Sashe 62
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru na yi masa kawai saboda ba na so maganar ta yi nisa. Ya zo ya rumgumeni ya sumbace ni a goshi ya na faɗin" Sai na dawo." Na yi masa fatan dawowa lafiya ina ganin shi sai da ya shiga ciki ya duba Gimbiya sannan ya fice, ina aiki ina danne abin da ke ta so min a ƙasan raina ina ƙara karfafama kaina gwiwan da komai ma zai wuce in sha Allahu, duk rashin son aikina yanzu na zage Saude na makaranta sai al'hamis zuwa lahadi ta ke zuwa. Ko kafin Gimbiya ta tashi barci na gama duka aikina har na yi wanka sai da na fita falo na ganta zaune muka gaisa cikin faram faram ɗin da muka saba. Maaganar abin da za ta karya na yi mata sai ta ce.
"Madam in da zan samu kunu da na so."
"Ina da sauran garin kunun ai bai ƙare ba sai na dama miki."
"Na gode Allah ya saka da alheri."
"Amin. Bakomai."
Na faɗa ina kallonta, sai na ga ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa sai na dawo ina faɗin" Na manta ya jikin? Yallaɓai ɗazu ya ke faɗa min jiya cikin dare ciwon ciki ya taso miki.?
Sai ta kalleni kafin ta yi mirmishi ta na faÉ—in" Laa ba fa wani abu ba ne, wai sai da ya faÉ—a miki?
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya ƙara lafiya. Ina fatan dai ba matsala?
"Babu matsala, kawai cikina ne ya É—an lalace amma ba matsala "
"Ayya sannu. Allah ya ƙara lafiya"
Ta amsa da Amin sai na ce ta kunna Tv mana zaman shuru ba daɗi sai ta ce ba ta son hayaniya. Sai na ƙyaleta na tafi kitchen na ɗora mata ruwan zafin sannan na ɗauko garin kunin na dama, tsamiyar tawa ma kaɗan ta rage ita kenan na yi mata amfani da shi har garin kunin ma ya ƙare daman Maman Saude ce na aika ma gero ta daka min dole itama zan ƙara yi ma mgana ta sake daka min tun da Gimbiya kokon ta ke sha ai saboda ita ne gero har tiya goma Yallaɓai ya siyo ya ijemin ni dai ya san ban cika shan kuni ba in dai ba azumi ba, zai yi wahala na sha kuni sai dai kuma in ba ni da lafiya Yallaɓai ma sai irin shekara bayan shekara gaskiya tun da na ga an kawo gero na san saboda wacce aka kawo shi.
Bayan na dama mata ban saka mata siga ba saboda ba ta so na kuma kawo mata har falo, ta karɓa ta na ta min godiya. Mun ɗan zauna ni da ita muna ɗan taɓa hira sama sama kafin ta gama shan kokon ta ce min za ta je ta sha mgani ta ɗan kwanta na ce mata to. Tun da ta shige ciki sai ni kaɗai a gida sai can da rana sai ga Naja'atu ta zo itama muna gaisawa ta shige ciki, daman haka suke yi da sun zo domin ita daman suka zo za su shige ciki.
Ni daman muna ta waya da mai hijabai za a kawo min wasu sannan na saka a ɗinka ma Amina domin ta ce ta yi talla ana so. To shi ne za a aika mata kaduna ni ma za'a aiko min dashi, da daddare tuwon shinkafa na yi miyar ganye Naja'atu sai mangariba Direba ya zo ɗaukanta ashe ƙasar za su bari ita da mijinta shi ya sa ta zo yi ma ƙawar ta ta sallama nima da suka fito ne Gimbiyar ta rako ta ta ke faɗa min na ce Allah ya tsare hanya.
Yallaɓai ya ɗauka na bar maganar sai ga shi ya na dawowa, bayan ya shiga ɗaki na ya yi wanka ya fito falo ya ni da shi da yara har da Gimbiyar muna cin abinci ita kaɗan ta ci tuwon miyan ne ta ɗan sha da yawa. Ni da Yallaɓai ne muke hira ita kuma daman yara ne abokan maganarta, ban sanin musu ba amma ba ta sakin jiki ta yi hira da shi in dai ina wajen gwara shi ma ya na ɗan janta da mgana ita ce za ka ga ta na wani sunne kai, amma na san in sun shiga ciki ba za su rasa yin hiran su ba.
Ni da Yallaɓai mun daɗe a falo muna kallo daman in dai ya ga ana Horror film sai ya ja ni ya ce mu kalla tare. Yara tuni sun shige ciki Gimbiya ma ana fara ta tashi ta ce ba ta kallon fina finan tsoro har ya na zolayanta da cewa" Ke ba Jaruma ba ce Daugther amma zan koya miki kallo kamar yadda na koyar da Sadiya ta."
Banza da shi ta yi ta shige ciki ta na yi min sai da safe ta bar ni da shi ya na ta takalata da hira ni ma da na gaji sai na fara yi masa hammar ƙarya, na kuma ce masa ina jin barci zan je na kwanta har na miƙe sai na kalle shi kafin na ce.
"Sai da safe."
"Sai na shigo dai ko?
Ya faÉ—a hankalin shi na wajen kallo.
"Ka manta! Ai a É—akin Gimbiya za ka kwana."
Sai ya É—ago ya na kallona kafin ya ce" Ba na ce a bar mganar ba."
"Ba za a barta ba. Domin da gaske na ke yi."
Kallona ya yi ni kuma sai na juya ina ƙara faɗin" Mu kwana lafiya."
Na yi wuceta ciki Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na koma É—aki na sauya kaya zuwa na barci ina shirin kwanciya sai ga shi ya shigo sai na kalle shi kafin na ce" Ba mun yi sallama ba?
Karisa shigowa É—akin ya yi ya na faÉ—in" Sadiya me ya sa kika yi hakan?
"Saboda hakan ne ya kamata. Ba ta da lafiya gwara ka riƙa kwana a kusa da ita."
Sai ya yi shuru bai yi mgana ni kuma sai na zauna a gefen gado ina faÉ—in" Kar ka damu ba matsala ni na ce ai ka je."
"Kin tabbata ba matsala?
Sai na kalleshi ina jin takaici in Yallaɓai ya yi min tambayar nan daman zai yi min kishiya ne ya ce min kuma ba matsala. Ban nuna masa ba illa ƴar dariya da na yi kafin na ce" Na ce ba matsala ka je kawai."
"Na je bakomai?
Sai na gyaÉ—a masa kai sai na ga ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Na gode. Allah ya tashe mu lafiya."
"Amin."
Takowa ya yi zuwa gaba na ya duƙa ya na sumbatar goshina.
"Sadiya."
Ya kira sunana na É—ago ina kallon shi kafin na yi mgana ya ce.
"Sai da safe."
"Sai da safe."
Na mayar masa da martanin mganarsa har ya juya zai tafi sai gashi ya ƙara juyowa ya na kallona kafin ya ce" Ko za ki ɗauko yara ne?
"Bar su kawai yau ni kaÉ—ai zan kwana."
Sai na ga ya kalleni ni wannam makircin na Yallaɓai ya fara ba ni dariya wai yau ya saba tafiya ya bar ni? Da ya ke barin gidan ma gabaɗaya fa? Duk bai yi haka ba sai yau.
"Ka je kawai Yallaɓai bakomai"
"Kin tabbata?
Sai kawai na kwashe da dariya kafin na ce" To ko da wani abun akwai abin da za a fasa ne?
Sai ya ware min ido ya na kallona ni kuma sai na cigaba da faɗin" Ba abin da zai canza Yallaɓai, mene ne a cikin kwana? Tun da na yi sharing ɗin ka da ita an gama mgana. Kwana a ɗakin ta ba zai rage ni ba kuma ba zai kare ni ba saboda haka ka je kawai sai da safe."
Ina gama faɗin haka na koma na kwanta ina mai rufe kafafuwana da bargo har ina lumshe ido, shima ganin haka ya sa ya ja siraran kafafun shi ya fice na bi shi da kallo daga wutsiyar ido na sai da ya fice ya jawo min kofa sannan na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙara jinjina halin Maza in suka ƙara aure. Na daɗe ban yi barci ba sai can kuma barcin ya ɗauke ni har sai da na makara domin sai bayan da Yallaɓai ya dawo sallar asuba sannan ya tashe ni a cewarsa ya ɗauka na tashi ne.
Da safen ne bayan Gimbiya ta fito mun gaisa sai take ce min wai Yallaɓai ya ce na ce ya riƙa kwana a wajenta har ta koma na ce haka ne, sai ta kalle ni kafin ta ce
" Ba komai ai na ji sauƙi wallahi."
"Duk da haka dai gwara ya na kusa da ke."
Ina kallonta ta na ta mirmishi amma ba ta ce komai ba a raina na ce munafukai to daga ita har shi ɗin suna ji da munafuci da gulma. Ranar an yi baki daga Rano, Yayarta Mardiya da wasu ƙannen Hajiyar Tafida suka zo duba ta, ni na yi musu girki suna ta min godiya Yayar tata har ɗaki ta same ni ta yi min godiya a kan yadda na ke kula da Gimbiya na ce bakomai ai an zama ɗaya sai La'asar suka bar nan zuwa gidan Nene. Ranar asabar kuma Anty Maimuna ce ta zo da yaran ta nan suka yini a ɗakin Gimbiya ni dai iyakata na girki na ba su shi ne aiki na sun ƙule a cikin ɗaki ana hira ana shewa saboda can da Yamma ma Anty Bahijja ta zo gidan. Ranar lahadi ma an yi baƙi ƙawayen Gimbiyar su biyu sun zo duba ta suna ta min taɓe taben fuska ni kuma ban ba su fuskar da za su rena ni ba ni da gidan mijina ba matar da ta isa. Suma ciki suka bi ta ranar ma Dambu na yi kuma sun ci sai la'asar suka tafi a daran ranar aka kawo min hijabai na Amina ma mun yi waya a ranar aka tura mata na ta.
Washegari litini kuma ina da komawa asibiti kuma magunguna sun kare shi ya sa na shirya na ce ma Yallaɓai zan koma asibiti amsar da ya ba ni lokacin ta ƙara sakani mamakinsa.
"To dole sai kin koma yau É—in ne?