Sashe 3
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya kalle ta cikin fusata yace, “tashi ki bane waje, shashasha mahaukaciya wacce bata sana binda take yi ba, in ina kallon ki a nan babu abinda zai hana ban yi miki baki ba. Ki kuma tattara kayan ki ki bar min gidana, don wallahi Allah baza’a haifi shege a gidana ba.” Maryam jiki a sanyaye ta tashi ta fito daga falon Abba ta rasa abinda yake mata daɗi a wannan lokacin.
Haƙuri suka dinga bawa Abba kafin su Yays isma’il su tashi su fito daga falon, su Daddy ma fitowa suka yi bayan sun gama bawa Abba shawara akan karɓar ƙaddara. Falon ya rage daga Mama sai Abba wanda yayi shiru bai ce komai ba haka ma Maman. Ɗago kai tayi ta sauke numfashi tace, “kaji zafin abinda ya faru a kan Maryam ko?.” Da mamaki ya kalle ta yace, “wannan wacce irin tambaya ce?.” Mama tace, “kaji zafi a lokacin Lubna ma ko?.”
Bai bata amsa ba tayi murmushi tace, “me ka fahimta akan abinda ya faru akan yaran ka mata guda biyu? Baka gane komai ba har yanzu?.” Kallon ta yake cikin rashin fahimta tayi dariya kaɗan tace, “Annabi Muhammad S.A.W yace duk wanda yayi zina da ƴar wani sai anyi da tasa ƴar, in kayi zina da matar wani sai an yi da taka matar, kai baka yi tunanin wannan ranar zata zo ba ko?.”
Nan take gaban Abba ya faɗi matuƙa amma bai nuna ba yace, “Hauwa me kike nufi da abinda kike faɗa?.” Mama tayi dariya ta tashi tsaye cikin takaici da baƙin ciki tace, “abinda ka fahimta shi nake nufi. Matan banza da ka ke lalatawa a waje shine ya fara dawowa kan yaran ka, kayi da ƴaƴan wasu ne shiyasa kaima aka yi da yaran ka guda biyu, sai ka jira matar ka dan nasa kayi da matan wa…..” Mari ya ɗauke ta dashi a fuskar ta cikin zafin nama da ɓacin rai yana kallon ta a fusace yace, “ni kike faɗawa haka Hauwa?.”
Mama bata bi ta kan marin da ya yi mata ba tace, “eh na faɗa maka, na fɗa in karya nake sai ka musa. An faɗa maka bamu san kana neman mata bane?, An faɗa maka bamu san kana ajjiye mata a gidan ka na nan Kano bane?, Ka ɗauka zaman da nayi da kai na shekaru sama da talatin a banza na yi su?. Wallahi duk wani motsin ka na sani, na san da kana neman mata shiyasa baka damu da mu matan da muke cikin gida ba, shiyasa ake neman naka saboda baka isa kayi lalata ƴaƴan su naka kuma kace ka killace su ba. Duk wayon ka, duk dabarar ka, duk iya tsarin ka wallahi baka isa ka yiwa Allah wayo ba.”
Abba kallon ta yake yi zuciyar sa na bugawa sosai yace, “Hauwa fita ki bani waje.” Mama tace, “bazan fita ba, ina so na tuna maka ka san abinda ka yiwa ƴaƴan wasu suka ji irin raɗaɗin da kake ji yanzu shi ake yiwa yaran ka. Na gidan aure ma basu tsira ba, har gida za a iya zuwa ayi zina da Farida balle su Kausar da suke gida har yanzu. Dole hadisi yayi aiki a kan ka, koda Kamal bai yiwa Maryam ciki, koda Mujahid bai yiwa Lubna Fyaɗe sai hakan ta kasance ko da mai gadin gidan nan sai hakan ta faru, saboda baka isa ka yiwa na waje ba kai kuma kace zaka ajjiye naka a gida ba.”
Abba ya kasa magana sai kallon Mama da yake yi tace, “ka cuci Maryam, ka cuci Lubna, abinda ka aikata ne yake bibiyar ka kuma yanzu ka fara gani wallahi, sai kayi dana sanin da baka taɓa yi ba a lokacin da abin ya tsallako kan matan ka da jikokin ka. Zina ai ba wasa bace, zina ai ba ƙaramin abu bace, zina ba ƙaramin laifi bace, zina ba ƙaramar illa bace ba. Allah da kan sa yace kar mu kusance ta, ta ya ya ka ke tunanin zaka aikata ta ka zauna lafiya?. Yaran ka suna zaman lafiya ka jawo abinda ka aikata ya shafe su.”
“Kar ki sake ce min mazinaci!.”
“Na faɗa mazinaci! Shi ɗin ne ai ko nayi ƙarya? Mata nawa ka yi zina dasu? Kai kan ka baka san adadin su ba sannan kace sunan bai kamace ka ba?..” juya yayi ya dafe kai yadda yake ji a zuciyar sa zai iya fasawa Mama baki a wannan lokacin.
Mama tace, “ita sirikar taka babar Manal matar Adnan a harkar ta sanka ko? Yanayin kallon da take maka ba a mutum kirki ta sanka, Anya Manal ɗin ma ba taka ƴar bace….” Maganar Mama ta maƙale saboda Marin da Abba ya sake kaiwa fuskar ta cikin fushi da tsantsar ɓacin rai.
BDƘB3P03
Mama kallon sa take shima ita yake kallo cikin tsantsar takaici da ɓacin ran da dukkan su suke ciki, hannun ta yana kan fuskar ta cikin mamakin sa, dan zata iya cewa tunda suka yi aure bai taɓa ɗaga hannu ya dake ta ba sai yau, bata ji zafin marin ba so take kawai ta isar da abinda yake bakin ta domin ya san sun san komai shiru kawai suke masa ba don suna tsoron sa ba.
"Ni kike faɗawa wannan maganar Hauwa? Anya kina cikin hankalin ki?" Ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallon ta. Mama tace, "A hankalina nake, gaskiya nake faɗa maka kai kuma itace baka so. Tsakanin ka da sirikar Adnan wallahi akwai wani abun a ɓoye, tunda ta ganka ta canja ƙarshe tace ƴarta ta biyo ta su tafi saboda kaii. Bana raba ɗayan biyu, in ma itama tana cikin ƴan matan ka na baya, ko kuma...." Sai Maman tayi shiru tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta cikin tsantsar tashin hankali.
Sai tayi murmushi ta kalle shi tace, "ka cuci yaran ka, ka lalata musu rayuwa da kan ka da kuma hannun ka. Bebi da ya kasance mai maka biyayya ko yaushe shima kana neman rusa masa tashi rayuwar, a yanzu zuciyar sa a karye take yana tunanin meye ya haɗa mahaifiyar ta da kai. Komai ya faru kai ne ka jawo, kana ganin kai yaran ka sun tsira saboda suna gida ko yaushe, kana ganin basa zuwa ko ina shiyasa hankalin ka a kwance ka ke lalata ƴaƴan wasu a waje kai kuma naka ka killace su. A gain ka zaka yiwa Allah wayo da dabara, ka manta da zina tabon ta baya taɓa gogewa."
Abba yayi shiru yana kallon ta zuciyar sa bugawa take yi sosai, a take a lokacin abinda take faɗa wanda ya manta da tunanin zai faru yake masa yawo a kansa.
Ganin ya kasa motsi tace, "Ba a tsaya a na ba wallahi, zafin da kaji ba komai bane domin wannan somin taɓi ne. Za a cigaba da yiwa naka yaran ana saka maka ɗaci a zuciya ka kamar yadda ka saka ɗaci a zuciyar iyaye su. Ahh ai ka naka karuwai ne su suke kawo kan su ta ina iyayen su zasu ji ɗaci, wannan shine tunanin masu hali irin naka a ko yaushe, a ganin ka ai ba ta ƙarfi ka ke musu ba dan haka babu abinda zai samu ƴaƴan ka saboda biyan su ka ke. To ka sani ko kai ka ke sakawa a kawo maka su, ko su suke kawo kansu, ko biyan su ka ke, ko kyauta suke baka kan su zina dai sunan ta zina. Allah da kansa yace kar mu kusance ta balle mu aikata, amma yanzu kun mayar da abin ado in baka zina ma kamar baka waye ba. To ga naka sakamakon nan ka fara gani tun a duniya, kuma ina so ka sani yanzu aka fara wallahi, a hankali abun zai dawo kan matan ka in dai ka nemi matar wani!."
Abba ya kasa magana a wannan lokacin yayi shiru kawai yana jin abinda mama take cewa wanda ya ɗaure shi da jijiyoyin jikin sa, ruwan kansa ya ɗauke ƙwaƙwalwar sa taje hutun rabin lokaci saboda baya gane abinda take faɗa ma gabaɗaya.
Bebi yana tsaye ya dawo ɗaukar wayar sa da ya manta a falon, duk abinda Mama take faɗa yana ji idanun sa suka ciko da hawayen takaici da baƙin cikin abinda kunnen sa suka ji, hankalin sa ya tashi zuciyar sa sai bugawa take yi saboda duk abinda Mama tace yaji. Da zafin nama ya juya ya bar wajan yana dana sanin abinda ya dawo da shi ya shiga ɓangaren Mama. Har cikin ɗakin ta ya wuce ya zauna a kan ƙaramar kujerar da take ɗakin ya dafe kai yana hawayen da bai san dalilin zuwan su ba.
Motsin Mama da yaji ne ya saka shi saurin goge idanun sa ya tashi tsaye yana kallon ƙofar, a lokacin ta shigo ɗakin ta kalle shi ta ɗauke kai ta zauna a inda ya tashi babu walwala a tare da itatace, "me yake damun ka?." Bebi ya gyara nutsuwar sa yace, "Komai ma Mama, na manta wayata a falon abba."
Mama tayi ƙaramin tsaki tace, "ya maganar Manal din? Kabi bayan ta amma dai ko?." Ya sauke numfashi yace, "daga gidan nasu nake na dawo nan."
"To ya akayi a can ɗin?." Bebi ya ɗan kulle ido ya buɗe yace, "maganar ɗaya ce Mummy, tace babu aure tsakanina da Manal."
Da mamaki Mama tace, "akan wanne dalili?."
"Wallahi ban sani ba, babu wanda ya san dalilin. Abinda na lura dashi ba ni ne matsalar ta ba Abba ne." Mama tayi dariya kaɗan cikin takaici tace, "daman ai ba kai bane, kai fa tasan kaine ka ke auren ƴar ta, in da kai ne damuwar ta da yanzu ba wannan maganar ake ba. Shi mahaifin ku shine matsalar, yanayin kallon da take yi masa zaka tabbatar ba da arzuƙi ta sanshi ba." Bebi yace, "Allah ne ya sani" ya faɗa dan ya kawar da wancan maganar ta Abba.
Mama tace, "Allah yasa ba ƙanwar ka ka ke aure ba." Mama ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani ba, ya kalle ta sai yaga bata san ta faɗa ba alamun zancen zuci ne ya fito fili.