Sashe 60
Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar zatayi kuka ta girgiza kai tana kallon Huzaifa tace, “Ni ba zan koma yanzu ba.” Huzaifa yace, “A’a Manal, abin yayi yawa. Tun jiya naso na mayar dake Allah bai yi ba sai yau.” Manal tace, “Bazan koma ba, ba shi yace in tafi kar na dawo ba? To bazan koma ba” ta faɗa tana juyawa ta koma ɗaki.
Huzaifa ya kalle shi yace, “kaga abinda ka jawo mana saboda banzan ɓacin ran ka da baya iya sarrafa magana. bara na bita Allah ya taimake ka na iya lallaɓa ta” ya faɗa yana nufar ɗakin da ta shiga sai ya kalle shi yace, “zan je mu tattauna matsayin Yaya da ƙanwa” ya faɗa yana dariya.
Huzaifa ya same ta a zaune tana kuka ya ce, “Manal haƙuri zaki yi ki zo ki koma.” Ta share hawayen ta tace, “Yaya bazan iya komawa.”
Huzaifa yace, “meyasa?.”
“Tunda na fita bai neme ni ba sai yanzu? Ni bazan koma ba.”
“Wallahi tallahi ya neme ki ni shaida ne, ya rasa inda kike gabaɗaya a cikin damuwa ki yake.” Manal ta goge ido tace, “bazan koma yau ba Yaya, don Allah ka ƙyale ni.”
“Manal kwanakin sun yi yawa, ki daure ki tashi ki bi mijin ki fushi ya isa haka. Koma meye in kin je gidan sai ku ƙarƙare shi. ki fito muna jiran ki” ya faɗa yana fita ya ƙyale ta. Ya kalli Bebi bayan ya fito ya ce, “muje kafin ta fito.” Bebi yabi bayan sa a sanyaye.
A harabar gidan Bebi ya kalli Huzaifa ya ce, “Daman tana nan baka faɗa min ba? Kasan irin wahalar da na sha akan neman ta kuwa?.”
“Tun daren nan tayo kai tsaye, da safe take sanar dani ita bazata koma ba kuma don Allah kar na faɗa maka. Da naga tana cikin damuwa sosai sai nayi shiru ban sanar da kai ba amma a jiya nayi niyar dawo maka da ita hutun ya isa. Da naga yadda ka tayar da hankalin ka sai nace bara na ƙyale ka naga zaka nemo ta. Kuma abinda ma ya bani mamaki ban ji kayi zancen bata nan ba, sai nayi tunanin kenan ba neman ta ka ke yi ba, baka so ka san inda take shiyasa kawai na ƙyale ta ta zauna.”
Bebi ya sauke numfashi yace, “ka ɗauki haƙƙina wallahi. Ta ya zaka je bana neman inda take? Matata ce fa.” Huzaifa yayi dariya ya ce, “ka san meye problem ɗin ka? Kai baka so a ɓoye maka wani abu amma kai kana iya ɓoyewa wani. Tun farko mun faɗa maka sanar da ita lamarin Rumana shine mafita amma sai ka ƙi, sai ka ke ganin in ka aure ta faɗa mata zai fi zuwar maka da sauƙi, kaga a yanzu babu aure tsakanin ka da Rumana amma kishi ya hanata fahimta hakan. Yanzu ma taƙi fitowa tace baza ta koma ba, kawai na bata umarnin fitowa ne ba don son ranta ba dan in na biye mata nan da sati ma baza ta koma maka ba, tace ai kace in ta tafi kar ta dawo.”
Bebi ya sauke numfashi ya ce, “na fahimci kuskure na, kuma ni ba wai naƙi faɗa mata bane tashin hankali ne bana so.”
“Yanzu gashi ai ta saka ka a damuwa na kwana biyar, itama ta jefa zuciyar ta a damuwa da kishi. Sannan kuma Bebi ɗaukar hannu ka mari mace ba halin miji na gari bane ba.”
Bebi ya kalle shi Huzaifa ya ce, “bata ce min ka mare ta ba, ni naga shaidar hannun ka a fuskar ta, fuskar ta kumbura har kunnen ta sai da ya yi ciwo saboda marin. Don Allah ka dinga sarrafa ɓacin ranka ka in ba haka wallahi za’a samu matsala nan gaba, baka san lokacin da zaka furta kalmar saki ba.”
Bai ce masa komai kallon hanya kawai yake ganin Manal ta fito ita da matar Huzaifa fuskar ta babu walwala ko kaɗan, tana ƙarasowa Huzaifa ya riƙo hannun ta Bebi ya kalli hannun nasa yana jin wani iri zuciyar sa da gangar jikin sa. Jikin sa yayi sanyi sosai gabaɗaya baya bai ji daɗin wannan riƙe ta ɗin da Hamza yayi ba. Huzaifa yace, “Manal mu je na kai ki mota da kai na.”
Da matar Huzaifa suka gaisa tana tsokanar Manal Huzaifa yana riƙe da hannun ta har bakin motar, Bebi ya fito da Ayan a hannun sa da kuma kaya a leda ya saka kayan a bayan motar ya ƙaraso inda suke Manal da Huzaifa suke tsaye. Hannun sa ya saka ya riƙe hannun Huzaifa ya raba hannun sa da yake cikin na Manal yace, “hakan bai kwantan min ba wallahi, zuciyata ciwo take min.”
Huzaifa yayi dariya yana girgiza kai tace, “Au Allah? Dan na lallaɓata ta fito ko?. Na rantse da Allah sai nace ta koma sai ka bani haƙuri, Sai ka tunzura ni na nuna maka ni babban Yayan ta ne dole ayi min biyayya.” Huzaifa ya faɗa yana buɗe mata gaban mota ta shiga tana jin su bata ce komai ba.
Bebi ya bata Ayan a cinyar ta ya kulle gaban motar ya kalli Huzaifa yace, “in ka fasa.” Huzaifa ya girgiza kai yace, “Wallahi naso kafin ka aure ta aka tabbatar da ni jinin Manal ne, Wallahi da sai na baka wahala fiye da tunanin ka, sai nayi maka test da exmas ɗin da ka ke yiwa samarin ƙanen ka.” Bebi ya Harare shi bai ce komai ba ya buɗe gaban mota ya shiga ya sauke glass gefen da Huzaifa yake tsaye ya yi masa wani banzan kallo, Huzaifa yayi dariya shima dariyar yayi yaja motar suka tafi.
BDƘB3P37
Tafiya suke bata ce masa komai ba shima ya kasa magana sai kallon ta da yake yi ta gefen ido, ta haɗe fuska sosai tana yiwa Ayan wasa da yake kwance a hannun ta. Kallon sa tayi suka haɗa ido ta ɗauke kai daga kan sa ta cigaba da yi masa wasa ganin yana dariya sai tayi dariya itama tare da ɗaukar wayar ta tana yi masa hoto.
Wayar ta ce tayi ƙara taga sunan Mubeena ta ɗauka a bayyane tace, “Yaya Mubeena ina yini.” Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tace, “to sai kun dawo, ina Maman?.” Shiru ta sake yi kafin tace, “To Mama Allah ya kiyaye sai kun dawo” ta faɗa kamar zata yi kuka kafin ta girgiza kai tace, “to Mama, Allah ya kiyaye hanya.” Daga nan ta kashe wayar ta sauke numfashi.
Hannun sa taji akan nata ta kalle shi taga ba ita yake kallon ba ta kalli hannun nasa wanda yake da kyau a ko yaushe, musamman azufar hannun sa da kuma agogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannun nasa. Bata motsa ba kuma bata janye hannun ta ba ya cigaba da tafiya har suka zo ƙofar gidan, mai gadi ya buɗe masa gate ya shiga da motar ya faka motar har lokacin hannun sa yana kan nata.
Zame hannun ta tayi ta buɗe motar ta fita ta shiga cikin gidan ba tare da ta kalle shi ba. Numfashi ya sauke yayi murmushi yace, “My life partner” ya faɗa yana shafa kansa yana murmushi. Fitowa yayi daga motar ya ɗauko kayan da ya saka a motar ya shiga ciki zuwa ɗakin ta. A tsaye ya same ta tana kaɗe gadon Ayan kafin ta kwantar dashi tana kallon ɗakin.
Juyowa tayi suka haɗa ido taga yana yi mata kallon ƙasan ido kawai sai ta shiga banɗaki ta barshi a wajan. “Zan je na dawo yanzu, duk fushin da kike zan iya ɗauka sa Madam” ya faɗa yana murmushi ya fita.
Bai jima da fita ba ya dawo da white bread, da maradar da take sha da sugar da komai wanda ya san tana amfani dashi ya siyo. Yana shiga falon ya sauke ajiyar zuciya saboda ƙhamshin air freashner da ya daki hancin sa,Gashi ta kwashe komai na falon ta gyara shi yayi tas kamar ba shine wanda ya tara masa kaya ba.
Kitchen ya shiga ya tarar ta wanke komai sai ƙyalli kitchen ɗin yake yi, murmushi yayi a bayyane yace, “gida ba gida bane in babu mace, Allah ya ƙara miki lafiya Fatima na” ya faɗa yana ajjiye abinda yazo dashi ya fita zuwa ɗakin ta. Bata ciki ɗakin amma shima ta gyara shi hakan ya saka shi fitowa zuwa na sa ɗakin.
Kamar yadda yayi zato tana ciki ta yaye zanin gafon gabaɗaya ta ajjiye a ƙasa, ya kalle ta yace, “sannu da aiki Partner. Meyasa baki bari nazo na taya ki ba?” Ya faɗa yana matsowa kusa da ita. Kallon sa tayi ta taɓe baki ta wuce zata bar wajan ya riƙo hannun ta ta baya ya dawo da ita kusa da ita, ya riƙe kafaɗun ta yana kallon idon ta yace, “fushi kike ko? Na san kin cancanci ki yi fushi amma na gane kuskurena kuma bazan sake maimaitawa ba.”
Bata ce komai ba ta zame jikin ta ta fita daga ɗakin ko kallo bai ishe ta ba, bai bita ba shima ya koma wajan Ayan da yake ta wasa akan lilon sa da ta shigo dashi ɗakin yana yi masa wasa. Manal dawowa tayi da zanin gado sabo a leda ta warware ta shimfiɗa a kan gadon, ta ɗauki jakar filon ta saka ta ɗauki turaren ƙhamshi tana fesawa a jiki, ta ɗauke wanda ta cire ta saka shi cikin wardrobe ɗin ɗakin.
Tana juyowa daga taga yazo gab da ita har ƙirjin ta yana taɓa nasa gashi tana jikin wardrobe, gefe tayi zata wuce ya hana ta, ta sake komawa ɗaya ɓarin ya sake hanata, sai ta tsaya cak bata sake motsawa ba. Kallon ta yake yi ya riƙe fuskar ta da hannun sa biyu yace, “Partner ki daina fushi dani don Allah.” Kallon idon sa tayi na wani lokaci shima yana kallon ta kafin ta ɗauke idon ta daga kan sa, hannu ya saka ya riƙo ƙugun ta ya jawo ta ya haɗa ta da jikin sa sosai yace, “ki yi magana don Allah.”