← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 84

Sashe 80

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal tace, “na sha wahala sosai, ni su biyun nan ma sun ishe ni, Mamana ma ai damu kawai ta rayu gashi yanzu mun tara mata guda huɗu. Ni na gaji bazan iya wahala ba.”
“Ai ba kai zaka tsayarwar da kan ka haihuwa ba Allah ne, ka’ide abinda zaka haifa a rayuwar ka babu kyau saboda Allah ne yake bayarwa ba kai zaka zaɓawa kan ka ba. Dan haka ki jira lokaci kawai, amma baza ki haihu da wuri ba sai Ayda tayi kamar yadda Ayan yayi in sha Allah.”

Ta kwanta a jikin sa tace, “to Allah yasa. Ga rigimar Ayan isata take yi, yayi ta kuka kara dalili.”
“Wannan kuma ke ya gada har yanzu haka kike.”
“Kace kaima na sha baka haushi ko?.”
“Eh babu laifi kina bani, musamman in ban yi miki komai ba ki fara yi min kuka.” Manal tayi dariya tana sake gyara kwanciya a jikin sa yace, “kinga ba kwanciya zaki ba, tashi zaki mu tafi kafin wannan yaran albarka nuna mu su farka mun yi abinda zamu yi. Tashi don Allah.”

Ta kalle shi tace, “ƙarfe tara na dare fa.”
“Zamu mori lokaci sosai, ke kan ki kin san yau ɗin ai ba ta wasa ba ce” ya faɗa yana tashi tsaye ya ɗauki Ayda ya tafi da ita ɗakin ya kwantar da ita ya dawo ya ga Manal ɗin a inda ya barta. Ya tartare hannun rigar sa yace, “Wulaƙanci ko? To bara ki ga” ya faɗa yana ɗaukar ta tana dariya ya shiga da ita ɗakin sa.

BDƘB3P50

Washe gari bai tashi da wuri ba sai gab da sallar azahar, a firgice ya tashi ya shirya da sauri ya fito falo ya tarar da Manal a tsaye tana waya ya kalle ta yace, “zan fita.” Ganin a yadda ya fito sai ta kashe wayar tace, “lafiya?.”
“Ina zuwa sauri nake” ya faɗa yana fita da sauri.

Bata yi tunanin komai ba ta cigaba da abinda yake yi. Kusan awa ɗaya da fitar sa sai gashi ya shigo bayan sa wata mata kyakykyawar mace mara mai jiki da fatar ta kamar ta larabawa. Manal na zaune taji yana cewa, “shigo mana.” Ta shigo tana kallon Manal da take zaune da Ayda a hannun ta.

Manal kallon sa take yi tana kallon baƙuwar ta miƙe da murmushi tace, “sannu da zuwa.” Matar cikin iyayi ta miƙawa Manal hannu alamun su gaisa, Manal ta bata hannu suka gaisa cikin murmushi ta karɓi Ayda cikin hausar ta da bata fita sosai tace, “sunana Zainab.” Manal da murmushi tace, “Ni kuma Manal.”

Dr Zainab tace, “wow! Nice name.” Ta kalli Ayda tace, “beautiful baby.” Manal ta miƙe ta je wajan fridge ta kawo mata ruwa da lemo da glass cup ta ajjiye mata. Dr Zainab ta kalli Adnan tace, “Matar ka kyakykyawa.”

Yayi murmushi yana zaune bai motsa ba. Kallon Manal yayi yace, “ki kaita ɗaki ta huta in anjima tazo taci abinci.” Dr Zainab tayi murmushi tace, “Thanks you handsome.” Jin abinda tace sai Manal ta kalle ta sannan ta kalle shi suka haɗa ido sai ya ɗauke idon sa.

Karɓar Ayda Manal tayi ta bawa Adnan ita sannan ta raka ta ɗakin da yake kusa da nata tace, “bismillah.” Ta kalli Manal tana murmushi tace, “na gode sosai.” Manal bata ce komai ba ta fito zuwa falon. Tana fitowa ta same shi a tsaye ya bata Ayda yace, “sauri nake yi yanzu zan dawo.”
“Ko abinci baka ci ba.”
“Yanzu zan dawo” yana faɗa ya fita ta bishi da kallo.

Dr Zainab ko da tayi wanka kwanciya tayi bata fito ba sai bayan la’asar, ta fito cikin doguwar riga ta shan iska dan sisirin hannu ce da ita kamar vest, kanta babu hula ta ɗaure gashin kanta kamar wacce take a gidan ta. Tana zama a falon Adnan yana shigowa ya zauna suna hira da ita a falon, da kansa ya kawo mata abinci dan bai ga Manal ba.

Ayan yana kusa da ita tana ta yi masa wasa suna hira da Adnan cikin harshen turanci suna dariya. Manal tunda ya jiyo dariyar su gaban ta faɗi,ta fito tana kallon su cikin wani irin abu da yazo zuciyar ta ganin ta zaune daf dashi sai Ayan da yake tsakiyar su kai kace mata da miju ne. Wani irin kallo take yiwa Adnan tana murmushi tana kuma kai hannun ta jikin sa.

Manal ta daure ta ƙaraso da sallama Dr Zainab ta kalle ta cikin harshen turanci tace, “Madam kin fito?. Na tashi tun ɗazu har naci abinci, mijin ki ya dawo yana taya ni hira.” Manal tayi murmushin yaƙe ta kalle shi suka haɗa ido ta kawar da kai ta zauna a falon zuciyar ta a cushe ganin yadda take masa dariya shima yana sakar mata fuska kamar ba shi ba.

Zaman wajan ya ishe Manal sosai ta tashi tsaye da Ayda a hannun ta ta wuce ciki ɗaki, tayi tunanin zai biyo ta amma bata gan shi ba tana dai jiyo tashin muryar ta. Sai gab da magriba taji shigowar sa ɗakin ta ya kalle ta yace, “Manal zamu je asibiti da Dr Zainab, zamu dawo zuwa anjima.”

Manal ta kalle shi tace, “Sai kun dawo.”
“Na manta ban faɗa miki ba, a nan zata kwana duk dare zamu dawo tare.” Tayi murmushin takaici ta ɗaga kai shi kuma ya fita.

Haka ta gama zaman ta a gidan babu walwala zuciyar ta a cushe, basu dawo ba sai goma da arba’in na dare, zuwa lokacin ta gama zuwa wuya saboda ɓacin rai da kishi mai tsanani. Dr Zainab tana ganin Manal tace, “barka dai Madam, mun dawo.”
“Sannun ku da zuwa” ta amsa ba yabo babu fallasa.

Ɗaki ta shiga itama Dr Zainab ɗin ɗakin da aka bata ta shiga. Waya ya yiwa Manal yace tazo ɗakin sa ta fito tana shiga ya kalle ta yace, “Yauwa ki bata abinci, a nan zata kwana, maybe sai jibi ma zata tafi.” Kallon sa take yi bata yi magana ba, ganin irin kallon da take masa sai yace, “baki ji abinda nace ba ne?.”
“Naji.”
“Amma ki ka tsaya kina kallo na baki yi abinda na ce ba?.”
Manal ta gyara tsayuwa tace, “amma wacece ita?Meyasa baka faɗa min zuwan ta ba?, sannan meyasa baka ce min a nan zata kwana ba?.”
Da mamaki yake kallon ta yace, “Yanzu ai na faɗa miki ko?. A nan zata kwana ki bata abincin da zata ci yanzu.”

Manal ranta ya sake ɓaci, kishi yana sake azalzalar zuciyar ta tace, “ina matsayin matar gidan nan ace an kawo ɓakuwa cikin gidana zata kwana ban sani ba?, sai dai kawai na ganta ace min kwana zata yi, hakan daidai ne?.” Ya kalle ta da mamaki abinda tace ya ce, “amma ai na faɗa miki yanzu ko?. Meyasa ki ke son maimaita magana ɗaya?, meyasa ki ke son mayar da ƙarami babba?.”

“Wannan dai kamar wulaƙanci ne ai. Wacece ita da zata zo har cikin gidana tana zama da mijina a falo tana hira kamar matar ka?.” tsaki yayi kawai bai ce komai ba ya fita ya bar mata wajan gudun kar ta saka shi magana ga baƙuwa suna da ita.

Da kansa ya kai mata abincin ya same ta a zaune a falo da kayan bacci riga da wando, wandon iyakacin sa guiwar ta gabaɗaya fararen ƙafar ta a waje suke. Ta fara cin abincin ya zauna suna tattauna batun aikin su. Manal ta fito sake ganin su a haka ga kayan da yake jikin Zainab ɗin, hakan ya sake ɓata mata rai sosai ta danne ɓacin ranta a lokacin dr Zainab take dariya harda dukan kafaɗar Adnan.

Rantse ido Manal tayi ta zo ta wuce su bata ce musu komai ba ta shiga ɗaki. Dr Zainab ta kalle shi tace, “matar ka tana da kirki sosai.” Yayi murmushi kawai bai yi magana ba. Ya jima a wajan ta suna hira kafin ya tashi ya shiga ɗaki itama ta shiga ɗakin ta bayan ta leƙa Manal ta yi mata sai da safa.

Manal saboda takaici bata ma sake zuwa ma inda yake ba a haka suka kwana tana ɗakin ta yana ɗakin sa. Ƙarfe baƙwai na safe ta tashi ta shirya Ayan ya tafi makaranta, tana kwashe kayan da Ayan yaci abinci taji motsin fitowar sa. Juyowa tayi ta kalle shi taga fuskar a ɗaure tace, “ina kwana.” Ya amsa shima babu fara’a sannan yace, “ki haɗa breakfast yanzu zata tafi” yana faɗa ya wuce ta.

Bata ƙi yi ba ta dafa ta ajjiye ta koma ɗaki. Tana jiyo motsin baƙuwar sai da ta gama cin abincin sannan ta shiga wajan Manal ta yi mata sallama suka fita. Ran Manal ya kai ƙarshe wajan ɓaci haka take a ɗaki har ya dawo lokacin ƙarfe goma na safe. Tana jin motsin sa bata fito ba shima bai je inda take ba. Shirin aiki yayi ya zauna yaci abinci bai nemi inda take ba ya fita zuwa wajan aiki dan kar ma ta ɓata masa rai.

Zuciyar Manal kamar ana tafasa ta a haka ta wuni a gidan, ranta a ɓace kishi yana azalzalar zuciyar ta tana ganin kamar Adnan ya gama wualaƙanta ta.

Da yamma ta fita wajan school bus ɗin su Ayan a nan taga motar Huzaifa zata wuce ta ƙofar gidan, ganin Manal ɗin a bakin gate sai ya tsaya ya sauke glass kafin yayi magana ta riga shi tace, “Yanzu Yaya ba dan ba ganka ba wucewa zaka yi?.” Zai yi magana tace, “ai kawai ka shigo mu gaisa” ta faɗa tana komawa ciki tana riƙe da hannun Ayan.

Huzaifa ba yadda zai yi ya shiga gidan ya zauna a falo tana murmushi tace, “yanzu da ban ganka ba sai ka wuce ko mu gaisa ko Yaya?.” Yayi dariya yace, “gaskiya ban yi niyar shigowa ba, Allah yayi dai sai na shigo mun gaisa.” Ta zauna tace, “ina yini.”
“Lafiya lau, ya gidan?.”
“Lafiya lau Yaya, ya Anty da ɗana?.”
“Lafiya lau suke.” Ya riƙe hannun Ayan da yake tsaye a kusa dashi yana tambayar sa ya makaranta.
Chapter 80 · 0% Book details