← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 89

Sashe 44

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ƙara yi masa banza sai ya matse hannuna shi ya sa na kalle shi kafin ya marairaice ya na faɗin" Na ce fa a yi haƙuri ba shikenan sai a huce haka nan ba?

"Na haƙura amma bayan wannan akwai wata mganar mu da ni kai."

"Me kuma na yi?

Ko kallon shi ban yi ba sai ma hannuna da na zare cikin na shi na yi gefe da fuskata ina kallon wucewar motoci fuskata a haÉ—e.

"Sadiya ta."

Sai na juya ina kallon shi.

"Me kuma ya sake faruwa?

Ya faÉ—a duk ya wani kama kanshi ba gaskiya. Sai ni kuma na É—auke kaina kafin na ce" In mun je ai za ka ji."
Sai ya yi shuru kamar ya na tunani kafin ya gyaɗa kai ya na mai faɗin" Shi ke nan ni sarkin laifi. Zan sake ba da haƙuri wannan karon ma."
Ko ƙala ban ƙara ce masa ba har muka isa gida, a waje ya ijiye motar na ce masa ya shigo cikin gida mu yi magana kafin ya wuce.

A falon farko muka tsaya ya na goye da hannayensa a bayan sa ya na kallona
Ni kuma sai na sauke mayafin kaina ina faÉ—in.

"Yallaɓai."

"Na'am"

"Na ce ko dai kai da Gimbiya ne kuka haifa min Jidda ne?

Sai ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce" Me ya kawo wannan mganar? Har ya na wani shan mur.

Kai tsaye na ce" Abin da ya kawota shi ne. Labari na ji a gari an ce ka ba ma Gimbiya Jidda halak malak ni kuma da na ji labari sai na ce ba ka gaya min ba, ban san da wannan mganar ba."
Na faÉ—a ina mai kallon shi sai ya wani rausayar dakai kafin ya ce" Ba har abada na ba ta ba. Daman ai yarta ce. Saboda ba ta jin daÉ—i ne kwana biyu nan ya sa na ce ta É—an zauna da ita. Ina tunanin ai ba ki da matsala da hakan ko?

"Ta ya ka san ba ni da matsalan da hakan tun da baka faÉ—a min ba?

Sai ya yi kasaƙe ya na kallona ni kuma sai na ƙare ware masa ido kafin na ce" E. Ai ba ka yi magana da ni ballatana ka fahimci ko ina da matsala ko ba ni da shi?
Sai ya yi shuru kawai ya na kallona, ni kuma na riƙe kugu ina cigaba da faɗin.

"A matsayina na mahaifiyar Jidda ban da mutumcin da za ka yi mgana da ni Yallaɓai? Sai dai na ga kana aiwatar da duk abin da ranka ya so maka kai kaɗai? Ko a farkon tarewan Gimbiya da Jidda ta ke zuwa ta kwana da ita ka nemi shawara ta.? Duk da dai ba zan hana ba amma aƙalla dai ka daraja sunana na uwa ka yi magana da ni ba wai na riƙa jin maganar abin da ya shafi ƴaƴana a gari ni ban sani ba."

"Sadiya ba ki da kara ne? Ba za ki yi ma Gimbiya kara ba?

A fusace na ce" Ita na yi mata kara shi ya sa kaga ban yi magana ba sai yanzu. Kai ne ba ka yi min kara ba Yallaɓai. Sam ba ka yi min kara ba."

"Laifi ne domin na zar tar da Umarni kan Jidda ban shawarce ki ba Sadiya?

"Ba laifi ba ne amma a kalla dai ka daraja ni. Ai ba ci baya ba ne in ka ce min Sadiya Jidda za ta koma wajen Gimbiya na wani lokaci ai kasan ba zan ce komai ba amma dai zan ji daÉ—i a raina ka martabani ko?

"To ki yi hakuri. Na ji ban kyauta ba shike nan ko?

Sai na É—an sassauta fushina ina mai juya fuska, mirmishi ya yi har ina jin sautin mirmishi kafin ya ce"Madam ki yi hakuri kin ji ko?
"Ni fa ba rai na ne ya ɓaci ba kawai na faɗa maka ne domin ka kiyaye. Ba na so kar ka sake yi min haka ina gidan nan in abu ya shafe ni ko ƴaƴana ka daina abu ba tare da ka yi magana da ni ba."

"An bari. Kuma za a yi mgana da ke in sha Allahu."

Sai na sauke numfashi na koma na zauna ba ta re da na yi magana ba sai shima ya zo ya zauna a kusa da ni ya na faɗin" Shiken ko faɗan ya ƙare ko?
Ya faÉ—a ya na rumgumoni zuwa jikinsa.

"Ni ban yi faÉ—a ba."

Na faÉ—a ina sunne kai a saman kirjinasa.

Saman kaina ya sumbata kafin ya ce" To in ba faÉ—a ba me kenan kika yi? Tun a mota sai faÉ—a kike yi min mun zo gida ma ban tsira ba. Alhalin kuma nima kin yi min wani abu da ya sosa min rai kuma kema kin sani amma ban yi miki mgana ba, ko faÉ—a ma ban yi miki ba."

Sai na yi saurin É—agowa ina kallon shi kafin na ce" Ni? Me na yi maka kuma?
"Kin sani fa Sadiya."
"Ban sani ba fa."
Na faɗa cikin shagwaɓa har ina kai masa duka a ƙirji, sai ya riƙe min hannu ya na kallona kafin ya ce.

"Kin tsara za ki fara kasuwanci amma ba ki faÉ—a min ba har aka kawo kaya na yi miki mgana sai ce min kika yi wai kin bar ni na gama cin amarcina ne? Wannan mgana ne? Tsakaninki da Allah duk wani abu da zan yi ko za ki yi mun saba zama mu tattauna a tsakanimmu, amma sai ga shi yanzu kin sauya kin fara yin abubuwa kai tsaye ba tare da kin faÉ—a min ba ko dai ba zan ba da komai a kallah dai na saka albarka na ba da shawara ko?

Ashe ya ji haushi, sai na ji daÉ—i ai ni haushin na ke son ya ji.

"Kin kuma san na ji haushi amma ki ka share ni."

Sai na yi mirmishi, kafin na ce" Afuwan Yallaɓai. Allah ya huci zuciyar Tafidan Rano."
Kawai sai ya jinjina kai kafin ya ce" Na yi haƙuri fa. Kawai dai na faɗa miki ne domin kin san na ji haushin ki."

"To a yi haƙuri Megida."

Na faÉ—a ina shafa sajen shi zuwa gefen masa.

"Laa la. Yallaɓai tafiya ta tafi. Furfura ka fara fa."

Na faÉ—a ina masa dariya, É—ankwalin kaina ya cire ya na faÉ—in"Ke ma ai kin tafi. Ina dubawa zan ga ta ki furfuran."
Ina dariya na kwaçe kaina ina faɗin" Ni yar yarinta? Yanzu na ke fa kai dai tsufa ya kama."

"To ke kika tsufar da ni. Saurayi ɗan ƙwalisa kika aura amma ji yadda yanzu na dawo."

Ya faɗa ya na wani kallon kanshi kafin ya ce" Sadiya ko yanzu na so zan auro biyu yan mata ƙwarara."
Sai na balla masa harara kafin na ce" Kai yanzu a zuciyarka akwai wajen wata mace?
"Ai ba ni na samar musu wajen ba Ubangiji ne."
Sai na kasa mgana na tsaya ina kallinsa shi kuma ya na min dariya sai kawai na miƙe tsaya na ja hannun shi ina faɗin" Sai anjuma Yallaɓai."

Ƙin tafiya ya yi sai da na riƙa tura shi sannan ya tafi ya na min dariya a raina na ce ni yanzu har wani aure za ka ƙara da zai ɗaga min hankali, ai sai dai Gimbiya itama ta ji yadda a ke ji na zafin kishi, yadda na samu na zazzage ma Yallaɓai abin da ke cikina sai na samu salama, kuma shima ai ya san bai kyauta ba shi ya sa ya ba da haƙuri.
Tuni Gimbiya ta warware. Yallaɓai ya san na yi masa tsiya tsiya sai ga shi ya zo ya na faɗa min Jidda ta na so ta dawo gida amma ya ce ta ɗan zauna ta ƙara kwana biyu na ce bakomai. Ni daman saboda tahfez ɗin ta ya yi rauni ne amma acewarsa ita Gimbiyar na yi ma Jiddan karatu a can.

Ko sati ba a yi da zuwana duba Gimbiya ba Nene ta faɗi a gida sai asibiti ana zuwa aka ba su gado. Jininta ya hau sosai ta samu jin jiri kuma ta ƙi mgana shi ne ranar kawai da safe ta faɗi Allah ne ma ya kyautata da ta samu shanyewar jiki, amma ko yanzu ɗin hannunta na dama da kafarta sun ɗan tabu bangaren hagu sun fi lafiya. Hankula sun tashi matuƙa ko ni na damu da ciwon Nene musamman saboda Yallaɓai ba ya son ganin ta cikin ciwo yanzu shina sai ya susuce. Shi ma ko in ba shi da lafiya ba ta da sukuni sai ta ji labarin ya samu lafiya shima ba ta yarda sai ta gan shi ya tako da kafafun shi ya zo duba ta.

A wani asibitin kuɗi ne na cikin gari in da Mimisco ke kaita ta na ganin likita ne aka kwantar da Nene. Gabaɗayanmu can muke yini da ni da Hauwa da har da Munnira da su Halima,Hajiya iya da Maman farko, su Anty Bahijja daman suna gaba gaba su masu uwa. Gimbiya kuma ta bar bangaren surukai ita ta koma bangaren ɗiya. Ita ta ke kwana da Nene Hajiya iya aka ce ta riƙa kwana da ita Gimbiya ta yi tsaye ta ce ita za ta riƙa kwana da ita su Anty Bahijja kuma suka amsa, da ita Mimisco ta ce gwara Hajiya Iyan ita babba ce sannan ita Gimbiya ga jikinta ba daɗi amma ta yi tsaye ta ce ta warke Yallaɓai ma ya amince ta riƙa kwana da safe sai ta je gida ta yi wanka ta huta ta kuma dawo.
Chapter 44 · 0% Book details