← Book details Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 84

Sashe 75

Baya Da Kura Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaren Maman Manal itama rayuwa take da ƴan uwanta cikin ƙauna da zumunci. Mama sun canja gida, duk da dai a cikin unguwar ne amma sun koma babba mai kyau har matan Baba, an canja musu gida. Abban Jalingo ya siyawa  Haruna mota kamar yadda yai alƙawari. Mama ita kaɗai take rayuwa a gidan sai masu aikin ta, sai kuma Ayan ɗin Manal da tunda aka yaye shi yake zama a wajan ta, duk da indai yaga Manal sai ya bita itama Manal ɗin tana son ɗan ta ya zauna kusa da ita.

Manal da Adnan kuwa sai da suka yi shekara ɗaya basa nigeria saboda aiki ya kai shi India, duk da in wani abun ya samu a nasu asibitin yana dawowa yayi abinda zai yi ya koma amma Manal na can bata dawowa. Manal tayi kyau sosai ta sake yin fari, duk da bata yi ƙiba soaai ba amma kai da ka ganta ka san tana cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Lokacin da suka dawo nigeria ta fara karatun ta a wata private university tunda dai taga mai gidan yana so amma in a ra'ayi tane ba wani karatu da zata yi.

Burin ta ya cika, ta buɗe baban cafe da ake siyar da kayan snacks da coffee mai daɗi, ta zuba ma'aikata da kanta take zama a ciki in bata da makaranta. Goyan bayan da mijin ta yake bata shine silar ɗaukakar ta, dan a lokacin tana cikin best arewa foods bloggers. Kowa ya san ta, musaaman da bbc suka gayyace ta aka yi hira da ita a nan aka san fuskar ta.

Ranar wata juma'a ta tashi daga cafe sai ta wuce gida dan ta gaida Mama. Har cikin gidan ta shiga da motar ta ajjiye sannan ta shiga ciki. Tun daga ƙofar falon take jiyo hayaniya, tana shiga taga Adda Halima da Adda Hadiza da kuma Mubeena sai Ayan da yake kan cinyar Mama yana wasa da wayar Mubeena.

Ayan ganin Manal sai ya taso a guje yana kiran Ammi yana faɗawa jikin ta. Riƙe hannun sa tayi suka shiga cikin falon ta zauna ya hau kan cinyar ta ta kalli Adda Hadiza tace, "Mummy barka da rana" ta amsa tana cewa, "Hajiya Manal, ke dai bakya ƙiba abin ki kullum gaki nan kamar budurwa." Tayi dariya ta gaida Addna Halima ta amsa kafin ta gaishe da Mama ma ta amsa.

Kallon yaya Mubeena tayi tace, "Taɓ Yaya Mubeena Wallahi kin zama lutiya." Mubeena tayi dariya da ɗan ta a jaririn da ta haifa mai sunan Daddy suna kiran sa da Hydar, sao ai babbar ƴar ta mai sunan Maman mijin ta da suke kira da Baby a kusa da Mama a zaune.

Mubeena tace, "kema ai kin yi ƙibar ai."
"Ai in na kai ki ƙiba na daina fita" ta faɗa tana dariya sosai. Mama ta kalle ta tace, "Ke wai Manal baza ki yiwa kan ki faɗa ba?."

Gaban Manal ya faɗi ta kalli Mama tace, "Mama me nayi?."
"Baki san ne kika yi ba ko?." Manal tayi shiru bata ce komai ba Mama tace, "shekarar Ayan huɗu a duniya, kin fara karatu har kin kusa gamawa amma baki da ciki har yanzu. Kalli Yayar ki, a bayan bayan auren ki tayi aue, yanzu gashi ta haifi ɗan ta na biyu. Ke a ganin ki daidai kenan?."

Adda hadiza tace, "Wallahi abinda yake zuciyata kenan, ke waye ya faɗa miki ana yin family planning daga yin haihuwa ɗaya?. Da yarintar ki da komai har shekara huɗu baki kuma haihuwa ba me kike jira?." Manal idon ta ya ciko da hawaye zata yi magana Mama tace, "da anyi magana ido ya ciko da hawaye har yanzu kin kasa canjawa daga yadda kike a da. Haka kawai daga haihuwar farko sai ki ɗauki zugar mijin ki sha wani abun?, Ki bari ki yi guda biyu mana in yaso sai ki yi tazarar, yanzu in haihuwar ta tafi kenan fa?." Adah Hadiza tace, "aure zai yi mana, zai zauna da wacce take da da ɗaya ne."

Addah Halima tace, "Manal planing ɗin yayi yawa, ki dakatar da duk abinda kike yi yanzu ki samu ciki ki haihu, in ba haka ba a dangin mijin ki za’a fara yi dake ana cewa ai kin ƙi haihuwa dan haka ya ƙaro wata. Ba laifi bane dan kin huta bayan haihuwar ki amma hutun naki yayi yawa, shekara huɗu fa da yawa, ko yanzu kika samu ciki kafin ki haihu an tafi shekara biyar."

Manal ta fara kuka ta sunkuyar da kai ƙasa Mama tayi tsaki cikin fusata tace, "aikin kenan, da an yi mata magana sai kuka, kije ki yi Manal kar ki haihu kin ji." Adda Halima ta kwantar da murya tace, "kar ki damu Manal, faɗa min me kike sha ko me mijin naki ya saka miki?." Manal kuka take yi dan in tace musu babu abinda take yi ba yarda zasu yi ba gwara tayi shiru kawai.

Mama tace, "ƙyale ta kar ta faɗa, ita ta sani." Manal ta kalli Halima tace, "Wallahi small Mom babu abinda nake sha, tun bayan haihuwar Ayan ban taɓa shan komai wai dan kar na haihu ba, kuma bai taɓa bani magani ba, sannan bai saka min komai ba." Mama tayi tsaki tace, "kyaji da ƙaryar ki. kinga Manal rayuwar ki ce fa ba tamu ba, ni ba planing ɗin nayi ba amma Allah ku biyu kawai ya bani daga ku ban sake ba, ke da kika ga ɗayan ya ishe ki ai shikenan."

Adda Hadiza tace, “to mijin ta da wadatar sa da komai family planing ɗin me zata yi?, in ma son yin take ina laifin na shekara biyu?.” Mama bata ce komai ba. Addah Halima tace, “Ai ba laifi bane dan tayi, kawai ba a cika son masu haihuwar fari su yi bane saboda gudun matsala, amma ba wani abun bane.”
“Halima Manal fa tana sane tayi, saboda ta gama makaranta ba ciki babu jego shine ya saka tayi.” Adda Halima tace, “tace bata shan komai, mu yi mata uzuri. Kuma kun san ciwon nan nata yana ham ɗaukar ciki da wuri, wataƙila matsalar sa ce ta kawo hakan.”

Mama tace, “ke kike goya mata baya Adda, komai tayi sai kin yi ƙoƙarin kare ta. Mijin ta fa likita ne, shi yasan irin surkulan ku na likitocin da yayi mata aka kawo yanzu bata haihu ba.” Adda Halima tace, “wallahi babu lallai akwai abinda ya bata, ciwon ta kawai zai iya hanta ɗaukar ciki da wuri” ta kalli Manal tace, “amma in kina da ra’ayin samun cikin yanzu ki dinga shan folic acid kullum guda ɗaya, zai taimaka miki wajan samun cikin.”

Adda Hadiza tace, “lallai ke kike zuga ta, wato in tana da ra’ayi ko?.” Mama ta kawar da kai kawai bata ce komai ba. Hadiza tace, “Manal ai gwara ki yiwa kan ki faɗa, kinga Ayan yana wajan Maman ki kema kin samu wanda zai zauna a wajan ki.” Mama tace, “Manal ce zata bar min Ayan?.”
“Gashi kuwa yana wajan ki.”
“Jira kiga dashi zata tafi, daman hutun makarantar ya ƙare ai. Baban sa har ya fita yi min kara.” Suka yi dariya suna kallon Manal.

Manal zaman gidan gabaɗaya ya ishe ta, ta tashi ta shiga ɗakin Mama ta kwanta Ayan ya biyo ta ahima ya kwanta a kusa da ita.

Mubeena ta shiga ɗakin itama ta zauna tace, "ke wallahi kar ki wani damu ni da nayi haihuwar da wuri haushi nake ji, gwara ɗan ki da ya girma har makaranta gashi yana zuwa. Su Mama ɗauka suke haihuwar yanzu irin ta dah ce, yanzu kana hutawar ma ya ka cika balle kana haihuwa a kai a kai. Wallahi kin ganni na je na saka infant, bazan sake haihuwa ba sai nan shekara biyar in sha Allah, wannan cikin ma bisa tsautsayi aka same shi."

Manal ta kalle ta tace, "Balle ma Yaya Mubeena wallahi babu abinda nake sha, babu abinda nake yi balle nace shi ya hana ni sake yin ciki."
"Ke kar ki damu da fadan su, ki cigaba da karatun ki a nutse." Tare suka zauna a ɗakin suna hira har su small Mom suka tafi.

Itama sai gab da sallar magriba ta bar gidan dan baya so tana yin tuƙin dare da baza ta tafi ba sai dare, da wannan damuwar ta tafi gida dan tunda suka sako maganar zai ƙara aure shikenan hankalin ta ya tashi. Tare da Ayan suka koma tunda ya ganta ya maƙale mata.

Sai da tayi wanka shima tayi masa wanka sannan ta fito ta shirya shi suka fito falo ta kunna masa cartoon yana gani ita kuma ta wuce kitchen ta ɗorawa Bebi abinda zai ci. Bayan ta gama girkin tayi sallah ta fito falon ta zauna suna kallon tare aka aka kira ta a waya.

Kallon lambar tayi taga sabuwa ce bata santa ba sai ta share bata ɗauka ba aka sake kira, Ayan yace, "Ammi ana yi miki waya." Ɗaukar wayar tayi ta saka a kunnen ta daga can ɓangaren akace, "Fatima meyasa in ina miki waya bakya son ɗauka?." Gaban ta ya faɗa jin muryar wanda bata yi tunani ba tace, "Malam na faɗa maka ni matar aure ce, Meyasa ka ke takura min da waya ne?."

"Baki kama da matar aure ba Fatima, inda kina da aure zan sani ko a bakin ƙawayen ki, amma gabaɗaya baki kama da wacce take da aure ba." Manal ta dafe kai tace, "to in baka daina kirana ba zan faɗawa mijina, akan wanne dalili na faɗa maka ina da aure ka ƙi daina bibiya ta?" tana faɗa ta datse kiran tana cewa, "wannan mutumin ya takura min, haba don Allah, na faɗa masa ni matar aure ce meyasa yake takura min da waya?."

"Waye ya takura miki da waya?."
Chapter 75 · 0% Book details