← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 89

Sashe 27

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar na yi masa sosa a in da ya ke masa ƙwaiƙayi tun da ya dafe ni sai da na gaya ma aya zaƙin ta kwanakinsa ya fanshe, sai bakwai fa muka yi wanka sannan na fita wajen yara, na sha dai sambatun Sadiyata ki yi hakuri ki yafe min wallahi ina son ki, da dai sauran su, har su Jidda suka tafi makaranta ban faɗa ma Baby zan yi tafiya ba saboda ba na son ta yi min rigima mun yi yar daɗi da Yallaɓai bayan tafiyan su Jidda ma ruwa muka koma shi dai kawai ya na faɗa min ya yi matuƙar kewata, ni kaina na yi kewarsa kuma na yi masa rawan jiki kamar yadda ya yi min.
  Shi da kanshi ya ce yara Gwammaja za su koma har na dawo saboda gobe ma Kaduna zai tafi bai san kuma lokacin da zai dawo ba shi ya sa na shirya musu kayansu a cikin ƙaramar akwatin su, ni ban nuna masa komai a fuska ba amma a raina na san Gimbiya za ta yi rawan jiki da su tun a baya ma ta yi balle yanzu mai dalili.

Ƙarfe goma muka fito daga gida na rufe gidan da key, Yallaɓai daman na da makullin shi, muna hanya zai kai ni Ɗorayi Rahila na can na jirana daga nan zai je Gwammaja ya kai kayan su Jidda daga nan na ya wuce Office, sai da muka je ƙofar gidanmu sannan ya turamin 20k na mota ya ce in na dawo za mu yi mgana. Tare muka shiga gidan dashi ya na riƙe da akwatina suka gaisa da Gwaggo da Alhajinmu.
Gwaggo dai sai ta yi masa fatan alheri. Alhajinmu kuma ya ce shi dai bai ji daɗi ba da ba a gayyace shi wajen ɗaurin auran ba duk kunya ta kama Yallaɓai ina gani duk ya kasa natsuwa. Ni ko a raina na ce Alhajinmu da kalan dangi.
Bai wani daɗe ba muka yi sallama ya wuce daman mun samu Rahila a gidan Ya Aina muke jira ta zo ta kawo mana kaya sai Ya Muntari da ya je karɓo ɗinkuna.

Mu ne ba mu tafi ba sai azahar motar mu ta tashi, ta yantumaki muka hau daga can ne in mun sauka za mu hau na Yashe, Rahila ce ke da goyo ni dai daga ni sai kayana ina zan iya, ba mu muka isa Yashe ba sai biyar na yamma ko a yan tumaki mun daɗe ba mu samu mota ba sannan wacce muka hau daga kano ta samu matsala a hanya. Ni fa sai yau na ƙara yarda da cewa tafiya yankin azaba ce mun gaji ga kishi ga yunwa, yarinyar Rahila na ta rigima na ce kya yi yarinya mu kan mu iyayenki mun jiggata.

Mun ga tarba a Yashe daman ahalin Alhajinmu Ahali ne masu karamci da son zumumci a ɗakin uwar Amarya muka sauka wato Marliya abokiyar zaman Mahaifiyarsu Muntari Jummai, gida ya sha fenti an gyara shi tsab yadda ƴan'uwa suka zagayemu ana ta hira ne ya sa na ji na manta da damuwata kamar na zo wata sabuwar duniya. Wayata na jaka sai da bayan isha'i na duba na ga Yallaɓai ya kikkirani ban gani ba sai daga baya na kira shi, ya ce min lokacin ya na Gwammaja ne zan yi mgana da Baby ta na ta rigima kuma shi yanzu ya dawo gida amma zai saka Gimbiya ta kirani sai na yi magana da ita. Kai tsaye na ce.

  "Ƙyaleta kawai za ta ba ri ne."

Domin ba na son magana da Gimbiyar ne gabaɗaya. Mun ɗan taba hira tunda daman da muka sauka na tura masa saƙo, tun da muna hanya ya na ta kirana, Yallaɓai fa ya na da kulawa matsalan kishiyan da ya yi min ne ya sa duk na daina ganin kirkin shi, a daran nan ba abin da ba'a kawo mana ba tuwo ni dai na ci miyar kuɓewa, na kuma sha fura har wajen sha ɗayan dare muna ta hira da su Baba Aminu haƙika ko ba su nuna ba sun yi farinciki da zuwan mu tun ballatana ma da muka ce musu har Gwaggo za ta taho su Alhajinmu kuma sai ranar ɗaurin aure.

"Ma sha Allah. Gidan Yaya Sule gabaɗaya za su yi mana baƙunta kenan."

In ji Baba Sani cikin murna da fara'a. Ni dai ina kwance a kan kafitar da aka sauke mu, Rahila ita na kan gado domin ta ce ba za ta kwana da ni ba kar na shure mata da Æ´a da kafafuwata.
Sai na buÉ—e baki ina kallonta ita kuma ta na dariya kai na jinjina kafin na ce" Rahila ki sani zan rama ne."
Ta na dariya ta ce sai dai na rame, na daÉ—e ban yi barci ba ina jin wani iska na shiga jikina, ina ji in da ace ban zo ba da na yi kewar wannan yanayin na farinciki da na ke cioi mu ne har wajen biyun dare muna hira da Rahila, mu na tuna baya muna ta dariya ji na ke yi kamar baya ta dawo yanzu rayuwar ta fi daÉ—i.

  Ko kafin ranar alhamis ɗin da su Ya Aina suka iso, mun riga mun zama yan gari domin mun sha yawo, mu ne gidajen yan'uwa da suke aure a kusa, sannan har gidan su Gwaggo mun je, sun zo sun iske mu mune ma ke yi musu maraba.
Ya Aina sai Ma'u da Ya Murya, sai Zaitunan Ya Abubakar Gwaggo sai jibi za ta taho tare da su Alhajinmu.

Mun sha biki sai wanda ya gani. Malunfashi a ka kai Amarya ni da Rahila da Ya Aina har da Ma'u mun je kai amarya Ya Murja ce ba ta je ba,  ranar lahadi muka dawo Yashe, litini su Ma'u suka koma kano da ya ke biki ne kuma ga jama'a har muka rabu dai ba mu raba hali ba. Ma'u dai ta je ta ga dangin babanta  kafin su koma. Baaba ba ta samu zuwa megidanta ba lafiya.
Mu kuma muka ce sai mun cike sati gobe kenan talata, na ji daɗin zuwana Yashe domin ya sa na shafe tunanin auran Yallaɓai a cikin raina muna waya da shi lokaci bayan lokaci yara ma mun yi magana da su sau biyu Baby ce ke ta karaɗin ba ni labarin Anty Gimbiya ta yi musu kaza ta yi musu ita Jidda ba ta da surutu.

Ranar litinin ɗin da yamma Munnira ta kirani a waya ta na faɗa min an kama ma Gimbiya hayan wani gida ita kaɗai a sharaɗa. Ni kuma dai Tauraini ya ce min da farƙo wataƙila wancan bai yi ba ne suka kama wani, ni kuma daman na ce ya daina zaunar da ni ya na faɗa min abin da bai shafe ni ba shi ya sa duk labarin da Munnira ke ba ni na ce mata ban san da labari ba. Ta na ga ya min anan Gwammaja za a yi taron biki, Hajiyar Tafida za ta yi nata acan Rano amma taro na gidan Nene, har da labarin Yallaɓai ya ba ma Gimbiya kuɗi masu yawa na lefe da na hidimar biki. Har Munnira na faɗin" To ke nawa ya baki? Gwara mu ji saboda mu ma mu shirya namu taron ko ya kika ce?

Ina mirmishin ya ƙe na ce" Ni ba na gari ai na zo Yashe biki ƙila sai na koma za mu yi maganar da shi." Mun rabu da ita a kan in na koma zan yi musu waya ita da Hauwa da farko na ji a raina ba zan yi wani taro ba amma ɗazu da muka yi hiran da Rahila sai ta ce na yi domin kauda idon masu mgana gazawata a ke nema abu kaɗan zai zama abin magana nima na shirya taro ni da ahalina domin a zo a ɗebemin kewa sai kuma da ta faɗa na aminta da maganarta sannan mun yi chart da Ant Zabba itama ta nuna min fa'idar haka tace har kunshi da kitso duk na yi na gyara kaina yadda duk wanda ya ganni zan yi masa kwarjini, sai na ji duka na aminta da shawarwarin sa na ɗau damaran in na koma gida za mu yi mgana da Yallabai daman taron gidana ai nawa ne, na su na can Gwammaja.

Na bari sai in na koma Kano sai na kira Inna Mariya na faɗa mata halin da a ke ciki kar su ji a wani waje, su ce ban faɗa musu ba. A daran na ga Yallaɓai ya turamin 1m miliyan ɗaya a acct ɗina, sai na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na tura masa saƙo.

"Na ga saƙo Yallaɓai na mene ne?

Da ya saƙon ne ya kirani, ni kuma na gaji na kwanta da wuri sai da safe na ga kiran shi da saƙon shi.

"Na ki ne. Yau dai za ku dawo ko? In kin dawo sai mu yi mgana."

Ko bai faɗa min ba na san na faɗan kishiya ne, tun kana ji abin daga nesa ga shi yanzu har ya zo kaina wai Yallaɓai ya turamin kuɗi amma kuɗin na faɗan kishiya ne, duk dauriyata sai da na shige makewayi na ci kuka na ƙoshi, da zamu koma gida fitan safe muka yi Baba Aminu ya ba mu wake mai yawa ni da Rahila mu ne barkoni waken suya,daddawa kuɓewa zogale bushasshiya, da sauran su duk mun yo tsaraban shi ko da la'asar ta yi muna Ɗorayi sai yamma Yallaɓai shi da yara da ya biya Gwammaja ya ɗaukosu suka zo suka ɗauke ni zuwa gida.

In ka yi tafiya duk sai ka ji gaɓɓanka sun saki, barci na yi ta yi kamar wata mattaciya kuma Alhamdulillah natsuwan da na je domin na samo kuma na samo ta, sosai na ji zuciyata ta samu sauƙi, bayan na huta da kwana biyu muka yi mgana da Yallaɓai shi ne ma ya ke faɗa min ya samu wasu kuɗi daga aikin su na Kaduna ne, na yi haƙuri da kuɗin hannuna na siya abin buƙata na kaya da sauran su , na yi ƙokarin nuna masa bakomai cikin raankwafa na yi masa godiya.

"Na gode Yallaɓai. Allah ya ƙara buɗi"
Chapter 27 · 0% Book details