← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 89

Sashe 43

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hauwa ke faÉ—a min Anty Bahijja ta ce ta É—auka ciki ne Gimbiya ke da shi sai da a ka je asibiti sannan a ka ce ba ciki ba ne, ni dai na yi shuru ban ce komai ba ina nazari ni kaÉ—ai.
Sai da ta ce ta ga ai Jidda a can ta na tambayanta ko ta koma can ne gabaÉ—aya sai wai Anty Bahijja ta ce e ai jeka ka dawon bai da amfani gwara ta dawo wajen Gimbiyar gabaÉ—aya.

"Haka ta ce miki?

Na faÉ—a cikin mamaki ina kallon Hauwa.

"E mana. Anty Maimuna ma na wajen ta kada ba ki ta ce ai daman Jidda ai yar gidan Gimbiyar ce shi ya sa Tafida ya ba ta ita."

Kai kawai na jinjina a raina ina girmama tunanin Yallaɓai, ina ga ya manta da ni ce na haifi Jidda ba Gimbiya ba. Hauwa ta tafi ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ta dira a gidana da yamma domin ta na shigowa ana ta kiraye kirayen sallar mangariba ne.
Na karɓe ta hannu bibbiyu kamar yadda na saba kamar ma ba zama ta zo yi ba. Sai da na ce ta zauna ita da Sulaihat ne, na tashi domin na kawo musu ruwa ta ce na bar shi kawai ta zo ne domin ta na son yin magana da ni sai na dawo na zauna ita kuma sai ta ce ma Sulaihat ta je ta zauna tare da Baby.

Sai da ta fice ne sannan ta juyo ta na kallona kafin ta ce" Sadiya kin kyauta kenan?
Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Me na yi kuma?
"Laifi ki ka yi mana."
"Laifin me?
Na faɗa ina ƙara tambayanta domin ni dai ban san na aikata wani abu ba.

"Kishi ne ya hana ki zuwa ki duba Gimbiya da jiki?

Sai kawai na yi wani sansarai ina kallon Anty Bahijja.

"E kalle ni dakyau. To in ba kishi ba menene? Ai ciwo ya wuce wasa ko da ba ki taɓa zuwa gidanta ba tunda yanzu rashin lafiya ne sai ki danne komai ki je ki duba ta ko bakomai a matsayinku ɗaya da ita kamar yadda kike matar Tafida itama haka take matarsa. Da auren shekaru da wanda aka ɗaura yau ai duk sunan su aure ko?

"Haka ne."

Na bata amsa ina shanye mamakina.

"To ba ki kyauta ba. Da na ji an ce ba ki zo ba kin san halina yar gaskiya da gaskiya ce na ce sai na zo na faÉ—a miki ba ki kyauta ba, shima Tafida na kira shi a waya na yi masa faÉ—a ya ce ya sha'afa ne amma zai kawo ki domin ki duba ta."

Sai kawai na zaune ni dai ban ce komai ba ina kallon Anty Bahijja. In tsaya ma yi mata wani bayani ma ɓata lokaci ne sai kawai na ce ta yi haƙuri zan je na duba ta in sha Allahu sai ta miƙe lokaci ɗaya ta na faɗin" Yakamata. Su kansu masu taya ki kishin su Hauwa duk sun je sun duba ta."

"Zan je nima in sha Allahu."

Ta ce Allah ya sa har da na rakasu haraba ta na min shaguɓe.

"Sadiya kowa ya san mu mata muna da kishi amma ɓoyewa ake yi. Ki daina bayyanawa  gudun kar Gimbiya ta fahimta ta raina ki. Ga shi ta na son ki ta na son mijinki da ƴaƴanki ko domin haka ba za ki danne komai ki je ki gaishe ta ba?

"Gaskiya ne. A yi haƙuri na yi kuskure."

Sai ta wayance ta na min dariya wai ta na sona ina da fahimta wani lokacin in ban so rashin kunya ba. Ni Allah na tuba yaushe na taɓa mata rashin kunya! Iya biyayya fa ina yi musu da ba su girmansu su ne ba su iya kama girman na su ba haka na dawo cikin gidana ina ta juya maganganun Anty Bahijja a ƙasan raina ba kowa ya ja min wannan wulaƙancin ba sai Yallaɓai kuma wallahi ba zan ƙyale shi ba.
A ranar daman zai koma gidan Gimbiya ba nan zai sauka ba, kuma na ce ba zan kira shi a waya ba sai ya zo za mu yi ta ƙare, ya kirani a daren mun yi sallama daman haka ya ke da safen litini bayan Baby ta tafi makaranta da wuri na shirya na riga shi fita kafin shi ya baro can zuwa gidana sai dai muka haɗu a can ni da shi bai ma san na zo ba sai ita Gimbiyar ne ta je ta kira shi. Ba kuma sanin gidan na yi ba, Hauwa na kira ta yi mini kwatan cen gidan Allah ya taimake ni gidan ma ya na bakin titi ne, sai da na sauka adaidaita na yi tambaya a ka nuna min ina buga get ɗin sai ga ta ta zo ta buɗe min.

Ba ma shi ba, har ita na san ta yi mamakin ganina. Kuma ni dai yadda ake zuzuta rashin lafiyan na ta ban ga haka ba. Da bakinta ta ke faɗa min ta ji sauƙi, saboda na ganta cikin gayunta ne domin ai ba su yi tsamnanin ganina ba. Yallaɓai kuma ta ce yanzu ya dawo daga kai Jidda makaranta ina falo ta bar ni, ta je ciki ta kawo min lemu da ruwa ta ce abin karyawa na ce na karya daga gida duk da ina tunanin su kansu ba su karya ba.

Gidanta itama ya yi kyau duk da iya falo na gani. Amma falon ya yi kyau ƙwarai kayanta duka yan waje ne forum, tare suka fito da Yallaɓan ya na sanye da Jallabiya da ya ganni zaune sai da ya nuna mamakin sa.

"Shi ne kuma ba ki kirani na zo na kawo ki ba Madam?

Ya faÉ—a ya na zama a gefena.
Har ya na rumgumoni.
"Gud morning"
Ko amsa shi ban yi ba na juya ina kallon Gimbiya kafin na ce" Ki yi hakuri kar ki ga ban zo duba ki ba. Ni bai faÉ—a min ba ki da lafiya ba."

Kanta na ƙasa ta na wasa da hijabin da bayan shiganta ta sako shi ta ce" Laa bakomai wallahi."
Shi kuma ni ya ke kallo kafin ya ce" Ki ji tsoron Allah ban faÉ—a miki ba ta jin daÉ—i ba?
Kallonsa na yi tare da balla masa harara kafin na ce" Ka dai yi magana da Jidda amma ni baka kalle ni ka ce Sadiya Gimbiya ba ta da lafiya ba. Ka ja ita ta ga laifina sannan yan'uwanka ma sun ga laifina tunda an biyo ni har gida an ce saboda kishi ne ya sa ban zo na duba ta ba, shi ya sa yau bayan Baby ta tafi makaranta na taho domin na wanke laifina. Ki yi hakuri ba kishi ne ya hana ni zuwa na duba ki ba."

Daga ita har shi sun ɗan ji wanni iri, ni kuma ban damu ba sai na miƙe daman na tsaya a hanya na siya ayaba da kankana na ijiye mata saman center table ɗin dake tsakiyar falon lokaci ɗaya ina faɗin.

"Amarya Allah ya ƙara lafiya."

Ta amsa da Amin itama ta na miƙewa kafin ta ce" Ni fa ban ji wani abu ba. Ciwon ma ba sosai ba ne kawai su Anty Bahijja ne suka tambayeni kin zo na ce a'a amma ba da wata manufa na faɗa musu ba."
Sai na juyo ina kallonta kafin na ce" Kar ki damu fa. Bakomai."
Na faÉ—a ina mata murmishi shi kuma Gogan ya na zaune ya kasa mgana sai da na juya ina ce masa tafiya zan yi sannan ya ce na jira shi mana ya yi wanka sai mu fita tare.

"A'a bari kawai na tafi kar Saude ta zo ba ta same ni ba."
   
Ganin na dage ba zan tsaya ba ne dole ya sa ya ce bari ya zo ya kaini gida sai ya dawo har zan ce ya bar shi daga baya kuma sai na yi shuru saboda ina so mu ƙare ta ni da shi.
Ya É—auko ni a mota muna hanya zai kai ni gida ya ga tun da muka É—au hanya ban yi masa mgana ba sai ya kama kan shi.

"Ki yi hakuri na É—auka kin ji lokacin da na ke faÉ—a ma Jidda ne."

"Oh.."

Na faɗa ba tare da na kalle shi ba ina ma ƙoƙarin sassauta fushina ne.

"Kin ji ko?

Sai na kalle shi kafin na ce" Ni fa abu ɗaya ya ɓata min rai yadda ka ja zamin zagi wajen yan'uwanka? Ka faɗa min ne? Ko kuwa don kana magana da Jidda sai ya zama da ni ka ke? Ni ba za ka iya faɗa min baki da baki ba Yallaɓai?

Na faɗa ina mai ƙuresa da ido sai ya gano kuskuren shi nan da nan ya fara ba ni haƙuri.

"Ki yi hakuri don Allah. Na yi kuskure."

Na haɗe rai ina faɗin" Burin ka daman yan'uwanka su ga laifina. Sannan matarka ta ji haushina ban zo na gaisheta ba. Ka kyauta Yallaɓai ka kyauta kawai zan ce maka."

"Duk na ji kuma na amsa laifina. Na ce ki yi haƙuri."

"Hakuri ai zama dole. Amma dai ba ka kyauta ba. Ko maganar zuwa gidanta da ban taɓa yi ba laifinka ne itama in za ta zo gidana ai kai ka ke kawo ta ba ta taɓa zuwa ita kaɗai ba sai dai ku zo tare da ita ko ka kawo ta ka maida ta. Ni ka taɓa ce min na zo mu je? Sai na yi tunanin ba ku gayyata ta shi ya sa ban tusa kaina ba amma kuma daga baya sai ni a ga laifina! Ko saboda ni ce Sadiya uwar laifi?

Na faɗa ina kallon shi, saboda wallahi abin ya ɓata min rai matuƙa.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na amsa laifina. Ki yi hakuri haka ba zai ƙara faruwa ba."

Shuru na yi masa ban yi mgana ba sai ya riƙe min hannu da hannun shi guda ɗaya, ɗayan kuma ya na tuki dashi.

"Am Sorry kin ji"
Chapter 43 · 0% Book details