Sashe 63
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe ido take yi ta dafe kai tace, "kaina ciwo yake min, Wallahi bayana ya riƙe sosai." Yayi ƴar dariya tace, "ba ke kika ce min bazan iya ba?" Ya faɗa yana ɗora mata Ayan a jikin ta tare da ciro nonon da kansa ya saka masa a baki ita kuma ta tallafe kansa ya kalle ta yace, "har yanzu bakya riƙe shi sosai, in kina masa wannan riƙon zai dinga gaggarawa yana zuwa kunnen sa" ya faɗa yana ɗago hannun ta ya daidai ta mata yadda zata riƙe shi.
Manal ta jingina da fuskar gadon ta rufe ido, a gajiye take sosai ta sha wahala a hannun sa fiye da tunanin ta, kiss ya yi mata a baki ta kalle shi ya ɗaga gira yace, "ya muje round seven ne?." Ta bata fuska kamar zatayi kuka tace, "Allah ka bani wahala soaai, na gaji bayana ciwo yake min Gashi yunwa nake ji." Yayi murmushi yace, "nima na gaji, amma dole ce ta saka na kasa haƙura dake. Ji nayi kamar an canja min kw kin dawo sabuwa tal kamar ranar da aka kawo min ke." Ta kalle shi suka haɗa ido sai yayi dariya tunawa da wannan daren ita kuma ta kulle idanun ta cikin jin nauyin sa.
"Mai kunyar matata, har yanzu kin kasa daina kunya ta hakan kuma yana burge ni sosai. Kin san dai jiya daren nan ya zama na musamman, dan yaso yafi na farko ma, kawai dai dan na farko na farko ne amma da sai nace wannan yafi na farko. Saboda wannan da taimakon ki ya zama na musamman, Wancan kuwa kamar matacciya haka kike a kwance."
"Allah ka daina faɗa min bana so."
"Allah sai na faɗa, kin ji daɗi naji daɗi, na farko kuma kin sha wahala naji daɗi shine fa kawai." Manal ta rantse ido yayi dariya yaja hancin ta yace, "gulamammiya kawai." Tayi murmushi ta zare Ayan daga jikin ta ta bashi shi tace, "ni ka ɗauke shi ku fita bacci zanyi"sai kuma ta kalli Agogo tace, "Wallahi ina da class yau, Gashi har lokacin ya wuce."
Ya kalle ta ganin da shagwaɓa tayi maganar yace, "matata ko babu culinary school ita ɗin professional chef ce, jiya ma na shiga page ɗin ki na Instagram naga ana ta missing posting girkin ki." Ta kwanta a kafaɗar sa tace, "ina jin daɗin goyan bayan nan da ka ke bani." Ya saka hannun sa a rigar ta yace "in ban baki goyan baya ba wa zan bawa?, duk abinda kike da buri zan cika miki shi in sha Allah." Hannun sa ta doke tace, "ka bari bana so."
"Ni ina so kuma."
"Allah bana so na gaji" ta faɗa tana kallon sa kamar zata yi kuka. Shima ya kwaikwaye ta yace, "Allah ina so ban gaji ba." Suka yi dariya a tare ya tashi ya kwantar da Ayan yace, "taso mu je nayi miki wanka ki ci abinci" ya faɗa yana riƙo ta ta tashi tsaye ya kaita har banɗakin.
Wanka kuwa yayi mata ya fito da ita ya shirya ta ya riƙo hannun ta suka fito bayan ya kai Ayan falon. Abincin ya kawo mata ya ajjiye ta ɗauki tea tana sha yace, "yau ki ci girkin Adnan." Ta ɗauki dankalin tana ci tace, "wannan har wani girki ne? Ai abu ne mai sauƙi." Bai ce komai ba tace, "yau dai na ciri tuta an yi min girki, gaskiya na yarda yau ɗin ta musamman ce." Yayi dariya yace, "giyar amarci ne ya saka nayi miki ban ma san nayi ba." Ta kalle shi tace, "ni na sani, in ba dan haka ba ni na isa?."
"Har kin yi yawa, ai duk abinda ki ke so zan yi miki ranki ya daɗe."
Kamar waccs ta tuna wani abu da sauri ta kalle shi tace, "Partner na shiga uku." Shima da sauri yace, "meye?."
"Partner bamu ɗauki ko wanne mataki ba kar nayi ciki a jiya fa." Ya wara ido yace, "ai kam zaki iya, dan jiyan nan ni kaina na san daƙyar ba a samu rabo ba."
Ta ajjiye plate ɗin abincin tace, "Innalillahi, na shiga uku partner, wallahi bana son sake haihuwa yanzu, ka taimaka min a san abinda zam yi." Ganin da gaske hankalin ta ya tashi yayi dariya yace, "wasa nake miki, kar ki damu baza ki samu ciki yanzu ba in sha Allah."
"Dame ka dogara?."
"Ke dai ki yarda mana, kar ki manta ni likita ne fa. Zaki iya samun ciki a duk sanda Allah ya nufa amma in sha Allah da sauran lokaci."
Ta sauke ajiyar zuciya tace, "har naji daɗi, sai na huta zan haihu in sha Allah." Ta fada tana cigaba da cin abincin. Yayi dariya yace, "matsoraciya ce ke ai." Ta taɓe baki tace, "na faɗa maka ba ka san me ake ji a labour room ba" ta ɗago tana kallon sa tace, "a other room kafi kauri." Dariya yayi soaai yace, "baza ki daina faɗar maganar nan ba ko?." Manal tace, "ai gaskiya ne, inda ka san wahalar da ake sha baza kace min matsoraciya ba."
Yayi dariya yace, "gaskiya ni other room ne ɓangarena, haƙƙin da Allah ya ɗora min nake sauke miki." Ta taɓe baki bata ce komai ba.
"Ina so gobe zan kai Ayan circumcision."
"Ai gwara ka kai shi ayi masa ya huta, bana so naga sai yaro ya girma ace za'a yi masa." Ya bita da kallo yace, "ahhh kenan daman kin san meye circumcision ɗin?." Manal tayi masa hararar wasa tace, "ai tunda na san wannan kalmar mai take nufi na daina faɗa da hausa, kunya nake ji a gaban mutane a dinga faɗa babu sayawa."
Bebi yace, "to sai meye dan ance kaciya? Hausawa suna sayawa suce shayi ko?." Manal tace, "wallahi bana so, gwara da turancin yafi."
"Meye na kunyar?."
"Oho min" ta faɗa tana dariya. Yayi murmushi yace, "ke komai kunya yake baki ai." Manal tace, "naji, da kace bani da kunya gwara kace ina da kunya." Murmushi yayi suka cigaba da hira yana tsokanar ta.
Tana gama cin abincin ta kwashe kayan ta kai kitchen ta shiga ɗaki ta tarar Ayan ya tashi ta ɗauke shi tayi masa wanka ta shirya shi suka fito falo suka zauna yana hannun ta. Shigowa falon yayi ta kalle shi ganin bai shirya fita ba tace, "baza ka fita ba?." Zama yayi kusa da ita yace, "babu inda zan je, yau a gidan na zan yini."
Manal tace, "babu aikin kenan?."
"Akwai mana, kawai bazan fita bane a gida zan zauna." Ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba. Agogo ya kalla yace, "lokacin sallar la'asar har ya kusa, zan je na gaishe da Mummy na dawo."
"Bana jin daɗin jikina da nazo mun je tare." Wani irin kallo yayi mata yana murmushi yace, "ki yi zaman ki naje na dawo, nima bana so ki fita nafi so ki huta saboda kar ki gaji kafin anjima."
Ta kalle shi tace, "me ka ke nufi?."
"Kin fini sani."
"Koma me ka ke nufi a gajiye nake wallahi, jikina ciwo yake min."
"Ki sha magani" ya faɗa yana matsawa kusa da ita yayi mata kiss a goshi ya tashi tsaye yace, "zan cewa Mummy kina gaishe ta" ta ɗaga masa kai ya fita da sauri.
Bayan Kwana biyu.
Manal tana zaune akan kujera Bebi yana kwance yayi matashi da cinyar ta yana duba wayar sa ita kuma tana wasa da gashin fuskar sa. Sallama akayi tare da shigowa inda suke. A tare suka amsa ya kalli inda aka shigo ya tashi zaune yana bin wacce ta shigo da kallo itama tana kallon su.
Rumana ce ta shigo ta rame fuskar ta kamar an saka sirinji an zuƙe ta, ta koma ƴar ƙarama kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar da tayi doguwar jinya. Murmushi Rumana tayi wanda sam bai mata kyau ba saboda ramar da tayi. Rumana ta ƙaraso ta zauna bayan ta ɗauki Ayan tace, “Sis barka da yamma.” Manal tayi murmushi tace, “barka da zuwa, ina yini.”
“Lafiya lau, nazo babu sanarwa.”
“sai kace wata baƙuwa?, ya jikin naki?.”
“Jiki alhamdulillah, sallama nazo nayi mu ku zan koma Abuja.”
Bebi kallon ta yake tunda ta shigo cikin tausayawa, yasan duk a kan soyayyar sa ta koma haka, bai san adadin raɗaɗin da take ji a zuciyar ta ba amma ya tabbatar da raɗaɗin bawai kaɗan bane yana d zafi sosai. Ganin yana kallon ta sai tayi murmushi tace, “Barka da yamma Bebi.” Maimakon ya amsa sai yace, “haka kika zaɓarwa kan ki? Kalli yadda kika koma don Allah, kina shan magani ma kuwa?.”
Rumana tayi murmushi tace, “nifa naji sauƙi wallahi.”
“Ita wannan ramar daga ina ta zo?.”
“Bana ce ba, kawai nima naga ina ramewa ne amma bawai dan akwai dalilin ta ba.”
Bebi yace, “Ruman kar ki min ƙarya, ke kin san na san halin ki, babu ta yadda za’a yi ki ce min wai kema baki san daga inda ramar nan tazo ba. Damuwar da nake cewa ki cire daga ranki ce kika kasa har ta haifar miki da wannan ramar.”
“Ba yadda ka ke tunani bane wallahi.”
Kallon ta yake yi kafin yace, “hmmm! Ki sausautawa kan ki dai, in ba haka ba damuwar illa zata yi miki. Na maimaita miki maganar nan na sake maimaita miki amma bakya ji, ai shikenan Ruman ki yi abinda ki ke so.” Ganin yadda yake mata magana cikin tsantsar nuna damuwar sa a kanta sai tayi murmushin jin daɗi tace, “balle ma ba abinda ka ke tunani bane. Ƙanwata mijin ki baya so wani abun ya same ni.” Manal tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Tashi yayi ya fita ya bar su su biyun a zaune, ba wata hira suke ba sai maganar tazo bata jima ba ta miƙe tsaye da niyar tafiya.