← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 89

Sashe 89

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko ta kan gidan ban bi ba na faɗa tiolet na yo wanka bayan na fito ko mai ban shafa ba na zura wata doguwar riga ta atamfa ƙaramin akwatina na jawo na fara haɗa kayana. Ban san ina zan je ba amma ji na yi zuciyata na tunkaɗani da tunanin na bar ma Yallaɓai gidan shi tun da ya ce ba gidan Uba ba ne, sannan me ye amfanin zaman nawa? Tun da duk sadaukarwar da na yi ta tsawon shekaru sha takwas da aure na da shi duk ya ta shi a banza to ai ban gama amfanin zama dashi ba. Duk wani abin da zan bukata sai da na haɗa shi a cikin akwatina sannan na ɗauki jakata na saka waya ta da Atm ɗina na duba kuma akwai kuɗi a ciki ya kai 10k. Hijabina dogo na zura na ɗau key din gidan ina jin cikina na jin yunwa amma bakina ya bushe ba na jin zan iya cin wani abu.

Sai da na kulle gidan sai kuma ga ni ya bakin gidan ina tunanin to ni yanzu da na fito ina zani? Ɗorayi?. Wata zuciyar ta ce min a'a bai kamata na je gida yanzu ba. Aurena shekaru sha takwas ban taɓa zuwa da wata matsala ba bai kamata yanzu a ganni da ƙaton akwati da kaya ba. In kuma a ka tambaye ni me zan ce? Yallaɓai ya yi min wulaƙanci na dawo gida? Ya ji na yi ko mene ne?

Hawayen baƙin cika suka zubo min a saman fuskata. Ba ni da in da zan je. Dangin Mama duk suna gandun albasa kuma bai kamata suma na je musu a wannan yanayin ba, duk in da na yi tunani sai na ji bai kamata na je ba. Har Ya Aina ta kawo min arai amma sai na ji iskar garin ma gabaɗaya ba na so na cigaba da shaƙa gwara na tafi wani waje nesa da in da na baro ko zan ba ma zuciyata damar da za ta samu natsuwar da za ta yi tunanin abin da ya kama ce ta.

Sai kawai na sumgumi akwatina na fara tafiya zuwa titi na tari adaidaita na ce ya kai ni tasha. Muna zuwa tasha na ga motoci ana ta lodi na rasa in da za ni. Kawai sai ga wani É—an union ya zo gabana ya na faÉ—in.

"Kaduna. Kaduna. Kaduna za ki je Hajiya?

Sai na bishi da kallo ban san bakina ya furta kaduna zan je ba ni dai kawai na ga an saka kayana a mota nima na shiga na zauna.

Har motan ta cika muka ɗau hanya tunanin makomar sunan tafiya ta na ke yi? Ya ji na yi ko kuwa kashe aurena zan yi? Tun aurena da Yusuf yau shekara goma sha takwas. Ina da budurwa ƴa a gabana ban taɓa zuwa gida da sunan yaji ba, ban taɓa jin na gaji da auran Yallaɓai ba sai yau, ban taɓa jin in na yi yaji ban yi abu mara kyau ba, in har a shekarun da muka yi tare da Yusuf bai ji ko sau ɗaya na yi masa alfarma ba to bai kamata ni na yi masa wannan alfarman ba. Tun da muka yi aure ban taɓa kai ƙaran shi gidanmu ko gidan su ba amma yau abin da ya faru ya yi munin da ba zan yi zama a cikin gidansa ina tuna munanan kalamansa akaina ba. In na cigaba da zama baƙin ciki zai iya kashe ni.

Mun fara nisa amma tunani kawai na ke yi, gabaɗaya ji na yi zuciyata na tashi, kaina ya yi wani girma ya na sara min. Kawai sai na fiddo wayata da ke cikin jakata kai tsaye lambar Yallaɓai na laluɓo na shiga bangaren tura masa saƙo ba tare da wani tunani ba na yi masa rubutu.

"Ina so zan je Kaduna."

Wayar na hannuna sama da mintina goma sannan ya dawo min da amsa.

"A dawo lafiya."

Kenan ya amince na tafi duk in da zan je bai damu ba. saboda ya gaji da ni yanzu ba ya buƙata ta a cikin rayuwarsa. Sai kawai na kashe wayata na mai da ta cikin jaka a kusa da window na zauna sai na jinginar da kaina ina kallon giftawan motoci hawaye masu zafi suna bin kumatuna, sai na saka hijabina a cikin rabin fuskata saboda kar hankalin mutane ya dawo kaina. Amma ni dai na san mun daɗe muna tafiya sannan har muka shiga kaduna kuka na ke yi.

A tashar Kaduna na sauka ana ta kiraye kirayen sallar azahar. Ko da na sauka har jiri na ke gani, drop ɗin adaidaita na samu zuwa anguwan Rimi in da gidan Amina ya ke. Allah ya sa ban ɗauko wani kaya ba daga ƙaramin akwati sai ƙaramar jakata. Bayan na sallami mai adaidaita ina jan jikina da na ke ji kamar na faɗi jikina har ya na rawa rawa bakina ya bushe kamar yadda zuciyata ta bushe.

Get É—in na buga megadi ya buÉ—e ya na tambayana wajen wa na zo sai na ce masa matar gidan, bai sanni ba domin kamar an sauya megadin ne.
Kafin ma ya tsaya min wani magana na ce masa ni yayar matar gidan ne ina ga kammani ya gani ya buɗe min ƙofa na shiga ina jan kafa har wani duhu duhu na ke gani.
A ƙofar shiga falon na duƙe ina jin amai na taso min bayan na buga mata ƙofa. Amai na ke yi ruwa ruwa tun da bakomai a cikina. Na kasa tashi har na ji an buɗe ƙofar na ji muryan Amina ta na kiran sunana.

"Ya Sadiya?

"Ke ce?

Ɗagowa na yi ina kallonta da idanuwana da suka yi laushi. Hannuna na miƙa mata ta kamani lokaci ɗaya ta na faɗin" Innalillahi Ya Sadiya me ya same ki?
Ni dai ban bi ta kanta ba, nan na watsar da jakata da akwatin Amina ta kamani zuwa cikin falonta kan kujera na yi yarf kwance domin sai na ji kamar ruwan jikina ya ƙare da gudu ta koma ta ɗauko jakata sannan ta jawo akwatin zuwa tsakiyar falon. Ni kuma amai ya ƙara taso min sai na tashi ina tangaɗi na yi bedroom ɗin ta da gudu ina jin ta ta biyo bayana ta na faɗin.

"Subhanallah Ya Sadiya."

Sama sama na ke jin ta sai da na dangana da tiolet ɗin bedroom ɗin sai gani zaune a ƙasan tiolet domin ba zan iya tsayuwa ba, ji na ke yi kamar ba ni da ruwa ba ni da jini, ina amai amma ina ji kamar hanjin cikina za su yo waje, kakari kawai na ke yi ni dai na ji Amina ta buɗe ƙofar tiolet ta na ƙara kiran sunana amma ina kamar a wata duniyan na ke jin ta ,kaina da ya yi min nauyi na jingina da jikin garon Tiolet ɗin ina jin kamar fitsari na bin jikina.
Ya illahi fiteari na ke yi a zaune saboda jikina ya yi mugun sakin da ba zan iya motsa koda É—an yatsa na ba ne.

"Innalillahi na shiga uku Ya Sadiya."

Na ji ta kamani ta na ƙoƙarin miƙar da ni tsaye amma ina jikina gabaɗaya ya saki. Idanuwana suna lumshewa amma sai da suka gano min jan abu da na ga ya na zirarowa ta ƙasan kafafuwana. Kamar jini na gani. Ba kama ba ne jini ne ke bin ƙafafuwana ba fitsari ba ne.
Sai na yi ƙoƙarin tashi ina mai dafe bango Amina na riƙe ni har ta fara murya kamar za ta yi kuka.

"Mun shiga uku Ya Sadiya jini kike zubarwa."

Na ƙara bin ƙafafuwana da kallo jini ne da gaske har ya gangaro ya ɓata farin tayels ɗin Tiolet ɗin. Ina ƙoƙarin na tsaya da kafafuwana amma na kasa. Kamar an ɗauke ni daga wannan duniyar haka na ji kamar ɗaukewar iska shuu.! Sai na tafi yaraf na faɗa a jikin Amina. Bakina na motsi ina so in yi magana a lokacin sai komai na duniyar ya tsaya mini cak kamar an zare rai daga gangan jikina.

*Ƙarshen littafi na biyu.*

*ZA MU TAFI HUTUN KWANA BIYU KAFIN MU ÆŠORA A LITTAFI NA UKU IN SHA ALLAHU.
NA GODE DA JIMARIN BIBIYAR WANNAN LABARIN.

*16. Jan 2025.*
*Janafty*
.
.
Chapter 89 · 0% Book details