Sashe 27
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manal bata ce komai ba ta jingina da kujera ya kalle ta ya ce, "yau zamu fita da daddare mu je farkon estate ɗin nan mu dawo." Manal tayi kamar zata yi kuka tace, "wallahi gajiya nake yi, ni bana son fitar nan."
"Dole kuwa sai mun yi, tafiyar shine zai saka ki samu sauƙin doguwar labour, zai rage miki wahala."
"Daman ai wahala ake sha in za'a haihu." Cikin son ya kwantar mata da hankali ya ce, "A'a ai kowa da yanayin yadda Allah yake bashi, yadda kike da ƙoƙarin ibada da addu'a na tabbatar Allah zai baki haihuwa mai sauƙi, sai dai ma ki haihu baki san kin yi ba."
Manal ta sauke numfashi jin yadda yayi maganar a nutse ba tsokana sai ta yarda tace, "to Allah yasa hakan, amma ni tsoron nake ji. Anty Samira baban yayar su Surayya ta sha wahala wajan haihuwa, daga ƙarshe ta rasu" ta faɗa cikin rauni da nuni da gaskiyar abinda yake zuciyar ta kenan. Hannun ta ya riƙe ya ce, "shiyasa nace miki ko wacce mace da yadda Allah yake bata sauƙin haihuwar, ita ajalin ta ne a wajan shiyasa ta sha wahala sosai, ke meye na jin tsoron bayan kina dani? Kar ki manta fa ni likita ne." Ta kalle shi ido na kawo ruwa tace, "Amma ba likitan haihuwa bane ba ai."
Ganin zatayi kuka ya ce, "amma zan iya karɓar haihuwar ki, dan haka kar ki damu ina gefen ki daga lokacin da zaki haihu har Allah ya sauke ki lafiya." Ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tace, "in kana kusa dani bazan sha wahala ba?."
"Baza ki sha wahala ba in sha Allah, zan dinga yi miki addu'a ina shafa miki, gashi kuma blood sugar ɗin ki ya sauka yanzu kin ga babu wannan damuwar."
Motsi taji alamun ana shigowa ta kalle shi tace, "baka kulle babban falon ba? Naji ana shigowa."
"Surprise!" Aka faɗa ana shigowa falon da suke, duk suka kalli wacce ta shigo ba kamar Bebi da yake kallon ta.
Rumana tayi murmushi tace, "gani nazo." Ya ɗauke kai daga kallon ta tace, "Sallamar kenan?."
"Kai baza ka gane bane, wallahi nayi kewar ganin ka sosai, in na kira ka a waya ko ɗauka baka yi" ta faɗa tana zama a kusa dashi ya zama sun saka shi a tsakiya ita da Manal.
Yafi zaka very close da Manal amma ita Rumana kafaɗar ta tana dukan tasa saɓanin Manal da kanta yake kafaɗar sa. Kallon Manal yayi yaga shi take kallo ya kalli Rumana ya ce, "Ke wai yaushe zaki hankali ne?." Rumana tace, "dan na zauna kusa da kai shine ka ke cewa haka? To na matsa" ya faɗa tana matsawa gefe tana kallon Manal da take kallon ta.
"Sannu Amarya" ta faɗa ba tare fuska a haɗe tana kallon Manal ɗin da itama ita take kallo. Kafin Manal tayi magana tace, "Beb wallahi nayi kewar ka sosai, amma kai tunda ka kira ni farkon zuwa na kace ya jikina baka sake min waya ba, amma na san kana yi min addua."
Shi Bebi wani iri yake ji a jikin sa in tana yi masa magana a gaban Manal sai ta ɗaure shi da jijiyoyin jikin sa, saboda bai taɓa bawa Manal labarin abinda yake tsakanin sa da Rumana ba. Canja maganar yayi ya ce, "Ya mutanen Abuja? Kowa yana lafiya?."
"Lafiya lau Beb, Mun zo duba jikin Abba ne." Ya girgiza kai baice komai ba Manal ta tashi zaune sosai Rumana ta kalle ta tace, "Amarya ina sannu baki amsa ba."
Manal tace, "ban ji ki ba, kin zo lafiya?." Rumana tayi wani irin murmushi tace, "lafiya lau, i'm sorry hankalina yayi wajan Beb mun jima bamu haɗu bane, kin san kuma akwai shaƙuwa sosai a tsakanin mu." Manal ta girgiza kai tace, "na ga alama."
Jaka ta buɗe ta ɗauko wata a cover tace, "Beb na kawo maka kyauta" ta faɗa tana buɗewa sai ga azurfa mai kyau a ciki, ta ciro ta riƙe a hannun ta kafin ta riƙo hannun sa da niyar saka masa. Da hanxari ya ƙwace hannun sa yana yi mata wani irin kallo zai yi magana ta riga shi tace, "kyauta na kawo maka fa, ko baza ka karɓa ba ka bari na saka maka in yaso sai ka cire ka dawo min da ita. Don Allah kar ka mayar da hannun kyauta baya, na jima ina dakon ta kawai dan na baka ita matsayin tsaraba" ta faɗa a raunane tana kallon sa.
Manal ya kalla yaga kallon su kawai take yi duk sai yaji babu daɗi a zuciyar sa kamar mara gaskiya ya kalli Rumana ya ce, "Shikenan bani, na gode" ya faɗa yana miƙa mata hannu ta bashi azurfar ya ajjiye a gefe. Manal ta kalla sai a lokacin ta lura da cikin jikin ta kulle ido ta buɗe ƙirjin ta yana bugawa sosai, tana tunanin anya zata iya haƙuri da Mama take faɗa mata?.
Sake kallon Manal tayi suka haɗa ido Manal taƙi ɗauke ido daga kanta kuma bata ce komai ba sai Rumana tace, "ashe mun kusa samun Baby." Babu wanda ya bata amsa Manal ta kalli Bebi shima hankalin sa yana kanta dan yaga ta tamke fuska kamar ba ita ba duk sai ta sake ruɗa shi, ya diririce ya rasa ina zai kama ba tare da ya san dalilin hakan ba.
"Lafiya ki ke partner? Akwai abinda yake damun ki ne?" Ya faɗa yana kallon ta da murmushi. Manal ta girgiza kai tace, "me zai same ni? Kawai ina kallon dramar ku ce ta burge ni" ta faɗa tana kallon Rumana. Rumana ta maimaita drama a zuciyar ta, lallai ma wannan yarinyar nan Manal bata da mutunci, wato ma drama ce ita ba ma kishi take ba.
Manal yunƙurin tashi take yi ya tashi da sauri ya ya riƙe ta ya miƙar da ita tsaye ya riƙee hannun ta, Manal ta kalle ta tace, "Ina zuwa yanzu zan dawo" ta faɗa tana fara tafiya shi kuma yana riƙe da ita har cikin ɗaki.
Suna shiga ɗakin taga yana kallon ta kamar wanda yayi wani laifi, tsoro ya bayyana sosai a kan fuska sa, Hakan da ta gani ne ya saka zuciyar ta take rawa akan sa da kuma Rumana, amma bata ce masa komai ba ta share batun kawai ta shiga banɗaki.
Wajan Rumana ya dawo a fusace ya kalle ta ya ce, "har cikin gidana, a gaban matata zaki zo kina yi min wannan shirmen tsabar wulaƙanci? Ke baki da hankali ne baki san ya kamata ba?." Rumana ta tashi tsaye tace, "me nayi? Zuwan nawa ne matsala ko kyautar da na kawo maka?."
"Zuwan ki gidan nan bani da matsala dashi, amma meyasa lallai sai kin nunawa matata kamar ke wata ce a wajena? Akan me?."
Rumana tace, "ni ba wata ɗin bace a wajan ka?." Ya Harare ta ya ce, "wacece ke ɗin to?." Idon ta ya ciko da hawaye tace, "ni ka ke cewa wacece ni?."
"Matsayin Kausar kike a wajena, bayan wannan babu wani abu na faɗa miki ba yau ba jiya ba. Ki shiga hankalin ki, ko nan gaba kar ki sake maimaita wannan kuskuren a ko ina. Kar hannun ki ya sake zuwa inda nake, kar ki sake zuwa ki ganni a waje ki zauna a kusa dani, ki tsaya a matsayin ki."
Rumana ta kalle shi tace, "har yanzu baka canja ra'ayin ka a kaina ba? Baza ka tausayi min ba duk da ciwon da na samu ta dalilin son da......" ya dakatar da ita saboda kar Manal ta jiyo ya ce, "ya isa malama! Na faɗa miki kar ki sake wannan kuskuren" yana faɗa yana komawa ɗakin Manal ya tarar ta fito daga banɗakin a lokacin.
Ya kalle ta ya ce, "magriba tayi, in mun yi sallar i'sha sai mu fita ko?."
"Ta tafi ne?."
"A'a tana nan." Manal ta kalli fuskar sa tace, "Sai naga ka canja, lafiya?."
Bebi yace, "babu komai." Bata ce komai ba ta fito falon sai ta tarar da Rumana bata nan. Kallon bayan ta tayi ta ganshi ya fito daga ɗakin tace, "kace min tana nan."
"Ta tafi kenan." Kallon idanun sa take yi ta matso kusa dashi sosai tana kallon sa tace, "na taɓa tambayar ka meye tsakanin ka da ita kace min ƙanwar kace, tun a lokacin na faɗa maka ba kamar su Mimi take jin kanta ba. Matsayin ta yafi na su Mimi a wajan ka, ba iya ƙanwar ka bace ba. Dan na tabbatar ko Yaya Farida baza ta yi abinda tayi maka abinda tayi yanzu a gabana ba. Ya maganar take?."
Ta fahimci ya ruɗe duk da yana ƙoƙarin dannewa sai ta kawar da kai ta kalli gefe shi kuma ya ce, "babu komai, kawai tana rayuwar turawa ne ita a ganin ta hakan wayewa ce shine kawai." Manal ta sake kallon sa tace, "kenan kowa ma haka take masa kamar yadda tayi maka?." Bebi ya ce, "eh kusan hakan."
"Ka tabbatar hakan ne?."
"Haka ne mana."
"Bana so naji wani abun da ba wannan ba nan gaba." Yayi murmushi ya ce, "babu abinda zaki ji." Bata ce komai ba ta wuce shi ta shiga ɗaki ba dan ta amince da abinda yace mata ba.
Bebi ya bita da kallo yana jin wani iri a zuciyar sa, Allah ya sani yaso ya faɗa gaskiyar lamarin mata amma yanayin da take ciki ne baya son tayar mata da hankali shiyasa ya kawar da maganar, amma nan gaba zai faɗa mata wacece Rumana a wajan sa da kuma alƙawarin da ya ɗauka akan ta.
BDƘB3P15
Tafiya suke yi a hankali ta saka slippers kamar yadda aka saba suna tafiya a hankali yadda baza gaji ba. Sun saba suna tafiya tana magana amma yanzu tayi shiru tun daga lokacin da Rumana tazo shikenan walwalar ta ta ragu. Kallon ta yayi cikin hasken layin nasu ya ce, "yau kin yi shiru, bakya bani labarin komai."