Sashe 71
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwaggo ta ce min bayan ta ce a bani wayar ta yi ta lallashina ta ce Alhaji zai yi adalci kuma Ma'u ba ta kyauta ba kuma za a gaya mata. A kallah dai yanzu sun yarda da cewa Ma'u munafuka ce kuma fuska biyu gare ta.
Gidan Ya Aina na kwana akan gadon ta ni da Marwa. Ita kuma a turakan megidan ta kwana tun da asuba Kawu Abba ya kira wayata lokacin ma ina zaune kan darduma ina azkar ne bayan mun gaisa ya ce min.
"Sadiya na ji duk abubuwan da suka faru. Ban ji daɗi ba. Amma ina so ki sani Tafida ba zai ƙyale wannan mganar ba. Yanzu haka ya kira su Kawu Sa'adu yau muna tafe za a yi zama a gidan Nene ki yi haƙuri duk wanda ya haɗa maganar nan domin ya tozartaki sai dai shi ya tozarta ta in sha Allahu."
"Allah ya sa."
Na faÉ—a cikin sanyin murya.
Ba mu wani daɗe muna mgana ba har ya na ce min ina gidan su Marwanatu ko? Na kuma san ita Marwan ta faɗa masa ina gidan su tun da ai na ji ta ƙasa ƙasa da daddare suna waya.
Da safiyar jumma'a na wayi gari a gidan Ya Aina duk breakfast ɗin da ta haɗa min ban iya cin komai ba sai Tea kawai da na sha. Yara duk sun tafi makaranta Marwa ce kuma aikin rana gare ta yau, Ya Aina ta saka min ruwan zafi na yi wanka ta ba ni kayanta na saka tunda yawancin jikin mu duk ɗaya ne sai dai ma ta dan fi ni kiɓa.
Munnira ta kirani a waya ta na faÉ—a min suma an kira su gidan Nene ita da Hauwa.
"Ni ba wanda ya kirani ko Yallaɓan ma tun jiya da ya sauke ni gidan Ya Aina ban ƙara jin sa ba."
Munnira ta ce" Hmm jiya bayan tafiyarki an yi abubuwa Sadiya. Daman ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Sadiya Allah ya wanke ki. Tafida ya tsaya miki jiya har ita Gimbiya sai da ta raina kanta."
"Me ya faru?
Na faÉ—a cikin sanyin murya.
"Bayan fitan ki Mimisco ta zo itama ta yi ta faɗa da Anty Bahijja. Da ita kanta Gimbiya Nene kuma ta ce tunda Anty Bahijja ba ta jin maganarta ta je tun da ta isar da abin da ta so. Da ko Tafida ya dira a gidan sai da ya haukace musu. Shi da Anty Bahijja suka yi kaca kaca Mimisco kuma ta da su Maman farko suka goya masa baya. Har da Nene da ya ce ba zai ƙyale maganar ba ta ce itama ba ta ce ya ƙyale ba. Ita kuma Gimbiya a gaban mu ya kalleta ya ce" Ke kuma kin ban mamaki Saudatu! Sadiyar ce za ki bari masu zuga ki zuga ki ki yi mata ƙazafi? Shin kin ji lokacin da likita ya ce wani mganin zubar da ciki ki ka sha? Da har za a zo a yi mgana ki amince har kina maida zencen! Kin ban kumya. Ta yi miki alheri kin saka mata da sharri. Ina so ki sani ba zan ƙyale ki ba ke ma sai kin maimaita abin da kika faɗa a gaban hukuma."
Nan fa hankalinta ya tashi ta fara kuka ta na ba da haƙuri da cewa Anty Bahijja ce ta ce yar uwan Sadiya ta ce ta na shiga malamai ƙilama ta so zubar mata da ciki shi ne ta ce ai ta taɓa ganin ƙanwar mamaki ta kawo miki mgani ta na rantsuwan ita abin da ta faɗa kenan kawai."
"Munafuka."
Na faɗa ina jin zafin daga ƙasan zuciyata.
"Wallahi ai duk kukanta Tafida bai saurareta ba. Kowa fa ya ba su rashin gaskiya shi ne a ka ce yau za a yi zamacda gabaÉ—aya waÉ—anda abin ya faru suna nan."
"Allah ya kyauta."
Na faÉ—a ina cije baki, na ce mata ina gidan Ya Aina anan na kwana.
"Su Jidda fa?
"Muna gidan har dare amma ba su zo ba."
"Ina ga suna gida tare da Baban su."
Da haka muka yi sallama. Ya Balki ta zo gidan itama da safe ashe Ya Aina ce ta kira ta ta faÉ—a mata, itama ta yi ta gunduma ma Ma'u ashar ta na faÉ—in" Yar asara kawai. sai ta je ga ta ga mutanen duniyan nan."
Tana ma gidan Yallaɓai ya kirani ya ce ya na kofar gida na fito. Ina fita fuskarsa ba fara'a ina gaishe shi ya amsa ya na kallona kafin ya ce.
"Kin tashi lafiya.?
Bai jira amsawata ba ya ce" Shigo mota mu je."
"Ina?
"Gwammaja."
Sai na ce bari na koma na É—auko jakata da wayata.
Ina komawa cikin gida na faÉ—a ma su Ya Aina ya ce mu je can gidansu yanzu.
"Gwara ku je kan a yi ma lamarin tufkar hanci."
Na tafi da cewa duk yadda ake ciki zan kira Ya Aina a waya. Ya Balki ta rakani da cewa" Shi ya gama na shi mu ma za mu yi namu Allah sai mun taru mun ci uban Ma'u ƙila za ta shiga taitayinta daga yanzu."
Ni dai na fice na bar su, tunda na shiga motar nan Yallaɓai bai ce min ba nima ban ce masa ba sai da na ji ya na waya ya na faɗin ga shi nan ya ɗauko ni.
Sai da na bari ya gama wayar sannan na kalle shi ina faÉ—in.
"Ina so na fara zuwa gida."
"Me za ki É—auka?
"Wani abu ne."
Sai ya kalleni amma bai yi magana ba.
Gida ya maida ni, na shiga ciki shi kuma yana cikin mota.
Kaya na sauya da hijabi sannan na sauya takalmi, na shiga kitchen na ɗibo magungunar da Inna Mariya ta kawo min na tusa a jaka ta, a yanayin kitchen ɗin na gane a gida yara suka kwana Yallaɓai ya yi musu girki shi ya sa na ga kitchen ɗin a hautsine.
Ko kafin na fito sai da ya kira waya na lokacin ma ina bakin get, sai na fito na rufe get É—in da makulli, ina komawa motar ya juya muka nufi Gwammaja. Tare da shi muka jera har falon Nene sai na ga ashe ma kowa ya hallara mu kaÉ—ai ake jira.
Ga Kawu Sa'adu da Kawu Abba sai Hajiyar Tafida da Nene a saman kujera sauran duk suna ƙasa hatta ko da Mimisco har da su Hauwa duk suna falon. Duk da zarafina da a ka ci jiya a gidan bai sa na fasa zuwa gaban Nene da Hajiya na gaishe su ba suka amsa min kamar ba abin da ya faru.
Sai na koma can kusa da su Hauwa na zauna sannan na gaida su Kawu Sa'adu da Mimisco. Anty Bahijja da Anty Maimuna kallo ba su isheni ba, ballatana wata Gimbiya can.
"Ma sha Allah. Tun da su sun iso. Ku yi ma su Maman Farko mgana su shigo."
In ji Kawu Abba.
Halima ce ta tashi ta je ta kira su sai ga shi sun shigo tare. Su kan na gaishe su tun da su kam ba su yi min komai ba, suka amsa min suma kamar ba abin da ya faru. Yallaɓai dai kusa da Kawu Abba ya zauna a saman kujera.
Mimisco ta buÉ—e taron da addu'a sannan Kawu Sa'adu ya fara jawabi.
"Kowa anan wajen ya san dalilin taruwar mu a wannan falon jiya da yamma Tafida ya kira ni cikin damuwa ya na ba ni wani labari da ya ɗaga min hankali. Da cewa ke Bahijja kin ci zarafin mai ɗakin sa da yi mata kazafin ta na son zubar ma da ita amaryansa Saudatu juna biyu! Sannan har kina ikararin ita yar asiri ce kina ba da wani labarin da ba wanda ya san da ingancinsa. Abin na ki bai tsaya nan ba sai da kika bita da baƙaken maganganu mara sa daɗi waɗanda suka yi dai-dai da kin ci mata mutumci. Ta ce za ta kai hukuma shi ya hana ta da cewa shi ya kamata ya ɗau mataki shi kuma ya ga ya na da manya shi ya sa ya kira ni ya sanar da ni, ni kuma na taka na je na samu Hajiya na ce ta shirya mu je tare a yi komai a gabanta."
Sai ya É—an dakata falon ya yi shuru sai saukan numfashin mutane.
"Ko ba haka a ka yi ba ke Bahijja?
Ya faÉ—a ya na kallonta sai ta dago kanta ina kallonta ban ga alamun nadama a cikin idanuwanta ba.
"Haka ne. Amma ai nima ba a ji zagina da.."
"Ban tambaye ki ba."
Ya daka mata tsawa sai ta yi shuru.
Ni ya kallah kafin ya koma ya na kallon ita Anty Bahijjan É—in
"Ina jin ki yanzu ki faÉ—a min farkon abin da ya faru."
Jin haka yasa ta gyara zama ta na rattabowa har da ƙarya wai na zazzageta. A cewarta mganar asiri ba ita ta faɗa ba yar'uwa Ma'u ce da ta zo gai da Gimbiya a asibiti ta ce sai an bi a sannu saboda zan iya zubar da cikin gimbiya.
"A cewarta daman halin Sadiya ne shige shige. Tun da dangi mamanta su har shaidan bin bokaye aka yi musu. Ban san da labari ba sai ga shi ta na faɗa min ni kuma na ga yar'uwanta ne tare suka tashi ta fi kowa sanin Sadiya shi ya sa na yarda. Sannan da na zo ina mgana sai Gimbiya ta ce ai taɓa ganin Innarta ta kawo mata wasu maganguna ta na tunanin na asirin ne. Ni me na faɗa? Duk abin da ya faru ne na faɗa sai a ga laifina?
Ta faÉ—a ta na hararata ni ko kallonta kawai na ke yi amma na kasa mgana saboda tsabar mamakinta.
"Shi likitan ne ya ce wani abu ne ita Saudatun ta ci da cikin ya kusa zubewa?
Ya katse mata mganarta sai ta fara kame kame.
"Bai ce ba amma ya ce ta ci wani abu da cikin ta bai karɓa ba."
"Sai kuma ke kika ce ita Sadiya ce ta yi sanadin hakan?