Sashe 1
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TKG*
01.
"SADIYA.."
Wannan karon a yanayin yadda ya kira sunana sai da na ji jikina ya amsa da ya sa kaina na ƙasa sai da na ɗago na kalle shi. Tabbas a cikin idanuwansa na hango kamar hawaye sun cika masa kwarmin idanuwa kuma na hango gajiya da haƙuri harda kunya a lokaci ɗaya.
"Sadiya.."
Ya sake furtawa cikin wani irin rauni. Raunin da har ina jin sautin fitar shi daga muryansa.
"Sadiya.."
"Ta.."
Ya sake faÉ—a ararrabe daga gani ya kasa sarrafa kanshi halin da ya ke ciki na neman tona masa asiri.
Ba na so ko É—aya na nuna masa na san labarin abin da ke faruwa yadda bai faÉ—a mini ba nima ba zan nuna masa na sani ba. Tabbas na yi dauriya domin a lokaci ji na ke yi kamar na zube a kan kafafuwana tsabar yadda suke rawa. Ina jin wani irin nauyin jiki wanda na zuciyata ne ya sakar ma gangar jikina.
Na yi iya ƙokarina kar ya fahimci nima a firgice na ke shi ya sa na gayyato mirmishi wanda ka na ganin shi gwara ma kuka a kan shi saboda ba daga ƙarƙashin zuciyata ya fito ba.
Ina yin mirmishin ina kallon fuskar Yallaɓai amma sai na ga yau ba na ganin shi da haske a idanuwana sai ya yi mini wani baƙi kamar ba Yusuf ɗina ba.
"Sadiya ta. Na dawo"
Ya faÉ—a ya na kallona domin tun É—azu idanuwanshi suna kaina ne. Ni kuma cikin rawan jiki da na zuciya na buÉ—e baki dakyar ina jin harshena na karkarwa a cikin bakina.
"Na'am"
Murya ta na rawa ina so na daidaita kaina amma wallahi na kasa. Kai jama'a kishi bala'i ne sai yau na sake samun tabbacin haka duk yadda na so a ro jarumta sai na ji na kasa ji na ke yi wani abu na min yawo a cikin jinin jikina. Kaina ya yi nauyi gabaÉ—aya ji na ke yi kamar zan faÉ—i saboda tsabar gigitar da na ke ciki saboda tashin hankali.
"Na'am Yallaɓai n.."
Sai sauran kalamai na suka maƙale a fatar bakina. Na kasa iya kiransa da yau ɗaya da Yallaɓai na. Yau ɗaya da na kalle shi ina jin dukan zuciya da cewa Yallaɓai yanzu ba nawa ba ne ni kaɗai ya tashi da ga mallakina ni ɗaya ya koma mallakinmu ni da wata. Ashe haka sauran mata da dama suke ji in an yi musu kishiya? Na ɗauka in Yallaɓai zai ƙara aure ba zan wani damu ba ashe ashe kishi ba a yi masa da wasa. Tabbas Ubangiji ne ya hallici mu mata shi kuma ya sanya mana kishi a zukatanmu shi kuma kaɗai ya san dalilin shi na haka.
 Balle irin auran da Yallaɓai ya yi ban shirya ba. Lamarin ya zo min ne cikin bazata da tsamanin abin da ban taɓa tsammani ba. Ban taɓa zaton a wannan yanayin ne zan fara raba Yallaɓai da wata ba. Ban taɓa tunani ko hasashen haka ba.
Takalmin da ke kafata har ya jiƙe da zufa haka wayar dake hannuna tana maiƙon zufan da ke fita daga jikina
Yallaɓai ya fara taku ɗaya, biyu zuwa gare ni da sauri na yi baya a nufina na guje ma haɗuwar jikina da na shi domin yau kawai na ji ba na so Yallaɓai ya kusantoni. Ƙokarina na yi baya amma jikina ya ƙi ba ni haɗin kai saboda a firgice na ke. Bayan da na yi da sauri ya ja takalmin kafata ya turkuɗe na yi baya zan faɗi ban san lokacin da wayar hannuna ta faɗi ba, sai na ji Yallaɓai ya rike ni gam lokaci ɗaya yana kallona kafin ya ce.
"Lafiyan ki kuwa?
Ya faɗa ya na mai kallona cikin fitan hayyaci na kalle shi sai na ji in na cigaba da kallonsa zan iya fashewa da kuka har na tona asirin zuciyata. Ya ji jikina na rawa ya kuma ya fahimci duk a firgice na ke ba na cikin hayyacina, shi ya na ƙoƙarin ya ta da ni tsaye ya raɓa ni da jikinsa ni kuma hannayen nashi na ke kallo domin sai na ga kamar sun zame min baƙi a cikin idanuwana yau ɗaya kawai sai na ji hannun Yallaɓai kamar baƙo a gare ni da ban san lokacin da na yi gefe ina mai kauce ma riƙonsa baa. Hannun kujera na dafe ina haki sama sama domin na ji tabbas numfashina na cijewa kamar ya na neman ya dawo wuyana.
Yallaɓai ya kalleni a tsorace ya sake kallona kafin ya ce" Sadiya? Kina lafiya?
Ya faɗa ya na ƙokarin ƙara matsowa kusa da ni da sauri na yi baya amma kuma ban saki hannun kujeran da ke gefena ba domin in har na yi gangancin saki ba zan iya riƙe kaina ba.
Sadiya ki yi jarumta Sadiya ki daure. Haka na ji wata zuciyar na faɗa min da ya sa na yi saurin ƙwato numfashina da karfi na sauke ajiyar zuciya ina mai kallon wayata da ta faɗi a ƙasan Tayels. Yallaɓai ya bi in da na ke bi da kallo shi ya duka ya ɗauko min wayar ya riƙe ta a hannun shi.
Kallona ya ke yi yana so ya yi mgana shima bakinsa ya yi masa nauyi kawai sai na miƙa masa hannu ya saka min wayar lokaci ɗaya yana faɗin" Kin tabbata kina lafiya?
Ji na yi kamar in balla masa harara in ko na buɗe bakina na tabbata sai na danna masa ashar na katsinawa. Amma sai ban yi haka ba, na sake gayyato mirmishi ina mai ɗaga masa alamun lafiya ta ƙalau. Ajiyar zuciya na riƙa saukewa a jejjere ina huro iska daga bakina domin na samu natsuwa daga ƙasan raina ina ta mamaita Innalillahi domin Allah ya sake ba ni jarumta.
Cikin ikon Allah na ji na samu natsuwa jikina ya daina rawa. Har na samu daman sakin hannun kujera na tsayu da kafafuwana.      Kallonsa na yi ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ba ni kaɗai ba shi kan shi ma a firgicen ya ke sannan ba natsuwa a tare da shi. Ban tsaya sake kallon shi ba na yi karfin halin wucewa wajen ledojin da ya ijiye na duka na ɗauka ina faɗin" Su Jidda sun gaji da jira har sun yi barci."
Na faɗa saboda gyara yanayina lokaci ɗaya ina ɗagowa da ledojin ta gabansa na wuce zuwa kan dining na ɗora ledojin amma ban buɗe su ba. Ina so na juyo amma ba na so mu sake haɗa ido da Yallaɓai.
"Ki tashe su mana."
Haka ya faɗa a sanyaye sai na juyo ina mirmishi kafin na ce" Sun riga sun yi barci fa? Ƙyale su kawai."
Shi kuma kawai sai ya saki hannayenshi ya wuce kawai zuwa falo ya na mai faÉ—in"Â Wannan babban rana ce a gare mu bai kamata mu yi murnan ba su a wajen ba."
Ya ƙarishe faɗa ya na buɗe kofar falon ya shige ni ban bi bayan shi ba ina ta ƙoƙarin yaji da abin da ke taso min. Ina jin sa daga nan ya na kiran sunanayen su Jidda daman ba ta da nauyin barci. Baby ma ba ta dashi amma ba kamar Jidda ba.
Tsayuwa na neman gagarata ya sa na samu ɗaya daga cikin kujerun falon na zauna ina sauke numfashi. A baya in yi ta ganin laifin matan da mazajensu ke ƙara aure su yi ta hauka sai da ya zo kaina na fahimci yanayin tabbas kishi ke haukata mata ya kuma sa ka kasa mallakan kanka, ina zaune a in da na zauna ya dawo falon tare da yaran dukkansu ya na riƙe da hannun su. Baby ce sarkin surutu sai faɗi ta ke yi.
"Abba yaushe ka dawo?
"Ban daÉ—e da dawowa ba Baby"
Ya ba ta amsa dai dai suna zama kan kujera mai zaman mutum huÉ—u.
"To ina ka je Abba?
Baby ta faÉ—a tana mai hawa jikinsa ya na shafa kanta ya ce" Na je Rano ne."
Ya É—ago kenan muka haÉ—a ido da shi sai na yi saurin kauda kai daman ina so na ji me zai ce? Tabbas can ya je kuma ya dawo da kyakyawan tsaraba na ce a raina a lokacin da na ji Baby na tambayan shi ya siyo mata tsaraba. Sai ya nuna mata ledojin kan Dining ya na faÉ—in ga tsaranbanta ca.
 Daga shi sai Baby suke hiran su ni da Jidda kamar ba ma falon ita ta na gefe sai hamma ta ke yi daga gani barcine a idanuwanta ni kuma ina zaune ina fama da turirin zuciya.
"Duk Umma ce ta haÉ—a wannan?
Ya faÉ—a ya na nuna cake É—in da ke gabansu.
Da sauri Baby ta ce" Umma ce da Yaya Jidda. Abba ni ma zan ci Cake É—in"
Ta faɗa tana leƙa Cake ɗin . Na ji ya kalleni a cikin jikina ni kuma sai ban juya na kalle shi ba, ina kallon gefe ina ƙokarin sakin fuskata na nuna komai bai faru ba amma ina jin kamar ba zan iya nuna komai ɗin bai faru ba.
Â
"Sorry Jidda barci ko?
Na ji ya faÉ—a sai na ji ita kuma ta na faÉ—in" A'a Abba."
"To Hammar kuma ta mane ne Jidda?
Ya faÉ—a ta gefen ido na kalle su sai na ga ya na jan hancinta ita kuma tana mirmishi. Yana É—ago kansa zuwa gare ni na yi saurin É—auke kaina kamar ban san suna wajen ba.
Ƙila ya daɗe yana kallona domin falon ya yi shuru sai karakainan Baby kawai ke tashi a falon ni kuma na yi matukar ƙokarin sassauta fuskata.
"Yaran nan fa na jin barci ta so su mu yi abin da ya kamata su je su kwanta."
Ya faÉ—a a sanyaye. Ni kuma sai na yi kamar ban ji ba sai na maida kaina can gefe kamar ina kallon Tibi ahalin Tibin ma a kashe ta ke.
"Sadiya"