← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 89

Sashe 32

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fada ta na wani mirmishi, wanda na tabbata na yake ne, to ba nasara ta ga abin da ba ta yi tsammani n gani ba. Nan ta ke Ya Aina ta ce mata in ta gama cin abinci ta na so za ta yi magana da ita sai ta ce ti, sun yi dai hira da su Ya Murja ba wanda ya nuna mata ko a fuska, ni dai sai faman bina da kallo suke yi ita da Shema'u ganin yadda na ci kunshina baƙi da ja haka ma yara su Jidda su kansu sun sha gayu, suna falon sai ga su Suwaiba da Jamila sun leƙo min biki suna shigowa suka hau faɗin" Ina Uwargida a gidan Ya Tafidan ne! Ta fito mu tantance tun da mun gama gano gayun amarya saura na uwargida."

Sai suka ci karo da ni ai sai suka ɗau shewa daman Jamila shaƙiya ce ta karshe zagaye ni ta fara yi ta na faɗin" Kai jama'a cancanɗi. Ni fa na kasa gane ki. Anty Sadiya kin gama cinye wannan gasar."
Ta faɗa ta na buga shewa ta ba ni hannu muka kashe Suwaiba kuma sai zama ta yi kan kujera ta na faɗin" Ke ce ma Amaryan Ya Sadiya to ai ko Gimbiya sai dai ta nuna miki makeup ɗin da mai kwalliya ta yi mata. Amma tabbas Uwargida ta Yallaɓai wanka ya rusuna jama'a."

Sai ta karkace hanci ta saki guɗa su Munnira na ta ya ta falon ya ɗau ihu, ina gefe ina ta dariya. Allah ya ɗauke min hamdala kawai na ke yi a cikin raina ashe da ban yi taro ba haka zan zauna baƙin ciki ya kashe ni kaɗai a gida. Suma nan suka zauna suka ci waina ana ta hira ana shewa yau dai gabaɗaya ranar ta uwargidaye ne, su Ma'u ana gefe duk an muzanta. Wannan muƙamin na manyan mata ne, sai mai nasibi ubangiji ke ba ma wannan sarautar in ji Ya Balki nan ko aka saka mata guɗa ana faɗin kwarai ma da gaske Yayarmu, ni dai ba na mgana sai dariya Suwaiba ke faɗin Yallabai na can Gwammaja ana ta hotuna ta na ma cikin faɗa ne wayata na hannun Marwa ta kawo min ta ce Yallaɓai na kira suna ko jin haka suka ɗau ihu suna faɗin.

"Yallaɓai dai bai manta da matar Yallaɓai ba duk da ya ga Amarya."

"Ita kanta Amarya in ta zo sai dai ta yi mana mubaya'a. "
In ji Munnira sai suka ƙara saka shewa suna tafawa ita da Suwaiba daman mutuniyarta ne, Jamila ta mike ta na faɗin" Wai ya ne? Gidan Uwargida ba sauti?
Ya Balki yar ta ya ɓera bari ta ce" Shi ne da ya kamata sa kar mana sauti mu yi takun uwar gida ran gida Yallaɓai ya na yi ma Sadiya rawa."
Ni kaina wannan karon na kasa rike kaina sai da na fashe da dariya a jikin Tv falon yara akwai wajen saka flash Amina na da shi aka yo dowloading É—in wakar Uwar gida suka kunna mana sauti, Suwaiba ta ce duk wacce ta san ita É—in ba Uwargida ba ce ta koma gefe wannan filin na uwargidaye ne.

Sai kawai suka miƙe suna takawa, ni dai na shige ɗakin su Jidda ina amsa wayar Yallaɓai tunda ya sake kira.

"Yallabai na"

Na faɗa har daga ƙarƙashin zuciyata kuma a cikin wayar ma har ya tona asirin halin da na ke ciki na farinciki.

"Matar Yallaɓai."

Ya faÉ—a daga can bangaren, ina jiyo hayani ya tabbata har lokacin ya na can Gwammaja É—in.

"Na'am mijin Sadiya."

Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Me kika samu ne? Na ji ki cikin farinciki ne'
Ina mirmishi na ce" Farinciki mana. Yan'uwana ke nan suna saka ni farinciki."
"Alhamdulillah na ji daÉ—in jin haka."

"Ya Hidima Yallaɓai?

A amsa min da Alhamdulillah.
"Sadiya ta yunwa na ke ji tun fitan mu fa ba mu ci wani abu ba."
Da sauri na ce" Me ya sa ba ku ta ho gida ba! Tun É—azu aka kawo waina alelen ma an gama fa."
Da sauri ya ce" To in zo za ki ba ni?
Ina dariya na ce" Ni na isa na hana Yallaɓai abinci? Sai kun taho zan shirya muku na ku in sha Allahu."

Da haka muka yi sallama, ko da na fito falo waje ya cika da shewa ga kiɗa. Har da su Ya Balki ana cikin fili ana takawa da, ban ga Ma'u da Ya Aina kenan ta ja ta gefe suna mgana. Amina na yi ma mgana abinci su Yallabai daman an cire musu, tare muka shiga kitchen ɗin ina ganin abin da ta ke haɗawan, ina cikin kitchen ɗin Munnira ta zo ta ja ni ina faɗin ta bari ina zuwa amma ba ta saurareni ba, sai tsakiyar falo ta kuma riƙe hannuna ta na rawa da ni farida ta mike ta na min liki, Shema'u na ga ta na kallona sai kawai na sakin hannun Munnira na fara takawa, suna min shewa da guɗa hana ni saƙat suka yi har su Jidda fa sun shige rawan suma sun ce ba za a bar su a baya ba.

Muna can muna bidiri ko shigowar su Yallaɓai ba mu ji ba, sai da ya leƙo da kansa ya na faɗin" Ku ce shasu kuke yi kenan"
Ai su Suwaiba suna ganin shi suka rufe shi da guɗa, ya na kare fuskarshi ya ke faɗin" Wai guɗan nan ba ta ƙarewa ne Suwaiba?

"Wanda muka yi maka a Gwammaja na Amarya ne. Wannan kuma ai sautin na uwargida ne."

Suwaiba ta faɗa ta na ƙara sakin masa guɗaa akai, ya dafe kansa ya na dariya Jamila ma ta kama Munnira na ta ya ta, Sai ga Kawu da Tariq sun shigo. Kawu shi cewa ya yi" Danƙari Tafida ka ce ga in da ake biki."
Tariq kuma ya ce" Shi fa Tafida duka amare gare shi."

Ya faɗa ya na kallona ni kunya ma na ji na sauke kaima ƙasa, Suwaiba ta fara yi ma kawu shaƙiyanci wai shima Allah ya sa baɗi uwar haka suna Rano sun je suna ya zabga mata harara kafin ya ce" Sai dai in da cikin ta zo ko?
Ni kaina sai da na yi dariya daman kawu akwai yanka mgana gaisuwa suka yi da su Ya Balki da su Inna Mariya ƙin barin shi suka yi suka ce sai an yi mana hotuna, haka nan suka tsaida mu suna ta ɗaukan mu hoto har da Tariq shima da wayarsa shi da Faridan sa, sai da na ce musu su yi haƙuri, Ango fa na jin yunwa a yi masa afuwa na bashi abinci ai sai su Suwaiba suka ƙara ɗaukan shewa suna dariya.

"Allah ya shirye ki Suwaiba."

Haka Tariq ya faɗa ya na girgiza kai. Dakyar Yallaɓai ya samu ya ƙwace suka koma falon shi sai na saka Marwa ta kai musu abincin da komai da komai a falon na Yallaɓai, bayan sun gama ci sun ƙoshi har suka bar ma gidan ban sani ba muna can ana ta hira da shewa, Ma'u dai tun da ta dawo falon ba ta ƙara dariya ba, ga ta nan dai zaune ta na bin kowa da kallo, muna nan tare da su Suwaiba har dare bayan mangariba na sauya kaya na saka material
Ya Aina da Ya Balki har da Ya Murja da Zaituna da mutanen Gandun albasa sun koma gida sai aka bar su Rahila, Ma'u ma da kawarta ba su tafi ba, da daddaren Halima ta zo ita da ƙawarta ta ce daga nan gidan Amarya za su wuce domin an tafi da ita tun mangariba ta zo min ne kawai na ce mata na gode. Haka ma Lailan Ya Auwal a lokacin ta zo ita da ƙanwarta na yi mata uziri tun da suna da hidima.

Sai wajen tara na dare gidan ya yi shuru, su Suwaiba sun koma Gwammaja su Ma'u sun tafi, Haka ma su Hauwa da Munnira daga ni sai Amina sai Rahila sai Sameena da ta yini ma kwance ba ta jin daÉ—i duk shewan da aka yi ta na É—aki, sai Saude da Marwa sai su Jidda har maman Saude da mai yi mana kitso sun zo min biki.
Su suka gyara gidan ma ya yi kintsi sai gidan ya koma ya yi shuru kamar ba shi ba ne ɗazu ya cika da hayaniyar mutane ana ta hidima sai kuma da ya yi shurun na fara jin wani iri a cikin ƙasan raina.

Ranar da na ke gudu ce yau ta zo. Ranar da Yallaɓai zai je ya kwana da wata mace ba ni ba. Tirƙashi.

*Janafty*
*TKG*

09.

*Assalamu alaikum!*
*Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.*
*Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.*
*Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*

*Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻*

For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻
7087809778
Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.

*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.*
Chapter 32 · 0% Book details