, “da sauƙi yayi bacci” ya faɗa yana shiga banɗaki. Tana zaune ya fito ya saka riga da wando na bacci ya kwanta a gefen ta yana kallon sama alamun akwai abinda yake damun sa. Kallon ta yayi ganin tana kallon sa sai yace, “babu komai fa kar ki damu.” Bata ce komai ba, dan da alama ya manta tace ta daina tambayar sa damuwar sa.
Haka suka kwana baya cikin walwala, abinda yayi kuɗurin yi baya cikin farin cikin aikatawa. Da safe ya sake komawa wajan Abban ya samu jikin yayi kyau sosai dan abinci ma yake ci Bebi ya zauna yace, “Abba ya sauƙin jikin?.”
Abba yace, “jiki yayi kyau Adnan, ko ciwon kan bana ji.”
“Haka ake so, amma Abba damuwa tayi maka yawa ita take saka ka a wannan yanayin.”
Abba ya girgiza kai bai ce komai ba sai daga baya yace, “Yauwa, akwai wanda yake neman auren Maryam, yanzu haka maganar na wajan Daddyn ku.” Bebi yaji daɗi a ransa sosai yace, “Allah ya tabbatar da alkhairi.” Ya amsa da amin. Shigowar Daddym su Huzaifa ne ya saka Adnan ya tashi tsaye, bayan sun gaisa yayi musu sallama ya fita.
Daddy ya kalle shi yace, “Ya jikin naka? Huzaifa yace min ba lafiya.”
“Naji sauƙ, daman jinin ne ya hau.” Daddy ya kalle shi yace, “akwai damuwa kenan?.”
“Babu komai, abinda ya wuce ne kawai bana son tunawa, kai kan ka kunyar ka nake ji.”
Daddy yace, “ni ya kamata ai naji kunya ba kai ba.” Abba yayi murmushi kawai bai ce komai ba dan bazai gane abinda yake nufi ba, shi kuma nauyim faɗa masa yake yi. Daddy ya kalle shi yace, “na gama tattara abinda zan iya na dukiyar babar su Manal zan mayar mata.” Abba yace, “in kace zaka yi haka kaf abinda ka tara nata ne fa, da dukiyar kayi ƙarfi haka.”
“Na sani, wani abun aai na koma qatar zan sake tattarowa.”
Abba ya sauke ajiyar zuciya yace, “hakan yayi, gwara ka fita haƙƙin ta, ko da baza ta karɓa ba dai kai ka bayar ka huta. Allah na gode maka da ban ci ko sisi a kuɗin ba, da yanzu tashin hankalin da nake ciki yafi haka.” Daddy yace, “so nake na gama da magana da damuwar nan gabaɗaya, na juya neman matata ta uku, wacce na faɗa maka ita na fara aura kafin babar su Manal.” Da sauri Abba ya kalle shi yace, “kana nufin akwai wata ma wacce ka tafi ka bari kenan?.” Daddy ya girgiza kai yace, “ƙwarai kuwa, ai na faɗa maka tun a shekarun baya ka manta ne. Amma ita na san dangin ta har gidan su na sani kuma ita ban barta da yaro ba, dole zan je na nemo ta a duk inda take ina da buƙatar neman yafiyar ta itama.”
Abba ya kalle shi da mamaki yace, “bayan ita sai wa kuma?.” Daddy yace, “ita kaɗai ce wallahi, su kenan su uku na aura. Kuma ita ban ɗaukar mata komai ba kawai nayi auren sha’awa da ita ne, ban taɓa zina ba kuma ban son yin zina kai ka sani, shiyasa tun a lokacin na amince na aure ta da na lalata ta.”
Jin abinda Daddy yace sai Abba yayi shiru jikin sa yayi sanyi ya sauke numfashi yace, “ka huta, kasan komai bazan ɓoye maka komai ba, nasan kasan sirikin da Allah ya baka, saboda Adnan yana auren Manal ƴarka hakan bazai hana ni faɗar abinda ka sani ba. Aliyu sharrin aikata zina ne yake bibiyata, yarana biyu a cikin gidan nan duk an yi zina dasu saboda nayi da na wasu. Ka huta da Allah bai saka ka a layin irin mu ba, da yanzu duniyar nan gabaɗaya baza ta tyi maka daɗi ba.”
Daddy yace sauke ajiyar zuciya yayi shiru yana jinjinwa hukuncin Alalh a kansu kafin yace, “kaima ai kayi nadama, kuma ka nemi tuba komai ya wuce.” Abba yace, “baza ka gane ba, baza ka gane irin ɓarnan da naso nayi ba shiyasa ka ke faɗat haka, Allah na gode maka da haka bani ikon aikata komai ba.”
Daddy yace, “yanzu taimaka min zaka yi na nemo ta na bata haƙuri itama komai ya wuce.” Abba yace, “a ina take?.”
“A nan kano take, a cikin unguwar…” ya faɗa yana tuna sunan unguwar kafin yace, “Unguwar Tarauni.” Abba ya sauke ajiyar zuciya yace, “meye sunan mahaifin nata?.” Daddy zai yi magana Mama ta shigo da sallama suka amsa ta kalle su bayan su gaisa da Daddy tace, “Su Sumayya ne suka zo gaishe ka dasu Yaya Mubarak.”
Abba yace, “bismillah su shigo.” Suka shigo da sallama aka amsa suka zauna Yaya Mubarak ya kalli Abba yace, “Alhaji ya jikin?.” Abba ya amsa yace, “Ya Abuja?.”
“Alhamdulillah.” Suka gaisa da Yayar Mama da kuma Sumayya ƙanwar Mama. Rumana ma na gefe suka gaisa da Abban. Daddy waya yake yi gabaɗaya hankalin sa baya kan au Ssi da ya gama ya kalle su suka gaisa da Yaya Mubakar yana kallon sa shima yana kallon sa.
Sumayya ce ta kalle shi sosai shima ita yake kallo, ɗauke ido yayi ya sake kallon ta ya kalli Yaya Mubakar ya sake kallon Sumayya ya kalli Abba yace, “Iyalan gidan Alhaji Abdullahi gwarzo ne?.” Abba ya ɗaga kai yace, “eh sune mana, Maman su Adnan ai ƴan uwan tane, lafiya dai?.”
Daddy ya kulle ido ƙirjin sa ya buga sosai ya kalli Sumayya da take kallon sa ya nunawa Abba ita yace, “itace wacce nake faɗa maka yanzu, itace matar da nake faɗa maka na aura. Meyasa abubuwan nan suke zuwar min haka? Meyasa suke zuwa a haka ne?, Meyasa duk abin ya zama wani iri?.”
Kowa kallon shi yake yi, Sumayya ta kalle su ta sake kallon sa amma bata ce komai ba. Yaya Mubakar yace, “in na fahimta daidai Aliyu ne a zaune girma ya kama shi haka ko?.” Mama da take gefe tace, “ban gane ba wai, waye shi ɗin?, kar dai kice min shine.” Sumayya ta girgiza kai tace, “shine Mama, shine wallahi.”
Rumana kallon su take yi a ranta tana maimaita shine wa….? Mama da take gefe tace, “kenan kina nufin shine mahaifin Rumana?.” Sumayya ta ɗaga kai alamun eh shine.
BDƘB3P30
Mama kallon Daddy tayi Abba ma kansa mamaki yake yi jin abinda yake faɗa, abin ya ɗaure masa kai sosai ya sake kallon Daddy ya ce, “Kenan Sumayya itace wacce ka ke min maganar ta yanzu?.” Daddy ya ɗaga kai ya ce, “itace” ya faɗa a raunane.
Mama ta kalli Rumana ta kalle shi ta kalli Sumayya tace, “kina nufin dai da gaske shine mahaifin Rumana?.” Sumayya tace, “shine.” Gaban Mama yayi mugun faɗuwa, ba komai ne yazo ranta sai tunawa da tayi kenan da Manal da Rumana mahaifin su ɗaya?. Ƙirjin ta bugawa take yi saboda tashin hankali. Sumayya tace, “lokacin auren bakya nan kina saudia lokacin Farida na fama da wannan ciwon cikin, hakan ya saka baki san shi ba har auren ya mutu kina can, kuma lokacin ba zamanim waya bane balle a tura miki hoto.”