Sashe 61
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata ce komai ba tana ƙirjin sa ya saka hannu ya riƙe bayan ta sosai, ya kai bakin sa daidai kunnen ta yace, “i’m sorry! i’m sorry!! I’m sorry!!!. I’m sorry Partner na san nayi ba daidai ba, ki ya yafe min.”
Tana jikin sa sosai dan ya matse ta a jikin sa tana jin duk abinda yake faɗa a kunnen ta tayi shiru bata ce komai ba, ya ɗago fuskar ta daga jikin sa yana kallon ta yace, “kice wani abun mana, na sha wahala kafin na gano inda kike, na tabbatar da ke ɗin rayuwata ce, in babu ke rayuwata tana cikin wani yanayi mara dadɗ. Na shiga damuwar rashin ki sosai, kice wani abun mana Partner, nayi kewar maganar ki” ya faɗa yana matso da bakin sa kusa da nata yayi mata kiss ya sake kallon ta yace, “talk to me please.”
Bata ce komai ba ya sake mayar da ita jikin sa yana sake riƙe ta sosai yace, “nayi kewar ki.” Nan ma bata ce masa komai ba ya ɗago ta daga jikin sa yana kallon ta ganin idon ta ya ciko da hawaye yace, “kar ki kuka don Allah, ki mayar da hawayen nan bana son ganin su partner .” Sakkowa hawayen suka yi daga idanun ta yace, “oh my god! Nace ki yi haƙuri fa meyasa baza ki haƙura ba? Hakuri nake baki fa partner.”
Goge idon ta tayi ta kalli Ayan da yake kallon su kamar ya san abinda ake yi ta kalle shi kamar zata yi magana sai ta fasa, yace, “don Allah ki yi magana kar ki fasa.”
“Cewa zan yi ka ƙyale ni.”
“bazan iya ƙyale ki ba, me kike so nayi miki kuma Na baki haƙuri ya kamata ace komai ya wuce.”
Kallon sa tayi tare da murmushin tace, “ba kace saboda Ayan ka zaɓe ni ba? To ka bar ni na tafi sai ka ɗauki Ayan ɗin ka bata ta riƙe maka” tana faɗar hakan ta fita ta bar shi a tsaye yana kallon ta.
Shafa kansa yayi dan shi ya manta da wannan kalaman da yayi mata gabaɗaya, lallai dole tayi fushi sosai. Ajiyar zuciya yayi ya ƙarasa ya ɗauki Ayan suka fito falon dan so yake ayi ta ta ƙare ya gaji da zaman kaɗaici.
Ɗakin ta ya koma ya same ta tana tsaye tana saka kayan Ayan a cikin baby wardrobe ɗin sa tana kuka sosai, a hankali yake takawa ya ajjiye Ayan a kan gadon ya dawo kusa da ita ya rungume ta ta baya, ƙoƙarin ƙwace jikin ta take yi tana kuka ya matse ta sosai, tun tana son ƙwace jikin nata har ta gaji saboda yadda ya riƙe ta sosai sai jikin ta yayi sanyi tana kuka sosai. A kunnen ta yake furta, “I’m sorry! I’m sorry!.”
Kukan take yi sosai ya matse ta a jikin sa ya hanata motsi har sai da kukan nata ya ragu sannan yace, “Fatima na ki daina kuka.” Kamar bazata yi magana ba sai nasihar Mama da tazo kunnen ta lokacin da za’a kawo ta gidan sa matsayin amarya, inda take cewa, _Kar ki kasance mai taurin kai, kar ki ga mijin ki yayi miki laifi yana bin ki yana rarrashi ki dinga jan aji ki ƙi bari komai ya wuce, in kika fara aikata hakan rarrashin ki zai sire masa, saboda zai ga yana bin ki yana rarrashi amma kina botsarewa. In kin ciza ki hura, ma’ana In kika ja ajin kaɗan sai ki bar komai ya wuce, in ba haka ba nan gaba in yayi miki laifin zai daina bin ki saboda zai ce ya san ba rarrashin zaki ji ba, gwara ya bar ki duk sanda kika so zaki dawo daidai._ wannan tunanin ya saka Manal tace,
“Ka daina sona, kace saboda Ayan ka zaɓe ni ba dan kana sona ba. Meyasa ka zaɓe ni bayan ka san baka sona?” Ta faɗa murya na rawa sosai.
“Ina son ki Manal, kece rayuwata.”
“Baka damu dani ba tunda har ka iya barina na fita daga gidan bayan ka san goma na dare ta wuce, a daren ko kiran wayata baka yi balle kaji inda nake, a haka zaka ce min nice rayuwar ka?.”
Ya sasauta riƙon da yayi mata ya juyo da ita yana kallon ta yace, “na damu Partner na damu, kema kin san na damu dake kuma ina son ki. Ban san kin fita ba sai kulle gate naji, a tunani zaki je gidan Mama ne shiyasa na bari kika tafi, ina cikin ruɗani ne a wannan lokacin amma ba wai don ban damu dake ba.”
Raba jikin ta tayi da nasa ta zauna a gefen gadon ta kalle shi tace, “amma ai cewa kaka yi in na tafi kar na dawo nai ta zama har abada, sannan ka kalle ni kace darajar Ayan naci da babu abinda zaka yi dani.” Ya zauna kusa da ita yayi yace, “Raina ne a ɓace, ina cikin damuwa a gaban ki komai ya faru, Mummy ko magana bata yi min, gani take kamar komai da ya faru ni ne silar faruwar sa. Na dawo gida saboda na samu nutsuwa a wajan ki kema kika so da taki maganar. Duk abinda ya faru laifina ne da kuma naki laifin, na san kina da tambayoyin da ki ke so na amsa miki da sai ki jira sai washe gari lokacin na nutsu, ban ce kar ki dawo da wata manufa ba, bance na zaɓe ki saboda Ayan dan da gaske hakan ne a raina ba, ke kin san ina sonki ko babu Ayan.”
Ta kalle shi tace, “Meyasa tun kafin ka aure ni baka taɓa yi min maganar Rumana ba?, Meyasa baka ce min bayan aurena da kai da shekara ɗaya zaka aure ta ba?, Meyasa ka ɓoye min kayi min shiru bayan kai ne mai cewa baka so a ɓoye maka komai kuma kai ka ɓoye min?. Ka manta abinda ya faru kafin ka aure ni? Ka manta saboda kana ganin kamar na ɓoye maka wani abun kaso ka fasa aurena?. Meyasa ni ka ɓoye min? Kenan kai ne mai zuciya ni bani da ita?.” Ta kalli cikin idon sa tace, “baka taɓa faɗa min abinda ya shafe ka, ko yaushe cikin ajjiye sirrin ka kake a zuciyar ka, bani da martabar da zan san damuwar ka.”
Ya girgiza kai yace, “fargabar kar na faɗa miki ki fasa aurena shine ya saka ban faɗa miki ba, in zaki tuna kafin auren mu ranar da nace kizo mota ki same ni har nace akwai abinda zan faɗa miki a lokacin maganar zan faɗa miki Manal. Amma da kika zo zai na kasa saboda zuciyata tana faɗa min kamar in na faɗa miki zaki ce kin fasa aurena ne. Bayan na aure ki sai na fahimci gwara na faɗa miki kafin na aure ki da ace na faɗa miki bayan kin zama mallakina, hakan ya saka na dinga ɓoye miki damuwata indai akan Rumana ne, bana ɓoye miki komai a kaina in kinga kin tambaya bance miki komai ba tabbas Mummy tayi min zancen ta.”
Ta kalli idanun sa tace, “da gaske ka so Rumana a baya?.” Ya sauke idon sa ƙasa ya kalle ta ya girgiza kai yace, “na so ta, itace mace ta farko da naso a rayuwata na kuma so na aure ta Allah bai yi ba. Tun daga lokacin da tayi aure Allah ya zare min ita daga zuciyata.”
“Kenan ba ni ce first love ɗin ka ba?.” Yayi Shiru ya kalle ta yace, “kamar yadda na ce miki na so Rumana a baya.”
Hawaye ya sakko mata tace, “‘meyasa baka aure ta ba?.”
“Allah ne ya zare mun ƙaunar ta daga zuciyata, kuma Allah bai yi ni mijin ta bane.”
“Yanzu sai ka koma mata ai” ta faɗa zata tashi ya hanata yace, “wannan maganar ta riga ta wuce ya kamata ki manta da komai.”
“Meyasa ka ɓoye min? Meyasa baka sanar dani ba?. Kaine ka ke cewa baka son a ɓoye maka komai meyasa kai ka ɓoye min?.”
Ya riƙe hannun ta yace, “na faɗa miki dalilin, Nayi hakan ne saboda nayi rayuwa dake, Kuma babu ita a raina na manta da ita ke kawai nake gani.” Ta girgiza kai tace, “ban amince ba, kaima kana son ta har yanzu saboda sunan da ka ke faɗa mata ma daban da yadda kowa yake faɗa, ban amince baka son ta ba domin abinda aka fara so yana da wahalar bari zuciyar wanda yaso.”
“Manal bazan miki ƙarya dan na wanke laifina ba, da gaske na san na so ta a baya amma daga baya komai ya zama labari, in ba ganin ta nayi ba ina mantawa da nayi soyayya a wannan lokacin. Na san mun shaƙu da ita sosai kasancewar a gida ɗaya muke zaune kuma tare muka tashi shekarun da na bata basu da yawa, har yanzu akwai wannan shaƙuwar a zuciyata amma babu batun soyayyya.”
“next month zamu yi shekara da aure kenan da sai dai naga an kawo ta matsayin matar?” Ta faɗa tana wara idanun ta kafin ta girgiza kai tace, “da bazan iya rayuwa ba, mutuwa kawai zan yi” ta faɗa tana kuka ya kwantar da ita a jikin sa tana kuka ya ce, “wannan duk maganar fa ta wuce Manal, Ruman yanzu Yayar ki…” ɗago kai tayi ta kalle shi tace, “bana so na sake ji kace Ruman ɗin nan, ka faɗi sunan ta kamar yadda kowa yake faɗa.”
Yayi murmushi ya shafa bayan ta tace, “Shikenan! Rumana, in kika tuna yanzu…” ta sake dakatar dashi tace, “Meyasa yadda ka ke faɗar sunan ta bambamta da yadda mutane suke faɗa?.”
“To Manal ya zanyi?, haka maganata take zan canja ne?.” Ta kawar da kai gefe yace, “Yanzu Ruman…oh sorry Rumana ƴar uwar ki ce, tana matsayin Yayar ki a wajena kuma matsayin ƙanwata.”