Sashe 18
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama tayi murmushi tace, "Komai ya wuce mahaifin ka mahaifin ta ne, kuskurena ne ma da na ɗauko ta tun farko bai kamata nayi haka ba. Ka yi haƙuri na ɗauko maka mata har tsahon kwanaki biyar bata gidan ka ba tare da izini ba." Adnan da yake murmushi farin ciki yace, "Babu komai Mama, ni zan bada hƙri a madadin mahaifina, ya sanar damu dukkan abubuwan da suka faru, ina ne..."Mama ta dakatar dashi daga abinda zai ce tace, "Adnan kamar yadda nace maka ya wuce ka ɗauka ya wuce ɗin, dawo da maganar baya bashi da wani alfanu Adnan."
"Mun gode Mama, Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin ta kalli Manal tace, "Manali kije ki ɗauki abinda zaki ɗauka kizo ku wuce, ko da yake da me ma kika zo?." Manal na zaune ta kasa tashi saboda kunya, tana so tabi mijin ta amma sai taji nauyin Baba da Mama baza ta iya tashi ba.
Baba yace, "ki tashi mana Fatima, dare yana yi kin barshi a zaune." Manal ta tashi ta shiga ciki Baba ya kalli Adnan yace, "Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya kawar da idanun maƙiya a kan ku." Ya amsa da amin yana mai farin ciki sosai.
Mubeena tace, "Ai gwara ta tafi na huta da takurar bala'i ga tsirfa kala kala, haka kawai ta tayarwa da mutane hankali wai dambu zata ci, ba dan Allah yasa Maman Surayya tayi dambu a ina zan samo mata?.
sai kace in an kawo mata ci take" ta fɗa tana hararar Manal da lokacin da ta fito.
Manal ma ta harare ta Mubrena tace, "kika sake hararar ta wallah sai na taso na daki idon na ki." Manal ƙasa-ƙasa tace, "in kin fasa." Sai kuwa Mubeena ta zabura zata tashi Manal ta gudu daga inda take, Mama ta riƙe Mubeena tace, "ke meye haka wai? Sai kin saka ta faɗi?."
"Mama hararata take fa." Mama tayi tsaki tana nuna mata Adnan da ido Mubeena ta kalle shi tace, "oh, ni na manta yana nan ai. Ai gwara ya shaida wata rana zai ga idanun matar sa a kumbure wallahi. Mai ruwan zabiya kawai."
Baba yana dariya yace, "yau naga aminta ku ke ji da ita, ya akayi ta ƙare da faɗa?." Mubeena tayi dariya bata ce komai ba Manal kuwa tana daga gefe a zaune akan kujera.
Baba yayi dariya yace, "yi haƙuri Adnan yaran ne kamar abokan gaba wani lokacin. Tashi kaje Allah ya tashe mu lafiya ya tsayar da komai iya haka." Adnan yayi godiya sosai ya ajjiye ledar da yazo da ita ya tashi ya saka takalmin sa ya wuce Manal da take zaune ya fita.
Baba tace, "Mubeena raka ta su tafi." Mubeena ta tashi ta ƙarasa wajan Manal ɗin take zaune sai ta taso ta dawo kusa da Mama ta rungume Mama kawai ta fara kuka.
Mama tayi tsaki tace, "ke kinga matsalar ki wallahi, yanzu meye abin kuka kuma?."
"Munafurcin fa?" Mubeena ta faɗa daga gefe. Baba yace, "Manal ta shi ku je kar ki barshi yana jira."
Tashi tayi suka fita suka same shi a zaune a mota yana hango fitowar su ya zubs mata ido har suka ƙaraso yaga alamun kuka ma take. Mubeena tace, "Shikenan ki gaida gida." Manal ta kalli Mubeena cikin sanyi tace, "Yaya sai da safe." Yadda tayi maganar ssi Mubeena ta kalle ta taga hawaye take yi sai ta tausasa murya tace, "Allah ya tashe mu lafiya, ki dinga cin abinci in akwai abinda kike so ki faɗa min."
Manal ta ɗaga kai tace, "to Yaya, ni dama zaki zo mu tafi can dake." Mubeena ta harare ta tace, "Baki da hankali ai." Manal tayi dariya ta rungume Yayar ta ta tace, "zan yi kewar wannan masifar taki." Mubeena tayi dariya tace, "ke a kan hanya muke, na wuce gida, a kular mana da unborn" ta faɗa tana janye jikin ta ta kalli Adnan da yake kallon su tace, "Sai da safe" ta faɗa tana wucewa Manal ta shiga motar suka tafi.
Kukan da take yi ya saka shi bai yi mata magana ba har suka je gidan su, ya paka motar ya kalle ta yaga har lokacin hawaye take yi yace, "partner baki son dawowa ne?." Ta kalle shi da jajayen idon ta yace, "tunda muka taho kike kuka, nayi shiru na ƙyale ki saboda nasan kukan na Mama ne amma naga kamar dawowar ce bakya so."
Idanun ta goge ta kawar da kai gefe ya buɗe motar ya fita ya zaga ya buɗe mata yace, "fito." Fitowa tayi ya kulle motar ya riƙe hannun ta zuwa ciki. Falon babu dauɗa sosai sai kayan da aka yi amfani dasu aka bar su a wajan. cup ɗin tea da aka sha aka bar shi a wajan, ga bowl da spoon har da glass cup da ragowar ruwa a jarka, ga lemo, ɓawon apple da na lemon zaƙi kana gani kasan namiji ne yake zama a falon.
Wuce falon suka yi har zuwa ɗaki sa ya zauna da ita a kan gado ya zare mata hijjabin jikin ta yace, "Nasan yunwa kike ji, me zaki ci?." Manal tace, "Naci abinci a gida yanzu."
"Kin tabbatar bakya jin yunwa?" Ta ɗaga kai alamun eh yace, "okay, bara mu yi rbs kwana biyu na san ba a gwada sugar ki ba" ya faɗa yana ɗauko abin gwajin ya dawo ya zauna kusa da ita, ya riƙo hannun ta ya fasa hannun ya saka jinin a abin gwajin ya kalle ta yace, "12.1 Manal, meyasa baya ƙasa ne? Kin ci abu mai zaƙi ko?."
Girgiza kai tayi alamun a'a ya ajjiye abin gwajin a kan table yace, "in baki ci ba meyasa baya sauka?."
"Ya sauka, wancan 13 kace fa."
"Amma kwana nawa?." Tayi shiru bata ce komai ba yace, "ki dinga yi a hankali, kin san ciwo a wajan mai ciki illa ne dashi musamman wannan ciwon na diabetes, ki dinga daurewa kina kawar da kai kin ji my love?."
Ta ɗaga kai alamun to yace, "yanzu sai muje ki yi wanka ko?."
"Nayi a gida kafin kazo" ta faɗa tana kwantar da kanta a kafaɗar sa. Yace, "kaya zan ɗauko miki ki canja kenan?." Ta ɗaga kai alamun eh. ta tashi daga kafaɗar sa ya tashi ya fita bai dawo ba sai da ya kulle gidan gabaɗaya, ya kawo mata rigar bacci mara nauyi irin wacce ta saba sakawa ya zauna kusa da ita ya cire mata rigar jikin ta ya saka mata ta baccin.
Kwanciya tayi ta kulle ido kamar mai jin bacci sai ya taji yace, "kar ki yi bacci baki yi alwala ba." Tashi tayi ta shiga banɗakin ta ɗauro alwala ta fito ta same shi yana cire kaya ta wuce shi ta kwanta a gefe tayi shiru labarin da Mama ta basu duk ya cika mata zuciya.
A bayan ta taji ya kwanta yace, "tunanin me kike yi?." Manal tace, "labarin da Mama ta bamu akan wahalar da ta sha damu, in na tuna bana sanin ina kuka" ta faɗa tana murya na fara yin rawa. Adnan ya sauke numfashi yace, "ai ba abin kuka bane Manal, abinda ya faru ya wuce yanzu gashi ya zama labari."
Tayi shiru bata ce komai ba shima bai ce ba dan bashi da abin faɗa tunda laifi har da mahaifin sa. Katse shiru yayi yace, "Da Mama ta kira ni ɗazu rasa nutsuwa ta nayi, so nake kawai dare yayi yazo saboda zuciyata ta kasa nutsuwa da kiran, wani ɓangaren yana faɗa min alkhairi wani ɓangaren na faɗa min akasin haka. Har Mummy na faɗawa ta yi min addu'a Allah yasa kiran alkhairi ne."
Manal tayi murmushi ta juyo ta kwanta a jikin sa, daman abinda yake so kenan ya zagaya da hannun sa ya riƙe ƙugun ta tace, "komai ya wuce a wajan Mamana."
"Na ga zahiri tunda gashi ta dawo min da farin cikina." Kallon idanun sa take yi cikin ƙarancin hasken ɗakin tace, "da gaske ni ce farin ciki ka?."
"Ke cikin rayuwata ce Manal ba iya farin ciki ba, kwanakin da nayi a gidan nan babu ke Allah kaɗai yasam adadin azabar da nasha, tunanin ki kawai nake yi a ko yaushe. Rabon da naci abinci mai yawa wallahi Manal har na manta, tashin hankalina na farko kar ace nida ke yaya da ƙanwa ne, tashin hankalina na biyu kar Mama tace baza ta bani ke ba, ban san ya rayuwata zata kasance in babu ke ba."
Manal tayi murmushi jin daɗi ta sake gyara kwanciya a jikin sa tace, "taɓ, nima da nace nida kai Yaya da ƙanwa ne ai da na daina fitowar ko ina" ta faɗa tana dariya shima yayi dariya yace, "hmm aikin gama dai ya gama, gaki da cikin mijin ki kuma yayan ki."
"Innalillahi! Allah mun gode maka."
Yayi dariya yana kallon idon ta ya ɗaga mata gira yace, "to ya dai? Na baki abinda kike so ko baki da lafiya?." Manal ta kulle ido tana sake saka kanta cikin rigar baccin sa yana dariya yace, "uhum faɗa min, ya za'a yi yanzu?."
"Ni bana so" ta faɗa tana daga jikin sa bata ɗago ba.
Yayi murmushi mai sauti yana shafa bayan ta yace, "to yanzu dai ki yi bacci tunda ba lafiya ce dake ba." Manal tace, "ni na warke."
"Duk da haka ki huta." Manal kamar zata yi kuka tace, "A'a ni dai."
"A'a ke dai me?. To nace ki faɗi abinda kike so kin ƙi, nace na baki abinda kike so kin ce bakya so, to ya zan miki?." Manal ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido taga kallon idon ta yake yi sosai yana murmushi kafin taga ya kashe mata ido ɗaya sai ta sake mayar da kan ta jikin sa. Hular kanta ya zame yana tura yatsun sa cikin gashin ta yace, "kedai kin cika gulma, ni kuma indai baki faɗi abinda kike so ba bazan gane ba."