← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 89

Sashe 49

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sake tambayata sai na yi saurin shanye kukan da ke taso min har ina yin mirmishi wanda na aro shi na yafa a saman fuskata duk domin na kauda ma Kawu tunanin cewa wani abu ya faru. Sai dai kash ya riga ya fahimta sai dai na basar kawai.

"Allah ba komai Kawu."

Na faÉ—a ina masa mirmishi sai kawai ya gyara zama kafin ya ce" Na ji kin ce dai bakomai amma ban yarda ba komai É—in ba Sadiya."
Ina kallon shi na buÉ—e baki zan yi magana sai ya dakatar dani da hannu lokaci É—aya ya kira sunana.

"Sadiya."

"Na'am."

Kai tsaye ya kalleni kafin ya cigaba da faɗin" Kin san dai ni san ba zan taɓa yarda wani abu bai faru ba ko? To gwara ki yi shuru a tafi a wani abu ya faru ni ba zan matsa miki sai kin faɗa min ba amma kuma ba shi zai hana na ƙi baki haƙuri ba"

Sai na kalleshi amma ban yi magana ba, ni ko a gida kowa ya sanni ba ni da daɓi'ar kai ƙaran miji duk abin da ya yi min a cikin gida za  mu yi ta ƙare shi ya sa a yanzu na ke jin nauyin furta cewa Yallaɓai ya yi min kaza, kamar yadda ya ce ne ina mgana tuni za a ce zafin kishi ne ya sa na ƙi kwantar da hankalina shi ya ma faɗa da bakin shi ballatana wani daga waje.

"Sadiya."

Ya katse min tunani sai na É—ago ina kallon shi.

"Ki yi haƙuri."

Sai na gyaÉ—a kaina kafin na ce" Bakomai Kawu."

"Ban san me Tafida ya yi miki ba. Amma dai koma mene ne don Allah karki riƙe shi a cikin zuciyarki. Ba wai ina kare shi domin ya na nawa ba. Kema tawa ce wallahi. Sai dai ba shi zai hana na faɗa miki wata gaskiya ba."

Na É—ago ina kallon shi, ba tare da na yi magana ba..

"Sadiya Tafida ya na sonki. Kuma duk macen da zai aura ko anan gaba sai dai su biyo bayan ki. Haƙuri za ki ƙara saboda kin san mu maza in muka ƙaro aure sai wasu canji canje su yi ta faruwa haka Allah ya hallicemu mu Maza wani lokacin muna da son kai da Matan alheri. Ki yi haƙuri ki yi masa uzuri na tabbatar miki da cewa ke ce giwar mata a wajen sa."

Ina kallonsa ne amma ni kalamansa ba su wani kama zuciyata ba, shi kuma ganin kamar ban yarda da shi ba ya sa ya jinjina min kai.
Sai kawai na yi mirmishin takaici kafin na ce" A da kenan amma yanzu Gimbiya ta sha gaba na."

"Ba ta sha gaban ki ba Sadiya. Ai ke ba macen da ta isa ta sha gaban ki a wajen Tafida Allah."
 
Mirmishin na sake yi ba tare da na ƙara mgana ba. Ni kaɗai na san yanayin da na ke ji a cikin zuciyata kawai dai ina dannewa ne.

"Ina da dalilina masu ƙarfi da ya sa na faɗi haka. Ba wai kuma don ki ji daɗi ba sai zallar gaskiya. Tafida fa kin san tare muka tashi dashi akwai wasu abubuwan da a mu'amala ne muka karanci juna ba ta hallaya ba. Ki amince da cewa ke Giwar mata ce a wajensa. Ki sani ke auran saurayi da budurwa kuka yi Tafida ya fara sonki tun zuciyarsa na da danƙo ya zauna dake zaman aure na shekaru zuciyarsa na buɗewa a kanki. Ki sani soyayyar da ya ke yi miki ba ya yi ma Amaryansa da ya aura. Bar ganin wai ko sun daɗe tare. Ba zan ce miki ba shaƙuwa tsakaninsu ba akwai amma ba so ba ne, ba kuma zan ce miki yanzu da suke zaman aure zuciyarsa ba za ta ribace shi za ta ja shi zuwa gare ta ba Amma ki sani ko ta ja shi ba za ta iya zurfin kai shi ta ki mazaunin ba. Shi ya sa na ce ki yi haƙuri ki yi masa uzuri wataƙila halin ɗan adam ne na ajizan ci kuma daman shi zaman aure zo mu saɓa ne kuma zo mu sulhunta."

"Haka ne"

Na faÉ—a ina jinjina masa kai.

"To kin gani. Ki ƙara hakuri. Amma fa ba shi zai hana in ya yi miki ba dai dai a ci ubansa ba."

Sai da na yi dariya shima dariyan ya yi kafin ya ce" E mana ai ba wu ce duka ba."
Ya na mgana ya na danna wayarsa sai ya kalleni kafin ya ce" Kin ga sai yanzu na samu wayar ta shi."
A speaker ya saka kiran har sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka murya a shaƙe daga ji barci ma ya ke yi.

"Ya a ka yi ne."

"Ban sani ba. Mallam watssake."
"Me ya faru ne?
"Ga ni a gidan ka."
Cikin muryan barci Yusuf ya ce" Wani gidan kenan?
"Wanda na fi sani."
Kawu ya bashi amsa lokaci É—aya.

"Gidan Sadiya.?
Kafim ma ya bashi amsa ya yi saurin cewa"Ka ƙariso nan mana ina nan ni."
"In ƙariso ina?
"Gidan Daughter mana. Daman ba ka taɓa zuwa ka ga gidan Amarya ba."
"Wacece kuma wata Daughter."
Sai da ya yi shuru kafin ya ce" To Saudatu."
Tsaki kawu ya ja kafin ya ce" Tafida kana da sanabe wallahi. To ba zan ƙariso ba in za ka zo ina jiran ka kazo in kuma ba ka zo ba sai ka faɗa min na kama gaba na."

"Kawu."

"Na'am Tafida"

"Gani nan zuwa."

Daga haka shi daga can bangaren ya katse kiran duk ina zaune in jin su, Kawu sai masifa ya ke ya na faɗin" Wai ka auri mace amma kana kiran ta da wata ɗiyar ka? Tafida ba shi da hankali fa, kai suna ba na uwarka ba na ƙanwar uwarka ba."
Ni dai ina ta dariya, mun É—an cigaba da hira sama sama har ya ke faÉ—a min ya zo duba wani fili ne a nan cikin gari.

"Ko dai auren ya tashi ne Kawu za a yi ma Amarya ginin gida."

Na faÉ—a ina masa dariya da sigan zolaya.

"Ko Aure na yi ai ban iya barin Rano Sadiya can a ka haife ni a can kuma nima zan gina nawa Ahalin in sha Allahu. Kawai dai ina siyan filaye ne anan cikin gari saboda Ajiya ne in ka bar kuÉ—in kuma za ka ksshe su ne a banza."

Na ce haka ne, shi da kanshi ya ke faÉ—a min ya siya filaye anan garin huÉ—u kenan kuma takardun ma ai suna hannun Tafida na yi ta jinjina kai ina mamaki lalle Kawu Abba ya tara ko na ce ya na kan tarawa.

"Kawu Allah ya sa ka samo mana mata wannan shekaran mu gwangwaje."

Ya na mirmishi ya kalleni kafin ya ce" Amin Sadiya. In sha Allahu nima ba na so na wuce wannan shekaran addu'a za ki yi min Allah ya ba ni tagari matan ne na wannan zamanin duk sun zama sai a hankali."

"Allah zai kawo ta gari in sha Allahu."

Ya amsa da Amin kafin ya ce" Na ga ma wata iri a gidan ki kwanaki ina ta so na yi miki mgana ayyuka suka sha kaina.'

Cikin mamaki na ce" Iri? Wani iri!? Sai ya kwashe da dariya kafin ya ba ni amsa an kira wayarsa sai kawai na tattara kwanukan da ya karya na fice na bar shi a falon ya na waya. Ina kitchen ina ta mamakin to wacece Kawu ya gani? Ko Saude ce? Wata zuciyar ta kira min sunan ta, sai kuma na tuna ai ya san Saude tunda ya na yawan zuwa gidana kuma ya na ganinta duk a iya tunanina na kasa gane wani iri ne wannan ya gani a gida kuma har ya yaba. A cikin raina ina fatan Allah ya sa ta gida ce, ina ganin mutumcin Kawu Abba ba domin ya na kawun Tafida ba sai domin ya na da kyakyawan halin da duk macen da ta  same shi ta more.

Ban zauna ba na fara gyaran Kitchen domin Saude ma sai ta dawo daga allo za ta zo ni kuma ba na so na zauna in na zauna zai yi wahala na sake tashi, ina aikina gefe ɗaya kuma na haɗa tea ina kurɓa ko zuwan Yallaɓai ban ji ba, sai jin muryansa na yi a saman kaina lokaci ɗaya.

"Madam ina kwana."

Sai na juya na yi masa kallo É—aya na É—auke kaina na daÉ—e ban gan shi ba tun daren ranar da muka yi faÉ—a da shi.

"Ina kwana."
.
Na mayar masa da gaisuwan shi kamar ba na so, na kuma cigaba da aikina na ma manta da wanzuwar shi a wajen ya gaji da tsayuwa ya ga ko kallo bai isheni ba sai shi ne da kan shi ya gaji ya ce." Madam ko zan samu shayin nan na mganin mura? Mura ta kamani tun jiya."

Ya faÉ—a ya na jan hanci ko juyowa ban yi ba na ce" Za a kawo."
Daga haka na isa gaban gas na kunna ina ɗora ƙaramar tukunya gajiya ya yi da tsayuwa ya kama gaban shi, ni kuma na raka shi da tsaki ni yanzu Yallaɓai ya fita kaina tunda ya gama ba ni mamaki ya yi min abin da ban taɓa tunani ba ko da ya ba ni haƙuri zai yi wahala na manta kalaman shi a kaina.

  Ina cikin dafa masa shayin ne sai ga Marwa na kalleta ina faɗin" Sannu sai yau? Tun jiya ina ta jiran ki. Baban ki fa ya ce Umarni kawai zan ba da za ki zo "
Tana dariya ta ce" Umma jiya aikin dare na yi sai yau da safe na dawo gida."
"To kin ja ma kanki ba yau za ki tafi ba."
"Daman sai gobe."
Kallonta na yi kafin na ce" Sai dai jibi ko?
"Umma jibi ina da aikin Safe ne."

"Sai ki tafi daga nan É—in ko?
Chapter 49 · 0% Book details