← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 89

Sashe 80

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ya na neman raina min wayau ya sa na gyara tsayuwa ina faɗin" Duk ranar da za ka dawo gidana sai ka kwasomin matarka ta zo ta raba min dare a gida ina so na sake da mijina ta bi ta kankame ta hanani sakewa.  Sannan bayan duk haka bai ishe ta ba sai ta ƙara jan ka ka je mai da ta gida nan ma ka ƙara ɓata lokaci kafim ka dawo! Shin wai me hakan ke nufi ne? Ko wani tsari ne ka fito da shi ni ban sani ba? Tsabar ma shiga haƙki ko ƴaƴana ka ga ina tura mata ranar da kake gidanta ne? Ballanta ni na riƙa shiryawa ina bin ka? Na yi muku kara da kawaici masu yawa amma na ga daga kai har ita ba ku san zuru ba shi ya sa na ce bari in yi magana in ka manta in ƙara tunatar da kai wannan dai shiga haƙƙi ne."

Na faÉ—a ina yarfa hannu da ya ke san ya san bai da gaskiya bai yi faÉ—a ba
Sai kawai ya ce" To ki yi haƙuri ba za a ƙara ba. Ban ɗauka hakan zai ɓata miki rai ba ne"
Tsabar takaici na kasa mgana sai kallon shi kawai na ke yi.
"Ita ce ba ta son zaman ita kaÉ—ai shi ya sa na ke É—aukota mu zo nan ko za ta samu sakewa."

"Ba ta son zama ita kaÉ—ai ko kai ne ba ta son kana yi mata nisa?

"To in ma haka ne laifi ne?

Ya faɗa ya na sosa ƙeya har ya na min ƴar dariya.

"Ba shakka. To ƙarshen soyayya dai ai mun ga Laila da Majnun"

Kawai sai ya riƙo ni ya na faɗin" To ni ai ke ce Lailata ni kuma Majnun ɗin ki"
Ture shi na yi ina hararanshi wai ni Yallaɓai zai yi ma wayau.

"Oh ni dai na faÉ—a maka ba na so."

"To ya kike son a yi yanzu?

"Ka daina kwaso min ita ba na so. Ta tsaya iya matsayinta ban hana ta zuwa gaishe mu ba amma kar kuma a mai da zuwan ya zama na ibada mana."

"To shike nan ba za a ƙara ba. Shi ke nan ko?

Sai na gyaÉ—a masa kai saboda ya ga na É—an zafafa sai ya rumgumeni ya na faÉ—in" Kai My Sady rigima."
Tureshi na yi ina faÉ—in" ba rigima ba ce gaskiya ne."
Ni ban san yadda suka ƙare ba fita ya yi ya bar ni a cikin ɗaki ban kuma san me ya faɗa mata ba amma tun daga ranar ta daina biyo min miji tana zuwa falona ta na min karairaya ba, shima ɗin ya daina kwaso min ita hakan ya fi kowa ya zauna in da Allah ya ajiye shi wannan dai da gida ɗaya muke da ta kashe ni da bariki ba ma gida ɗaya ba amma ba ta barni na huta ba

Ni da Ya Aina ta tare da Ya Balki muka kafsa kayan saka Rana. Biyu muka raba. Kashi daya namu kashi ɗaya na dangin Babansu Marwa. Namu Gwammaja muka je dashi muka raba har da Ya Murja. An cire ma mutanen Yashe na su sai kuma can ƴan gandun albasa. Sannam mu ma muka cire namu. Na Amina lokacin Datti na gida shi aka ba ma da zai koma makaranta ya tafin mata dashi. Na Ya Auwal da Ya Hamza kuma an faɗa musu suka ce kawai a rabar ba sai an ijiye musu ba, shi Gwaggo ta ce za ta aika dashi maƙota ita kuma Ya Aina daman tun a can mun ɗibar mata na ta, ita da Marwa da maƙota tare da mutanenta. Kowa ya na ta fatan alheri ni na kira Marwa da kaina ta na makaranta muka yi magana ta ce min ya ce a Rano za ta zauna na ce daman ya faɗa ba shi da in da ya fi Rano gida shi a wajen shi, kuma can ne ya gina ƙaton gida da daɗewa. Ta dai ce suna waya lafiya lau ana ta shan soyayya na ce to ta dake ta kama shi gam a hannu ta shiga zuciyarsa sosai kafin ta ayi aurin wanda in aka yin auren kuma shi kenan.

Yallaɓai na ji na ina wayar sai da na gama ya ce min wai ni uwar banza ce, na ce na ji bakomai ƙaramar uwa abokiyar wasa.
"Kin kusa ijiye na ki surukin fa Sadiya"
Ya faÉ—a ya na dariya nima ina taya shi na kuma ce masa ko Jidda ce haka zan zaunar da ita ina karanta mata.
"Ba shakka uwar zamani."
"Na gode Uban zamani."
Yallaɓai ya yi fafur ya ce shi kam Dattijon zamani ne ba da shi da zama uban zamani ba.
Bayan fitan shi na zauna ina tunani Jidda na cikin shekaru na sha biyar amma ba ta fara al'ada ba, sai dai ta fara ƙirgan dangi na gansu sun tsiro a ƙirjinta ban damu ba ƙila yanayin jikinta ne amma tabbas ta na gabda farawa  nan ba daɗewa ba, girma fa ya kama ni wasa wasa Jidda ta kusa kaiwa munzali. Ni kaɗai a ƙasan raina na ke musu add'an Allah ya tsare min su da dukkan tsarewansa wataƙila su kaɗai ne yayana anan gidan duniya.

****
Friday.

Munnira ce ta samu ɓari ni ban ma sani ba sai da Hauwa ta yi min waya ta na faɗa min tun da gaskiya mun kwana biyu ba mu haɗu da juna ba. Na dai san ta na da cikin tun da mun yi zencen da Hauwa kwanaki da ta zo gidana.
Kuma kamar haɗin bakin itama Hauwan ta samu ciki ɗan wata ɗaya ta yi ɓarin shi amma da ta je ganin gida ne a Rano ta ce ma ba ta san dashi ba. To itama Munnira ta samu ɓari ta zame a banɗaki ta faɗi gefen cikin shikenan sai jini kwananta ɗaya a asibiti aka sallamota ta dawo gida. Ni da Hauwa mun je asibitin shi ne bayan ta koma gida muka tsara za mu je mu yini ranar jumma'a. Na kuma faɗa ma Yallaɓai ya ce sai mun dawo.

Su Jidda a gida na ce zan bar su tare da Saude tun da na yi mata waya na ce in sun taso daga makaranta ta zo gida ina jiranta. Tun safe na gama ayyukana har da faten wake mai hanta na yi ma Munnira domin ta ce na taho mata da abin daɗi. Hauwa na zauna zaman jira tun da ita ce za ta biyo min, kawai ina zaune ina zaman jiranta sai ga wayar Yallaɓai bayan mun gaisa da ya ke yau ya bar gidana da yamma zai koma gidan Gimbiya.

"Kun tafi ne?

"A'a me ya faru?

Na tambaya saboda na ji mamakin tambayarsa.

"Daman zan ce ne ku jira Daugther ta taho yanzu da mota sai ta É—auke ku, ku tafi tare gabaÉ—aya."

Tuni na ji raina ya ɓaci Yallabai akwai sanabe da tsegemu. Yanzu haka ta ce za ta je ne zai ce ai mu ma za mu je ta biyo mu tafi tare.

"Na faÉ—a mata ta biyo ta gida ku wuce."

Har ya gama mganarsa ma, na so na danne ma zuciyata na amsa masa sai kuma na ga in na yi shuru ba amfani.

"Yallaɓai yaushe muka fara fita anguwa da matarka?

Sai ya yi shuru.

"Ka bar mu tafi kawai. Ba ta san gidan ba ne? mu haÉ—u a can"

"To ni na ce ta biyo ta nan ta É—aukeku ku wuce ko ban isa ba ne?

"Ka isa."

"To tun da na isa a yi yadda na ce."

Ya na gama faɗin haka ya katse kiran ya bar ni da ƙunƙuni. Da Hauwa ta zo na faɗa mata itama sai da ta ce topha sanabe daman kun saba fita tare ne?
"Ina fa? Sanabe ne da gulma irin ta É—a namiji ta na da mota mu kuma ba mu da ita ta zo ta yi mana lift mana."
Hauwa na dariya ta ce ba shakka masu mota.

Matar nan haka taɓata mana lokaci mu da muka ce yini za mu je mu yi sai 2 da wani abu na  rana sai ga ta zo. Har mamakin yadda ta ke cin kwalliya na ke yi in za ta fita. Allah ya sa nima da gayu na ta zo ta ganni ballantana ta ce ganin idone. Ita ta ɗauke mu a motar ta kamfanin toyota ce. Accord ina gidan gaba Hauwa na gidan baya har gidan Munnira itama da ta ganmu tare sai da ta yi min mgana.

"Ke kuma wani ci baya ne ya same ki yawo da kishiya."

Ina dariya na ce" Yallaɓai ne ya siyo min wannan wulaƙancin"

Nan ba ta labarin yadda muka yi dashi Munnira ta buga shewa kafin ta ce" Ki yi zuciya ki yi mota Hajiya. Amma tabbas an nuna miki kafacinty mota yau É—in nan"
Ni kaina sai da na yi dariya na ce to ai ina sana'ata domin na kama sana'ar Hijabai hannu biyu kuma ina samu sosai yanzu har kaduna na ke aika ma Amina.

"In sana'ata in da rai da rabo.."

"Jariri za ya zamo ango."

Hauwa ta karishe min muka tafa. Can falo muka bar Gimbiya a falo muna ciki muna hira muna shewa.
Ba mu bar gidan ba sai shidda har gida muka kai Hauwa nima ta kawo ni gida nan ta yi sallar mangariba da ya ke ta san miji na ta ne sai ba ta tsaya ba ta tuka kanta zuwa gida ciki dai gashi nan ya bayyana daga gani ta na da girman ciki sosai.
Chapter 80 · 0% Book details