Sashe 5
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Balki sau biyu ta kirani Rahila ce wajen sau huɗu da ta ga ban ɗauka ba sai ta haƙura amma ban da Amina da saboda na cin kiranta sai da na ɗaga wayarta.
Tun kafin na yi mgana na ji karaÉ—inta a cikin kunnina sai da na runtse ido.
"Ya Sadiya wai wani Yallaɓan kike nufi ya ƙara aure?
Haka ta faɗa cikin sauri kamar ta na jira. Daman na san za a rina wai an saci zanin makauciya. Mirmishin yaƙe na yi kamar ta na gabana Amina ce ƴar'uwan da muka haɗa uwa ɗaya ita ce zan je gidanta na kwanta mata ina kuka ta lallasheni amma sai dai kash ta yi min nisa.
"Wai dai Yallaɓan na ki babansu Jidda kike nufin jiya aka ɗaura ma aure?
Haka ta sake faɗa jin na yi shuru. Cikin sanyin murya na ce" Shi fa Amina. Ai yanzu Yallaɓai ya zama namu mu biyu, ya tashi daga Yallaɓai na ni kaɗai"
Na ƙarishe faɗa kamar zan fashe da kuka domin ina mganar ina jin wannan abun da ya tokaremin a kirjina ya na motsawa ina jin wani irin zafi a ƙasan zuciyata zafin da a kan jin in an yi maka wani gagarumin rashi mai zafi ko ka rasa wani abu naka mai muhimmaci. To irin wannan zafin da raɗaɗin na ke ji ya na taso min daga ƙasan zuciyata.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un na shiga uku ni Amina Yallaɓai dai ya ƙara aure Ya Sadiya"
"E."
Na bata amsa a takaice jin ta ƙara jero wani salatin ya sa na yi saurin cewa" Ke miye na wani salati! Shirka ne? Umarnin Allah ne fa."
Daga can bangaren Amina ta sauke numfashi har ina jin hucin sa daga cikin wayar cikin ƙaramin sauti da wani abu a muryanta ta ce" Uhm ni mamaki ne ya ishe ni. Wallahi na kasa yarda"
"Uhmm."
Na samu kaina da cewa kawai. Nima É—in in zan ji kamar karya ne sai kuma na ji wani shashi na zuciyata na gasgata lamarin.
"To wai ya aka yi ne aure kwatsam ba sanarwa? Sai kawai mu ji an riga an É—aura aure Ya Sadiya.?
Takaici ya ƙara kamani sai kawai na gyaɗa kai kamar tana ganina kafin na ce" E nima kwatsam na ji Amina."
"Kai jama'a har yanzu na kasa yarda Ya Sadiya."
"Ki yarda Amina. Da gaske ne Yallaɓai kam ya ƙara aure."
Sai ta yi shuru nima sai na yi shuru kafin can ta ce" Allah ya kyauta. To wacece ya aura É—in?
"Ƴar'uwansa ne. Ɗiyar marigayi Tafidan Rano ne. Mijinta ya rasu wattanin baya."
Amina ta jinjina kafin ta yi fatan alheri daga karshe ta ce" Ki yi hakuri ya Sadiya ki kauda kai. Na tabbata duk wacce Yallaɓai zai auro wallahi a bayan ki ne."
Uhm kawai na ce ban yi mgana ba. To wani baya kuma, ai an gama mgana tunda an raba mijin gabaÉ—aya shike nan kuma.
Muna cikin waya Rahila na ta ƙara kirana ina katse na Amina na ɗauki wayarta itama tambayar ta farko shi ne wai wani Yallaɓan ne ya ƙara aure?
Kai tsaye na ce mata" Wani Yallaɓan kika sani? Abban su Jidda ba."
"Kai Sadiya fa."
Sai kawai na yi mata dariya kafin na ce" Wai me ya sa kuke tamtama?wallahi tallahi da gaske na ke yi."
Rahila ta jim kafin ta ce" Danƙari! Aure kuma bagatatan Sadiya? Yar wacece a Rano ya aura?
Itama bayanin Gimbiya na yi mata da sauri ta ce" Gimbiya? Haba na gane ta ita ce ya aura ɗin? Sai na ɗaga mata kai kamar tana ganina fatan alheri ta yi kafin ta ce" Sadiya an shiga wata ƙwaryan sai kin ninka haƙurin ki. Duk da ta bangaren miji ba ni da haufi a kan ki in sha Allahu ba macen da za ta kama kafarki. Allah ya zaunar da ku lafiya."
"Amin"
Na amsa mata da Amin sai ta ce" Yaushe ne tariyan! Ko har an taren ne?
Kai na fara girgizawa kafin na ce" A'a.."
"To sai yaushe?
"Ban sani ba Rahila."
Haka na faɗa kai tsaye domin da gaske ɗin ban sani ba fahimtar yanayin da na ke ciki yasa ta yi min sallama kawai amma ni a muryanta sai na ji kamar tausayina ta ke yi. Tabbas ni abar tausayi ce domin ya kamata a riƙa sara ma duk wata macen da aka yo ma kishiya saboda zafin abin ba wanda zai iya kwatanta yanayin shi sai ya faru a kanka. Sannan duk macen da ta shanye ya ci a kira ta jaruma ko sarauniya kuma a yabe ta a jinjinta domin ta yi matukar namijin ƙoƙarin da ba kowa ne zai iya yi ba.
Muna cikin waya da Yaya Balki ne Yallaɓai ya fito falon. Ganin shi ya sa sai na ce zan kirata zuwa anjuma a lokacin n nasiha kawai ta ke yi min tana nuna min na ƙara hakuri domin zan ci riban hakuri tunda ai ita an yi mata tana ta bani misali da kanta da ba ta da haƙki ga shi matar ma ta fita sun rabu da mijin kuma da ƴaƴa biyu a tsakaninsu.
Kamar Yallabai ya fahimci wayar da na ke yi saboda sai da ya kalleni kafin ya ce" Wannan doguwar wayar fa?
Ina mikewa na ce" Ya Balki ce muna wata mgana ne."
"Ok. Na ga Tiolet ba ruwan zafi. Kin saka a heater ne.?
Ban yi masa mgana ba na dai gyaÉ—a masa kai na yi wuce gaba ya biyo bayana a cikin tiolet É—in daman na ke saka heater É—in ni na je na jona masa sai ya ce na haÉ—a masa abin karya in ya yi wanka zai fita akwai mutanen da zai gani a office ne sai na amsa masa.
Daga Tiolet na ja birki a kitchen ƙwai kawai na sake soya masa. Na kwasa na kai dining daman akwai ruwan tea a fulas sannan ga kayan tea ɗin da buredi. A niyyata na yi tafiyata falon yara na zauna amma sai na danne zuciyata na zauna a saman kujeran dining ina jiransa na tsawon lokaci ina zaune ne amma ina tunanin Mama. A raina na ce da uwata na raye yau da wajenta zan yini in sha kukana ta lallashe ni sai dai ina ba ta a raye.
"Allah ya jadadda rahama a kabarin Mama da Hajiya."
Na faɗa a fili ina jin ƙwalla na taruwa a ƙwarmin idanuwana sai dai na yi ƙoƙarin maida ƙwallar da ta taho min
Ina nan zaune ƙamshin turaren Yallaɓai ya fara min maraba a ƙofifin hancina sai ga shi ya bayyana a cikin falon cikin shigar Shadda mai ruwan toka sabuwa ce sau ɗaya Yallaɓai ya taɓa sakata da wancan sallar azumin ya ɗinka ta ɗinki ba tazarce ba ne half jamba ce irin na matasan samarin zamani. A lokacin Yallaɓai masifa ya yi ta ma telan shi wai shi tazarce ya ce bai ce ya yi masa ƙaramar riga ba. Ni na yi ta tausan shi na ce ya yi haƙuri tunda an riga an ɗinka. Daƙyar ya haƙura amma bai ƙara saka kayan ba. Kuma kayan suna yi masa kyau matuƙa amma saboda ba haka ya so ɗinkin ba sai kayan su ka fita daga ranshi. Na sha ce masa ya saka kayan suna yi masa kyau sai ya ce min shi ba zai saka ba saboda ɗinkin su ɗan kama masa jiki shi dai kawai basu yi masa kyau ba. Da na gaji da yi masa magiyan ya saka nima sai na haƙura na ƙyaleshi har na manta da kayan a tunanina ma ya kyautar ne ashe suna nan sai yau ya ɗauko su ya saka saboda ya na ANGO.'
"Ango.".
Haka na maimaita a cikin raina ina jin kamar ƙirjina na ɗagowa saboda yanayin da na ke ciki.
Kallonsa na ke yi da dukkan zuciyata. Haƙika duk macen da ta samun daman auren Yallaɓai ta gama dacewa domin shi ɗin mai kyau ne kuma ɗan gayu ne ɗan ƙwalisa da ya haɗa komai na matakin rayuwa.
Ya yi min wani irin kyau a idona. Sai wata zuciyar ke faɗa min wannan adon duk ba na ki ba ne Sadiya tun yaushe kike son ya saka kayan yaƙi? Sai yau tun da zai je ya ga Gimbiya.
Tuni na ji taɓon da ke zuciyata ya taso. na ma fara ganin hazo hazo ne saboda tuƙuƙin da ke muƙurƙusan zuciyata.
Har gabana ya tako ya na wani tashin kamshi. Kafarsa na kallah sai na ga takalminsa da ya ke ji da shi a cikin jerin takalmansa ya saka sai na ɗago ina kallon hulan kansa itama mai tsadan ciki ne ya ɗauko ya saka. Lalle Yallaɓai kallonsa kawai na ke yi na ma kasa mgana ina ƙoƙarin danne abin da ke taso min daga ƙasan raina.
"Kallon fa?
Ya faɗa bayan ya ɗan buga min agogon hannun shi a saman kaina kaɗan. Sai na ƙara kallon shi a baya in Yallaɓai ya yi kwalliya ya yi kyau in zai fita har wani alfahari na ke yi amma yau kam sai na ga ina ganin duhun shi domin zuciyata na raya min ne wajen Gimbiya zai je kuma ina da tabbacin domin ita ya yi wannan gayun.
"Ko na yi miki kyau ne Madam"
Ya faÉ—a ya na mai miko min hannun shi lokaci É—aya da agogon fatan da ke hannun shi.
Na fahimci nufinshi kamar na ce ya je da shi sai Amaryansa Gimbiya ta ɗora masa sai kuma na fasa na saka hannu na karɓa ina saka masa lokaci ɗaya ina faɗin" Yau kuma kayan da ba a so ne aka saka?
Na faÉ—a bayan na gama É—aura masa agogon na mike ina ja masa kujeran zama.
"Wallahi yau kawai na gansu ƙasan kaya. Na ɗauko su ne ban ma san za su shige ni ba ina ko sakawa sai na ga sun yi min kawai sai na bar su."
Ya faÉ—a ya na mai zama a kan kujeran da na ja masa.
"Uhmm."
Na faɗa ina tura masa farantin ƙwai a gaban shi. Ruwan tea ɗin ma na zuba masa a wani Mug na tura masa gabanshi sannan na koma na zauna.
"Kin siya wankan ne?
Uhm!