← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 89

Sashe 63

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"E zan koma saboda magunguna sun ƙare gabaɗaya."

Sai na ga ya yi jim bai ce komai ba sai na gyara tsayuwa ina faÉ—in" Me ya faru?
Lokacin ma wanka na ke shirin shiga shi kuma ya na zaune a saman gado ya na aiki a system É—in shi.

"Ina tunanin in kika tafi wa zai zauna da Daugther?

Sai na buɗe ido ina kallon shi, daman ai a rina an saci zanin mahaukaciya. Kamar ya ɗauke ni aiki na kula masa da mata har da cewa ya na tunanin in na fita wa zai zauna da ita? Kamar wata jaririya mata ta ji sauƙi in ta yi baƙi ta na dariya da shewa in a waya ne haka zan ji ta na ta rera hira rai rei amma ya na faɗa min in na tafi wa zai zauna da ita.

"Ko za ki É—aga tafiyar ne zuwa Next week?

Kallon shi na yi irin kallon ba ka da adalci, wato na fasa zuwa asibiti na zauna a gida saboda matarsa da na ciki. Kawai sai na juya na hau tuɓe kaya ƙala ban ce ba, shima bai yi mgana ba na jawo towel ɗina na saka na fice na bar masa ɗakin, ina wanka ina jin takaicin Yallaɓai. Gaskiya wasu mazan ba su da adalci, haka kurum na fa sa zuwa ganin likita saboda matarsa? Duk mutumcin da na yi masa baya gani. To lalle ko yau zai sha mamakina daman da safen nan bayan ya dawo kai yara makaranta Salisu ya yi tafiya shi ne ya shigo ɗaki na ya zauna da na yi magana sai ya ce wai ta kwanta barci ne ba ya so ya dame ta, ni kuma tun da likita bai ba ni hutu ba sai ya zo ni ya dame ni shi ya sa na haɗe raina ban sakin masa fuska ba sai da na yi masa mganar zuwa asibiti shi ne zai tare ni da mganar banza.

Ko da na fito wanka baya ɗakin na yi tsaki a raina na ce shirme kawai. Agurguje na shirya na saka hijabina sabo dogo har ƙasa, na ɗauki jakata a hannu da takalmina ina fiowa sai ga shi ya fito daga ɗakin Gimbiya sai muka haɗe.

"Sai ina kuma?

Ya faÉ—a ya na kallona nima ko ina kallon shi na ce" In da na ce maka zan je"
"Asibitin?
Sai na ɗaga masa kai, na duƙa ina saka takalmi kafata na saka safa gajera na zamani na mata.

"Ba ki fasa ba kenan?

"Na faɗa maka magunguna na sun ƙare ya kamata na je."

Bai ce komai ba, nima ban ƙara mgana ba, na raɓa ta gefen shi na shiga ɗakin Gimbiyar sai na ganta zaune a gefen gado ta na duba wayarta alamu dai ta ɗan jima da tashi.
Gaisawa muka yi ina tambayanta jikin ta, ta ce min ta warke ba ta jin komai.

"Allah ya sauwaƙe."

"Amin Anguwa za ki je ne?

"E asibiti zan je."

"Ba ki da lafiya ne?

Ta faÉ—a ta na kallona sai na yi mirmishi kafin na ce" A'a kawai dai zan je ganin likita ne."
"Allah ya dawo dake lafiya."
Na amsa mata da Amin.
Kafin na ce" Akwai ragowan shinkar jiya na É—umama miki sai ruwan zafi in za ki sha ruwan lipto"
Sai ta amsa min da to shike nan.

"Za dai ki iya zama ke kaÉ—ai ba matsala ko?

"Ba matsala na fa ji sauƙi Madam yadda na ke jin kaina ko aiki ma zan iya yi."

Sai na yi Æ´ar dariya kafin na ce" Ai haka muke so. Amma aikin nan ba yanzu ba sai kin fita daga dokar likita."

"To na gaji da zama waje É—aya.'

"Lokaci ne. Kar ki damu. Sai na dawo."

Ta rako ni har falo sai na ga Yallaɓai zaune ya na kallo dining na nuna mishi ina faɗin" Ga abin karyawan ka nan"
"Wa zai zauna da ita?
Tambayar da ya ƙara jefa min kenan ni ko kai tsaye na ce.
"Ba ga ka fa? Me ka ke yi?
Sai ya sake kallona kafin ya yi magana na ce" Sai ka zauna da ita har na dawo tun da kana tsoron kar wani abu ya faru ko?

Kunya ya ji ko nauyi ban sanin masa ba. Bai yi dai mgana ba sai ita ce ta kare mganar da cewa ita fa bakomai za ta iya zama ita kaÉ—ai. Ni dai na wuce na bar su nan har ya na wani mikewa wai bari ya zo ya kai ni, na ko daba masa mgana ina cewa" A'a ka zauna kar ka barta ita kaÉ—ai."
Sai ya yi shuru ya kasa mgana na fita haraba shi ne ya biyo ni ya ba ni 5k da cewa in an rubuta mangaguna, na kira shi a waya sai ya yi min transfer. Da a raina na saka da wuri zan dawo gida amma tun da Yallaɓai ya ne mi raina min wayau na ce sai ya ganni shi ya zauna mana ai shi ya yi cikin ɗan renin wayau kawai.

Na samu ganin Dr. Aisha da na ce mata maganina ya ƙare sai ta ce ba matsala. Ta tambayeni al'adata ya daidai ta ko har yanzu ya na min tsallake? Sai na ce gaskiya wattani biyu kenan normal sai ciwo mara amma wannan watan ya zo min da sauƙi.

"Zan sake rubuta miki mgani guda É—aya shima dai na dai daita jinin al'adan ne kamar wan can"

Sai na amsa ta mata da to. Abin da ke zuciyata na faÉ—a mata.

"Dr kina ganin zan sake haihuwa?

Ba ta kalleni ba ta na rubutu a saman takarda lokaci É—aya ta na faÉ—in" In sha Allahu"

"Dr ni ko ɗaya ne na ƙara."

Na faɗa cikin rauni sai da ta ba ni takardan da ta rubutamin mganin sannan ta ce" Me ya sa kike son ki ƙara haihuwa? Ba kina da wasu ƴa'ƴan ba.?

"Ina da shi Dr amma dai ina so na ƙara ne saboda mijina mai son yara ne."

"Ko dai kina da kishiyoyi ne ana rigiman magaji?

Ta faÉ—a da sigan zolaya sai kawai na yi mirmishi kafin na ce" Ko É—aya. Ai shi ya na da wata matar ciki ma gare ta kila ta haifa masa namijin. Ni kawai ina son na sake haihuwan ne Dr namiji ko mace duka ina so."

" Zai ba ki in sha Allahu fiye ma da É—ayan. Ai na faÉ—a miki ba ki da wata matsalan da zai hana ki haihuwa. Lokaci ne kawai."

Nima na yarda da lokaci ne, kuma lokacin ne bai yi ba, in ya yi zan ƙara haihuwa nima.

Na tsaya a phamarcy cikin asibitin na siya maganin kuma sai da na kira Yallaɓai ya turamin Kuɗi duk da guda ɗaya ne, ni fa na saka a raina duk wani abu na haƙkin Yallaɓai na daina masa kara a kan shi in biyar ne sai na kira shi ya tura, sai da na hau adaidaita sannan na kira shi na ce zan biya gidan Ya Aina sai da ya yi jim kafin ya ce sai na dawo na san ya na so ya ce min na dawo da wuri ne ba fuska, na kusa gidan Ya Aina sai na ga ya turo min saƙo.

"Ni fa na fita, Daughter ita kaÉ—ai ce a gida. Don Allah ki koma gida da wuri."

"Ba zan koma ba."

Na faÉ—a a fili saboda haushi har mai adaidaitan sai da ya juya ya na kallona tsaki na ja na maida wayata jaka, a bakin titi na sauka na taka zuwa gidan Ya Aina sai dai ta ganni kwatsam ko da na je Marwa ba ta nan tana asibiti mun sha hira duk dai akan Marwa da Kawu Abba Ya Aina na faÉ—a min cewa ba matsala Marwa dai na so ya kuma kawo mata waya faskekeya ban ga dai wayar ba amma na ga kwalin wayar. Zuwan shi biyu kuma da alamu dai sun fara dai daita kan su da Marwa.

"Ma sha Allah na ji daÉ—in haka."

Na faÉ—a ina jin daÉ—i har cikin zuciyata.

"Ai ya ce ba ya so a ja lokaci suna gama fahintar juna zai turo manyan shi."

"Haka ake so. Allah ya nuna mana "

Ta amsa da Amin mun cigaba da hira a cikin hiran ne ta ke faÉ—a min Murja fa ta sani.
Cikin mamaki na ce" Ke kika faÉ—a mata?
Sai ta ce e, ranar ta zo gidan ta iske Kawu ya zo kuma ranar ya kawo ma Marwa shi ne da ta tambaya ta faÉ—a mata.

"Murja har ta na jin haushina wai Marwa ta samu miji ban faɗa musu ba, ni dai na yi ta ba ta haƙuri "

Cikin mamaki na ce" Ikon Allah. Kamar an saka ranar ne ba su sani ba?
Ya Aina ta ce ai na san halin Murja ni fa a raina na ji ban so Ya Murja ta sani ba, sai ta kai mganar gaba kuma shi ya ce sai sun dai daita ne manya za su sani ko Nene Yallaɓai ya ce bai faɗa mata ba saboda Kawun ne ya ce su dakata tukunna ban dai nuna ma Ya Aina wani abu ba ban jira dawowar Marwa ba na tafi gida wajen uku na rana saboda yara ba kuma saboda Matar Yallaɓai ba, ina hanyar komawa gida Yallaɓai na ta kiran wayata na ƙi dagawa sai da na koma Gimbiya ke ce min Ya na ta kiranta ya na tambayar ta ko na dawo sai na ce zan kira shi, na gane daman gidan ya ke so na koma shi ya sa da matarsa ta faɗa masa na dawo bai ƙara nema ba.

Saboda haushin shi da na ke ji da wuri na kwanta na ce kaina na ciwo, na bar shi da yara da matarsa ko da ya dawo ina ciki kwance ya dai shigo ya duba ni.

"Kin sha mgani?
Chapter 63 · 0% Book details