← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 84

Sashe 67

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi dariya kawai baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba. In ya biyewa surutun ta baza ta bar shi yayi shiru ba. Ta sake kallon sa tace, "Gobe ina so zanje gida muna ta shirin bikin Yaya." Ya girgiza kai ya ce, "Allah ya nuna mana goben. Nima ɗazu Huzaifa yake min maganar nace ni zan faɗa masa ko shi ne zai faɗa min?." Tayi dariya tace, "gaskiya dai kai zaka faɗa masa." Ya kalle ta ta gefen ido ya ce, "bana son munafurci." Tayi dariya tana kallon sa yana murmushi ya kalle ta kafin ya saukar da ƙwayar idon sa ƙasa yana kallon ta ya ce, "wai yau kallon nan da ake yi min na meye ne?, Matso kusa dani ki faɗa min kallon na meye."

Manal ta sake yin dariya ta matsa kusa dashi kamar yadda yace ya kalle ta ya ce, "ina jin ki, kallon daga ina yake haka? me za’a bani ake kallona?." Ta sake yin murmushi tace, "kawai ji nake yau na naita kallon ka har sai na gaji." Yayi murmushi ya ce, "to ki fara mana, ki ta kallona har sai kin gaji ɗin." Murmushi tayi tace, “ai bazan gaji da kallon ka ba, kana da kyaun da idanuna baza su gaji da ganin ka ba” ta faɗa tana shafa fuskar sa wacce take ɗauke da murmushin da yake masa kyau in yayi. Ya yi hannun nata kiss ya ce, “duk kyauna ban ka ki ba, ke ce baza’a gaji da kallo bani ba. Kefa ko babu kaya a jikin ki kyau ki ke yi, ni kuwa bama kya iya kallon nawa balle ki ga kyaun.”

Fuska ta ɓoye a jikin sa yayi ƴar dariya itama dariyar take yi yace, “ko ba haka bane? Tsakanin ki da Allah kin taɓa ƙare min kallo ko sau ɗaya?.” Manal tace, “sau nawa kuma.”
“A’a ƴan mata, baki taɓa ba.” Dariya ta sake yi tace, “Allah kunya ka ke bani.”
“Aikin kenan.” Dariya kawai tayi bata ce komai ba ya riƙe hannun ta ta kalle shi taga Ayan yake kallo sai tayi shiru bata ce masa komai ba.

A kafaɗar sa ta kwanta haka kawai take jin farin ciki a zuciyar ta, in ta kalle shi sai taji daɗi sosai tana godewa Allah da ya bata shi a matsayin mijin ta.
"Partner zaka iya yi min kishiya?." Dariya ta bashi sosai ya dara yana girgiza kai ya ce, "kawai kice min duk wannan kallon tambayar da kike so ki yi min kenan, daman ni na san akwai wani abu a can ƙasa." Manal tace, "A'a wallahi, kawai tambayar ce tazo raina. Zaka iya haɗa ni da wata mace a duniya?."

"To yanzu me ya kawo wannan batu na ƙarin aure? Shekarar mu ɗaya da kwanaki da aure, wani abun kika gani da yake nuna miki zan iya ƙara aure ko ya ya?." Tayi murmushi ta ɗago tana kallon sa tace, "Allah ba haka bane, kawai ina so na ji." Ya taɓe baki yace, "to ni ban san me zance miki ba, ki adana tambayar ki zan amsa miki wani lokacin." Wayar sa ce tayi ƙara sai ya tashi ya ajjiye Ayan a gadon sa ya ɗauki wayar yana daga tsaye kafin ya kashe ya kalle ta yace, "Zan je nayi sallah daga nan zan je wajan Daddy, sai zuwa bayan i'sha dai zan dawo."

Ta ɗaga masa kai tana kallon idanun sa ya dawo kusa da ita ya manna nata kiss a goshi yace, "naga alama yau babu baccin dare ko?" Ya faɗa yana ɗaga mata gira yana dariya itama dariya ta tayi ya fita.

Kafin ya dawo tayi wanka dan da gaske soyayya take ji da ita ranar ta shirya cikin shigar da yake atampa ɗinkin riga da siket, siket din street mai tsaga ta baya, tsagar mai tsaho dan duk digagin ta a waje yake, rigar ƴar ƙarama bata da wani tsaho hakan ya bawa halittar ta damar bayyana a cikin kayan sosai.Abincin ta jera masa a dining da lemon da ta haɗa masa ta bar falon ta shiga ciki. Ba jimawa ta jiyo tsayuwar motar sa alamun ya dawo.

Shi kuwa shida Huzaifa ne suka haɗa a ƙofar gida shima yazo gidan sai suka shigo tare.

Sai bayan sun shiga falon Huzaifa yake kallon falon yace, "gaskiya ka samu ƙanwata a ɓagas, ka duba falonnan kamar yanzu aka gama yi masa fenti. Ina jin haushi wallahi, naso ace na wahalar da kai kafin na bana ita wallahi." Ya kalle shi gace, "yanzu ma sai ka kwace ta ai" ya faɗa yana ƙarasa wajan dining ya zuba abinci a plate ya dawo ya zauna.

Huzaifa yace, "baza ka yi min bismillah ba?."
"Ba gidan ƙanwar ka bane?." Jin hakan sai yayi dariya kawai ya tashi yaje ya zuba kamar yadda Adnan ɗin yayi ya taho da ruwa ya zauna yana ci. Adnan ya kalle shi yace, “tsabar rashin kunya wai Yaya ne yake zuwa gidan ƙanwa har yaci abinci, anyi asara.” Huzaifa yayi dariya yace, “kaga malam kar ka saka na ƙware, in kai kana ganin hakan ba daidai bane a wajena daidai ne.”
“Sai kai tayi ai.” Huzaifa yayi masa banza ya cigaba da cin abincin sa. A lokacin Manal ta shigo falon tana cewa, "to wai me zan maka ne? Sai kuka ka ke yi?" Ta faɗa tana kallon Ayan da yake hannun ta.

Dukkan su kallon ta suka yi jin ta fito tana magana. Bebi ya tsaya cak da cin abincin ganin yadda tayi kyau sosai cikin atampar da ta saka, tayi ɗaurin ɗankwali wanda ake turo shi gaban goshi, tayi ado da gashi ta baya fuskar ta dai ƙyalli take gashi ta zagaye laɓɓan ta da lips gloss.

Ganin Huzaifa a zaune sai tace, "lah Yaya yaushe kazo?." Murmushi yake yana kallon ta yace, "ina nan ina cin girkin ki." Tayi murmushi ta ƙaraso ta zauna tace, "naji dawowar ka amma ban ɗauka tare ku ke ba" ta kalli Bebi suka haɗa ido sai ya ɗauke kansa ya cigaba da cin abincin sa. Huzaifa yace, "bani Ayan ɗin" ta tashi ta yi ta miƙa masa shi ya karɓe shi ta dawo ta zauna Huzaifa yace, "yanzu nake cewa mijin ki ya samu garaɓasa da ya same ki, gaskiya kina ƙoƙarin gyaran gidan nan sosai. Gida kamar yau aka yi shi?."

Tayi dariya tace, "aikin ai babu yawa yaya, duk da akwai mai taimaka min."
"Gaskiya kina ƙoƙari sosai, ga abinci mai daɗi." Tayi dariya tace, "Ina Anty? Kwana biyu bamu yi waya ba, jira nake kawai ace ta sauka." Huzaifa yace, "ana nan ja dai, ɗazu ma Mama ta kira ni take cewa bata haihu ba nace zata haihu basu sani ba ne?." Manal tace, "Allah ya raba su lafiya." Ya amsa da amin.

Huzaifa ya ajjiye abincin da yake ci yace, "hanya ce ta biyo dani na shigo mu gaisa, da alama mijin ki yaji haushin zuwan sai harara ta yake ko magana ma yaƙi yi." Ta kalli Adnan da kamar ma bai san suna nan ba abincin sa yake ci hankali kwance.

Manal tace, "Haba shima zai ji daɗin ganin Yayan matar sa.” Huzaifa yayi dariyar shaƙiyanci yace, “dan rashin kunya kuma ko gaishe ni bai yi ba, abincin ma da kaina na zuba.” Manal tayi dariya tace, “ahh gaskiya bai kyauta ba.”
“Ƙyale shi, baya neman albarka ta ne. Amma zan nuna masa ikon da nake dashi akan ki.” Manal murmushi take yi dan ta fahimci tsokanar sa yake yi tace, “Na gode sosai Yaya, Yaya Mubeena ma ɗazu tace min ai kaje ka gaida Mama."
"Naje jiya mun gaisa an kuma duba blood sugar ta, har ta bani wani dambun kaza mai shegen daɗi."

Manal tayi dariya Huzaifa ya tashi ya zo har inda take zaune ya bata Ayan sannan ya kalli Adnan yace, "Bebi zan wuce." Ya kalle shi baice komai ba Huzaifa yayi dariya ya kalli Manal yace, "ƙanwata assalamu alaiki" ya faɗa yana miƙa mata hannu alamun su gaisa.

Manal ba tare da tunanin komai ba ta saka hannun ta a cikin nasa suka gaisa tana dariya tace, "a gaishe Anty." Ya zare hannun sa yana cewa, "zata ji. kin san Daddy yace min zuwa jibi zai zo, Ayra mutuniyar ki sai murna take tace a gidan nan zata zauna."

Manal tace, "kuma ɗazu mun gaisa dashi amma bai faɗa min ba. ina nan ina jiran Ayra aminiya ta."
“Wallahi kuwa sun kuwa zuwa saboda bikin Mubeena." Magana yake yana tafiya tana bin bayan sa suna hira har yaje bakin ƙofar falon sannan yayi mata sallama ya fita.

Tana juyowa taga baya falon ga abincin da ya gama ci ban ya bar kayan a wajan ya kuma tafi da Ayan. Kayan ta kwashe ta shiga ciki ta ajjiye ta fito taga abincin ya ƙare tayi hamdala dan bata son yayi ragowa shiyasa take yin kaɗan. Ruwan cucumber da apple ɗin da ta saba tasha ta zuba a kofi mai ɗan girma ta fito tana sha ta shiga inda yake cikin son burge shi da shigar da tayi saboda shi.

BDƘB3P42

A zaune ta hango shi ta ƙarasa ta zauna a kusa dashi tana shan ruwan lemon. Kafin ta yi magana ya kalle ta ya ce, "Meyasa kike yi min abinda bana so ne? Sai raina ya ɓaci nayi fushi kuma kizo kina complain akan na cika yawan fushi da sauran su. Meyasa bakya gujewa abinda zai saka zuciyata a ciki. fushin?." Manal ta kalle shi da mamaki ta haɗɗiye abinda yake bakin ta tace, "me nayi?." Ya kalle ta yace, "baki san ma abinda kika yi min ba kenan?." Ta kalle shi tace, "to naga a yadda muka rabu da zaka fita, ta ya ya zan san abinda nayi maka."

Ya girgiza kai ya ce, "da kika fito kika ganni da Huzaifa meyasa baza ki dawo ki saka mayafi ba? Kika zauna a gaban sa da wannan shigar a jikin ki har da zuwa kusa dashi ki bashi Ayan. Sannan dan tsabar wulaƙanci harda wani gaisawa dashi ko?." Mamaki ya bawa Manal ta ajjiye glass cup ɗin hannun ta tana kallon sa tace, "Partner ka manta waye shi a wajena ne? Yayana ne fa na jini."
Chapter 67 · 0% Book details