← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 89

Sashe 6

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni fa kwata kwata kalamansa sun daina wani burgeni. Shi ya sa na yi masa ba kan,  ina kallonsa a ɗage bai sani ba ya fara karyawa ya na min hira sama sama ina amsa shi, sai da ya ce min ƙila gobe ya shiga kaduna.

Sai kawai na gyaÉ—a kai kafin na ce" Allah ya kaimu."
Ya amsa da Amin na ga alaman yau ya ɗan saki jikinsa ba kamar jiya ba. Ya na cikin karyawa na ji buga get na san Saude ne sai na mike na ce masa bari na je na buɗe ina jin Saude ce illau ko ita ce tare muka dawo falon ta rankwafa ta na gaishe da Yallaɓai ya amsa mata har ya na tambayan mamanta ta ce duk suna nan lafiya.

"Sai yaushe za ku koma makaranta ne?

Na faÉ—a ina komawa in da na tashi na zauna.

"Ranar monday."

Sai na gyaɗa kai ban yi magana ba ita kuma sai ta shige ciki ta bar ni da Yallaɓai ya na karyawa har sai da ya gama ana ta ma kiransa a waya ya ce min Musbahu ne, ni ya tura na koma bedroom na ɗauko masa key ɗin mota har ga Allah na so na duje ne na ki masa rakiya amma ya manne min dole na yi masa rakiya kamar yadda na saba amma na kasa iya ɗaga masa hannu kamar yadda na saba sai na ke ganin kamar in na ɗaga masa hannu na cucu kaina wata fa zai je gani? Watan ma wacce ya raba min kanshi da ita shi dai ya ɗaga min hannu na yi masa ya ƙe ya na fita da motar na shige ciki na rufo kofar, Ina jin sa ya rufe get ɗin sannan ya koma motarsa ya fice.

Ina komawa cikin gida na ga Saude a kitchen ta fara haÉ—a wanke wanke kallonta na yi kafin na ce" Kin karya ne? Sai ta gyaÉ—a min kai ni kuma kawai sai na bi kofar da za ta maidani cikin bedroom É—ina wayata a hannuna ina faÉ—in" In dai kina jin yunwa akwai ruwan zafi ki sha tea kin ji ko?
Sai ta gyaɗa min kai ni kuma na wuce ɗaki na koma kawai na kwanta waya a hannuna na kasa buɗe data saboda ba na son na ga wani abu da zai ɓata min rai shi yasa na ƙi taɓa wayar ma.

Ina nan kwance a kan gado ina ta faman juye juye daga kudu zuwa arewa. Gabaɗaya zuciyata ba daɗi har hasaso Yallaɓai na ke yi ya na can shi da Gimbiya suna hira suna dariya. Kai kishi bala'i ne na kasa sukuni kamar zan haukace fa, in na runtse ido Yallabai na ke gani da Gimbiya sheɗan su kawai ya ke nuna min gabaɗaya na kasa sukuni kamar zan mutu haka na ji saboda zafin da zuciyata ke yi, ina cikin wannan halin Marwa ta zo zuwanta ne ya tsamo ni daga haukacewa na fara sumbatu saboda kishi.

Marwa ta daɗe ita ta yi mini girki sai mangariba ta tafi Saude daman tun wajen azahar bayan ta gama aikinta ta tafi. Itama na ɗibar mata cake da yawa na ce ta je gida su ci da ƙannenta.
Na yi na yi Marwa ta kwana ta ce min ba ta tambayi Babanta ba na ce zan kira waya ta ce a'a za ta dawo gobe in ta zo É—aukan kayanta.
Ina hararanta na ce" Marwa tawaye za ki yi min?
Ta na dariya ta ce" Umma can gida ya fi kusa da asibitin da zan yi pratical ne amma zan dinga zuwa Allah kuwa."
"Ki dawo nan mana sai Yallaɓai ya rika kai ki in zai fita office."

Sai da na faɗa sai kuma na kwaɓi kaina daga jiya Yallabai ya tashi daga wannan wanda na sani yanzu namu ne ni da wata ba ni da wannan ikon a kan shi kamar baya. Hakanan na ba ta 1k muka yi sallama na ce ta gaida Ya Aina. Sannan na ɗibar mata na ta cake ɗin har da kazan jiya na ce na Anniversy ne. Ni daman kazan ko a bakina saboda gani na ke yi kamar kazar angwancin Yallaɓai ne  saboda ya ƙure ni. Sauran na bar ma su Jidda amma ni na haramta ma kaina cin kazan nan.
Bayan tafiyarta na idar da sallar mangariba Ya Ainan ma ta kira wayata ta na faÉ—a min Ya Balki ta gaya mata wani labari wai Babansu jidda ya kara aure sai na tabbatar mata ita kanta ta jinjina har sai da ta ce min" Sadiya kishi akwai zafi sai kin daure."

A raina na ce" Tabbas kishi akwai É—aci ba ma zafi ba."

"Yaushe ne tarewar? A ina za ta zauna ita matar Balki ta ce min wai  yar nan Rano ce ko?

Sai na amsa mata kafin na ce" Ban san in da za ta zauna ba."
"Ko nan gidan zai haÉ—e ku?
A firgice na ce" Wani gidan Ya Aina?
Ganin yadda na zabura ne ya sa ta yi dariya kafin ta ce" Nam ma Sadiya."

Yaƙe na yi kafin na ce" Danƙari. Ai shi kan shi Yallabai ya san a nan gida ba Vacancy ɗin wata mace bayan ni ba ma zai fara ba."
Yaya Aina na ta min dariya kafin mu yi sallama ta ce ina Marwa ko nan za ta kwana sai na ce ta taho ai tana hanya ma, daga nan muka yi sallama duk da ba na so haka nan na buɗe data saƙonni wasu na ture wasu.
Ban duba na group É—in mu ba domin na ga mgana har 50+ sai Ma'u da ta yi min mgana ta Pc ne ya É—au hankalina da sauri na shiga na ga mgana ta yi a takaice.

"Uhm Sadiya kenan. kin san ko za ki yi ma wasu wayau ban da ni ko?

Haka kawai ta rubuta, na karanta na fita saboda ba ni da ta cewa sai wata lamba da ta min mgana ina shiga na ga an ce.

"Sadiya Shema'u ce ashe kuma Yallaɓai an yi tsiyar irin ta su ta maza."
Da uban emojin dariya kamar abin dariya ne ya faru wani malolon abu ya ƙara tokaremin zuciya daman ai ya na tokaren tasowa ya ke yi lokaci bayan lokaci in na tuna da abin.
Da kamar zan yi mata banza sai kuma na fasa a raina na ce in na yi mata shuru za su ce sun yi nasara a kaina ni kuma in sha Allahu Nasaran ce a kaina ba zan taɓa bari su yi ba.
Kawai sai na shiga na ba ta amsa dai dai da kalamanta.

"Tsiyar me? Umarnin Allah ne fa kike kiran shi da tsiya kuma na gode ma Allah ni ya fara sani kafin wata ko banza ina da wannan darajan. Sannan da ka je ka iske ai gwara kai a kawo maka ya fi daraja."

Daga ita har Ma'un na yi ma mganar a dunƙule ina kuma gamawa na yi blooking ɗin ta ba na son wata damuwa ta barni na ji da abin da ya ishe ni ma na shiga group na mu na gida ina ganin suna ta fatan alheri amma na kasa amsa su. Ya Murja dai sai da ta taɓa halin wai topha Yallaɓai dai ya ƙara aure? Ya Hamza ne ya yi mata mgana da cewa haramun ne! Ku fa mata kuna da matsala.
Ma'u ta karanta saƙona amma ba ta yi mgana ba ina tunanin ba ta tsammaci haka daga gare ni ba ne. Ta so na yi ta hauka ita kuma ta samu abin yamaɗiɗi da ni a duniya to da ikon Allah sai dai sharrinta ya koma kanta in sha Allahu.

Muniira ta sake turamin wani saƙo da ya ɓata min rai.
"Kin tabbata kina lafiya ta Yallaɓai?
Ta sani amma ta kasa faɗa min in da gasken ne ban ji labari haka daga su har Yallaɓai za su yi ta raina min wayau a fakaice.

"Ban sani ba."

Amsar da na maida mata kenan daga nan na rufe data na koma kawai na yi tagumi ina ganin lamarin kamar gaske kamar mafarki. Har to sai yaushe ne Yallaɓai zai gama wasa da hankalina ya faɗa min! ? Na ga kamar ba shi da niyya sai dai zan jira shi har zuwa tsawon lokacin da zai ta raina ma kansa wayau in da a baya ne kafin ya dawo ma yi waya sama da sau uku amma yanzu in na ma tuna shi raina sai ya ɓaci domin na daina tunashi shi kaɗai na koma in na tunanoshi sai tunanin Gimbiya ya gilmamin daga nan kuma sai na ji gabaɗaya Yallaɓan ya fita kaina gabaɗaya.
  
Bayan Sallar isha'i ina falo tare da yara bayan mun idar da salla wayar na hannun Baby ta na game kiran shi ya shigo sai ta wakilceni kafin ma ta kawo min sai ta ɗauka suka yi mgana ina ji kamar ya na tambayana ne sai ta ce gani can zaune ganin ta taso zuwa wajena ya sa na rarumo carbin da ke gefena na riƙe daman ina kan sallaya ne a lokacin ta na zuwa ta miƙo min wayar ta na faɗin.

" Umma Abba ya ce a ba ki."

Dai na gyaɗa kaina kafin na ɗaga carbin ina gyaran murya Uhm! uhm! Alamun ina uzuri ita kuma ba ta gane ba ta na ta ƙoƙarin kara min wayar a kunne Jidda da ke kan littafanta na makaranta na ture da kafata ita ta taso ta karbe wayar na ji tana faɗa masa Umma na jan casbaha ne Abba ban san me ya ce mata ta ce sai ya dawo sai da ya kashe wayar sannan ta kalleni ta na faɗin" Umma Abba ya ce a shigo da buredi ne?

"Duba in da saura mu gani."
Chapter 6 · 0% Book details